SANIN MUHIMMANCIN ILIMI – DR MANSOOR SOTOKO


SANIN MUHIMMANCIN LOKACI
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Ba wani mutum a duniya da ya kamata ya
san muhimmancin lokaci kamar musulmi.
Idan musulmi ya wayi gari abu na farko da
zai yi shi ne sallar asuba, can bayan rana ta
gota ya yi azahar.. haka har wuninsa ya kare
yana bibiyar lokuta don ya gana da
ubangijinsa. A sati kuma akwai sallar
jumu’ah.. a shekara akwai watan azumi,
akwai idi, akwai layya, akwai aikin hajji. Idan
musulmi yana da jari kuma akwai fitar da
zakkah duk shekara. Allah ya rantse mana da
lokaci don mu san muhimmancinsa. Lokaci
ga dan adam shi ne jarinsa, kai ma dai shi
ne rayuwarsa. A cikinsa ne kake murna ko
ka samu damuwa. A cikinsa ne kake ciwo ko
ka samu lafiya. A cikinsa ne kake talauci ko
ka samu arzikin duniya. A cikinsa ne kake
shuka alheri ka girbe shi lahira ko ka shuka
sharri ka same shi can yana jiran ka gome
alkiyama. Don haka a cikin lokacin duniya ne
ake samun aljanna ko a fada cikin
jahannama. Allah ya kiyaye mu. Lokaci ya fi
komi saurin wucewa. Ba ya jira, kuma in ya
tafi ba ya dawowa. Sannan kuma Allah bai
sanar da kowa lokacin da ya diba ma sa ba.
Lokacin da Allah ya ba ka shine tsawon
shekarun rayuwarka. Idan ka kwantar da
hankalinka sai ka ga dan lokaci ne da ba ya
da yawa. Wanda aka ba shi shekaru sittin
misali nawa ne za a cire daga ciki na
kuruciyarsa? Nawa ne yake kararwa a barci?
Nawa ne adadin kwanuka marasa amfani a
cikin su? Dan Adam ya kan yi nadama a kan
lokacinsa da ya wuce a wurare muhimmai
guda biyu: Na farko: Idan mala’ikan mutuwa
ya damke shi, ya hakikance cewa tilas zai
bar duniya a nan ne yake cewa: Ya ubangiji
ku dawo da ni. Domin kila in yi aikin kwarai
a cikin abinda na bari. Ina! Wata magana dai
ce da shi yake fadar ta, kuma a bayan su
akwai rayuwar barzahu da zasu yi har zuwa
ranar da za a tashe su. Suratul Muminun:
99-100 Wuri na biyu: Shi ne idan aka yi
tashin alkiyama, kowa ya ga sakamakonsa,
aka yanke ma kowa hukuncin in da zai
zauna. A nan ne dan adam ke cewa: Kuma
da zaka ga kangararru sun sunkuyar da
kawunansu a wurin ubangijinsu, (suna
cewa): “Ya ubangijinmu! Mun fa gani kuma
mun jiya, to, ka mayar da mu mu yi aikin
kwarai, mu fa tabbas mun gano gaskiya”.
Kuma da mun so da mun bai wa kowane
mai rai ikon shiriya, amma maganarmu ta
riga ta tabbata cewa, lalle sai mun cika
wutar jahannama da aljanu da mutane baki
daya. To, ku dandani azaba don mantawar
da kuka yi da haduwarku ta wannan rana,
mu ma mun manta da ku, kuma ku dandani
azaba ta din-din-din saboda abinda kuka
kasance kuna aikatawa. Suratus Sajdah:
12-14 Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallama ya fada mana cewa, akwai
ni’imomi guda biyu da ake kwaruwar dan
adam a kan su; lafiya da kuma lokaci. Dalilai
uku ne ke sa a kwari mutum game da
sha’anin lokaci. Ko dai ya kasance bai yi
cikakken amfani da lokacin ba ta hanyar yin
abinda ya kamata wanda zai samu babbar
lada, ko kuma ya kasa yin aikin lada sam
sam, ko kuma a cikin lokacin ya yi aikin
zunubi. Mutane sun kasu kashi kashi
dangane da lokaci. Wani za ka ga mafi
yawan lokacinsa yana cike da abubuwa ne
masu amfani, wani kuma duk lokacinsa na
sharholiya ne, wani shi kuma bai ma san ya
zai yi da lokaci ba! Matsalar wani ita ce bai
tsara ma rayuwarsa kome ba, wani kuma
bai san muhimmancin lokacin ba. Wani ya
sani amma bai da karfin zuciya da kwarin
guiwa na maida hankali ga abinda ke
amfaninsa. Yana da kyau mu duba rayuwar
magabata mu ga yadda suke cin moriyarsa.
