ALAMOMIN CIKAWA DA IMANI GUDA 21(Malam Aminu Ibrahim Daurawa)


ALAMOMIN CIKAWA DA IMANI GUDA 21(Malam Aminu Ibrahim Daurawa) Wannan duniyar cike take da rikici, da musifu, da bala’o’i, da tashin hankali da jarrabawa, da matsaloli, babbar nasara shine, cikawa da imani, Malamai sunyi bayanai gamai da wasu alamomi, idan mutum ya cika da su, ana yi masa fata na gari Sune 1- cikawa da kalmar shahada 2- mutuwa da gumin goshi 3- mutuwa a daren Juma’a ko ranar Juma’a 4- Shahada a filin yakin daukaka Addinin Allah 5- Mutuwa a tafarkin Allah 6- mutuwa da Annoba 7- mutuwa da sababin ciwon ciki 8- mutuwa da dalilin nutsewa a ruwa 9- mutuwa karkashin gini 10- mutuwa da kunar wuta 11- mutuwa da ciwon kaluluwa 12- mace ta mutu a wajen haihuwa 13- wanda aka kashe shi, wajen tsare dukiyar sa 14- wanda aka kashe shi wajen tsare iyalan sa 15-wanda aka kashe shi, saboda addinin sa 16- wanda ak kashe shi wajen kare kansa 17- wanda ya mutu da ciwon tarin fuka 18- wanda aka kashe shi, akan hakkin sa 19- wanda ya mutu wajen gadin addini da dukkiyar Al’umma 20- wanda ya mutu yana cikin aikin alkhairi, kamar sallah dawafi, azumi sujjada, da makamantansu, 21- wanda ya mutu mutane suna ta yi masa sheda ta gari, Dalilan wadannan bayanai, daga littafin Allah da sunnar Annabi saw, suna cikin littafin Ahkamul Janaiz na Shaik Albaniy da salatul Mumina na Dr Saeed alqahdaniy Allah yasa mu cika da imani Amin

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s