Abdurrahman bin Mahdi ya bada labarin
malaminsa Hammad bin Salamah ya ce, da
an ce ma Hammad ga alkiyama nan za ta
tsayu bai da yadda zai kara bisa ga aikin da
ya ke yi. Ba zamu yi mamakin wannan
maganar ba in muka san cewa malam
Hammad ya rasu yana cikin sallah. Saurari
wani dalibin ilimi abinda Abu Hatim Ar-Razi
Rahimahullah abinda yake cewa: “Mun nemi
malam Ka’anabi ya karantar da mu
Muwadda sai ya ce to ku zo da safe. Sai
muka ce masa da mun yi asuba wurin
malam Hajjaj muke zuwa. Ya ce, to ku zo in
kun kare. Muka ce sannan muke zuwa wurin
malam Muslim bin Ibrahim. Ya ce to ku zo in
kun gama. Muka ce ko da muke gamawa
azahar ta yi, sannan muke karatu ga Abu
Huzaifa. Ya ce, to, ku zo bayan la’asar. Muka
ce, makarantar Arim. Ya ce to ku zo bayan
magariba. To, daga nan muka rinka zuwa
wurin sa idan an yi magariba sai ya fito ana
sanyi ya nadiye kansa ya yi ta karantar da
mu har illa mashaAllahu”. Ta hanyar amfani
da lokaci ne kawai ake iya fito da baiwa iri
iri da Allah ya yi wa dan adam. Bincike ya
nuna cewa akasarin mutane ba su amfani
da kashi 25 cikin 100 na baiwar da Allah ya
ba su. Yaron da ya fadi jarabawa kuma ya
rufe aji yana iya zama na daya ba a
makarantarsu kawai ba a fadin jiha gaba
daya inda an yi kokarin fitowa da baiwar da
Allah ya ba shi. Shiriritaccen da zaka gan shi
yana kashe wando a bakin titi yana iya zama
babban malami ko babban mawallafi ko
kwararren likita ko gogaggen dan siyasa ko
fitaccen dan kasuwa. Amma an watsar da
baiwar da Allah ya ba shi, shi ya sa ya lalace.
Wanda ya zo na baya a wajen tsera ko gasar
karatun alkur’ani yana iya zarce kowa in da
an tona baiwar Allah da ke tattare a cikin sa.
Kana iya gwada wannan ga dan takara a
wajen tserar gudu idan ya kasa, ya koma
baya har ya kai ga faduwa saboda gajiya.
Idan likitoci suka auna shi a lokacin zasu ce
mana akwai sauran karfi da kuzari mai
yawa a jikinsa amma yana bukatar abinda
zai zakulo wannan karfin. Ya zamu gane
wannan? Mu sakar masa zaki ko maciji
misali. A nan ne zaka sha mamaki. Suna yin
arba da zaki zaka ga ya tashi ya ruga da
gudu, irin gudun da can da farko ma bai yi
shi ba. Me ya tono wannan kuzari na gudu
daga jikinsa? Daga sama aka sauko masa da
shi? A’a. Daman yana nan cikin jikinsa amma
yana neman abinda zai motsa shi! Wannan
shi zai fassara maka irin albarkar rayuwar
magabata wajen jihadi da karantarwa da
rubuce rubuce da makamantansu. Sun
sanya wata manufa a gaban su ita ce neman
yardar Allah. Wannan manufa sai take fitar
da iyakar abinda yake yiwuwa na baiwar
Allah da ke cikin su. In ba don Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ba da su
sayyidina Umar da Ibnu Mas’ud da Khalid bin
Walid da sauransu duk iyakar su su zamo
makiyaya ko ‘yan kasuwa ko ‘yan tauri ko
wani abu mai kama da wannan. Amma da
aka samu jagora cikakke mai manufa sai ya
fito da ikon Allah a cikin su. Nan take
kowanensu ya taka rawa mai muhimmanci
a tarihin duniya. Wani daga cikin magabata
ke cewa, wani lokaci sai bacci ya fara dauka
ta, ina cikin jin dadinsa sai in tuna da wuta
da aljanna. Idan na tuna haka sai in ga na
zabura kamar zaki na tafi zuwa kiyamullaili.
Ko kun ga yadda tsayayyar manufa take sa a
kula da muhimmancin lokaci? Fetur idan aka
zubar da shi ga kasa sai kasa ta shanye shi
bai amfani kowa ba. Amma in da an zuba
shi a mota fa? Wannan shi ne misalin
hikimomin Allah da bamu yi amfani da lokaci
muka ci moriyar su ba. Wannan kuma shi ne
sirrin da ya sa idan an yi yaki musulmi ke
galaba a kan kafirai. Allah Ta’ala ya ce: Kuma
kada ku yi rauni wajen yakar mutanen, in
har kuna jin radadi, to hakika su ma suna jin
radadi kamar yadda kuke ji, kuma kuna fatar
samun abinda ba su fatar samun sa daga
wurin Allah. Kuma Allah ya kasance mai
cikakken sani, mai cikakkiyar hikima.
Suratun Nisa’i: 104 A wata ayar kuma Allah
ya ce: Kuma kada ku yi rauni, kada ku yi
bakin ciki, domin ku ne madaukaka in har
kun kasance muminai. Suratu Ali Imran: 139
Wani malami ya tsaya a gaban ‘yan wasa
suna ta sharholiyarsu. Sai aka gan shi yana
jin haushi yana ciza yatsa. Don me? Ya ce,
wallahi na so a ce lokaci kaya ne, sai in sayi
na wadannan don ba ya da amfani gare su.
Ya ku bayin Allah! Ga wasu muhimman
shawarwari da zasu taimaka mana wajen
kula da lokaci: 1. Kada ka yarda ka bar wani
lokaci ‘yamti, domin wannan ba dabi’ar
mumini ba ce. Allah Ta’ala ya ce: “Idan ka
gama al’amurran duniya, to ka kafu wajen
ibada. Kuma ka yi kwadayi zuwa ga
ubangijinka” Suratus Sharh: 7 -8 Da zaran ka
samu lokacin da ba komai da zaka yi, samar
masa wani abinda zai amfane ka. Misali
lokacin jiran wani, kamar jiran likita a asibiti,
ko layin shiga mota, ko kuma kan hanya
daga wani gari zuwa wani gari ko wata
unguwa zuwa wata unguwa. A lokacin da
kake tuka babur ko aka dauka a kansa zuwa
kasuwa. A lokacin da kake shago amma ba
wani abokin ciniki tare da kai. A duk irin
wadannan lokuta kana iya kago wani abu
da zai amfane ka kamar yin zikiri ko karanta
wani littafi ko kuma wata tattaunawa mai
muhimmanci da wani wanda kake tare da
shi. Da wannan ma’aikaci na iya cin moriyar
abinda ya yi rara na lokacinsa. Dan kasuwa
ma haka. Mai achaba da mai lodi da kafinta
da mai kasa kaya a titi duk suna iya amfani
da lokutan rara a wajen ambaton Allah da
makamantansa. Ibnu Taimiyyah Abdussalam
yakan ce ma dansa Ibnu Taimiyyah Ahmad:
“Zo ka yi karatu kusan da ban-daki kafin na
fito” don ya saurari karatu a yayin da yake
biyan bukata, gudun kada lokacinsa ya tafi a
banza a daidai wannan lokaci. 2. Yi kokari a
kullum ka gabatar da abinda ya fi
muhimmanci. Idan ayyuka biyu suka hadu
babba da karami ka fara gabatar da babba.
Idan kuma dayansu yana amfaninka ne kai
kadai dayan kuma yana amfanin jama’a, fara
yin mai amfanin jama’a tukuna. Kamar sallar
nafila da karantar da mutane. Idan kuma
aiki daya yana da lokaci mai wucewa dayan
kuma ana iya yin sa a koyaushe to, fara
gabatar da wanda lokacinsa ke wucewa.
Kamar addua a lokacin ijaba. 3. Ka auna duk
maganar da zaka yi don ka tantance
amfaninta ko cutarwarta. Idan ka yarda ba
ta da amfani sai ka bar ta ka yi wata ko kayi
shiru don ka tsira da lokacinka. 4. Yi kokari
ka gano lokutan da kake tozartawa a wuni.
Misali, daga sallar asuba zuwa karfe goma,
awa ne? Wane amfani suke maka? Kar ka
manta cewa, kafin wannan lokaci ka share
dare watakila kana barci. Tsakanin magariba
da isha’i me kake yi? Daga isha’i zuwa shiga
bacci fa? Idan ka gano wadannan lokutan
sai ka tsara yadda za ka rage tozarta su. 5.
kada ka bari mutane su rika sitarin
lokacinka. Duba misali yadda Imamul
Bukhari yake yi idan ya yi bako mai nauyi.
Abinda yake yi shi ne sai ya dauko littafinsa
ya ce ma bakon yana da kyau mu karanta
wannan domin mu amfana. Shi kuma Ibnu
Akil Al-Hambali idan ya yi irin wadannan baki
sai ya dauko alkalumansa na rubutu ya ce su
taya shi fekewa. 6. Tuna mutuwa na taimaka
maka ainun wajen kula da lokacinka. Duk
matafiyi idan ya ci rabin hanya zai ji cewa ya
kusa kai. Amma a mas’alar rayuwa da
mutuwa ba mu tuna haka. Sai ka ga mutum
in ya yi shekaru talatin yana ganin tukuna
bai yi kome ba. Shi ya sa ake cewa mafi
yawan mutane suna mutuwa ne a cikin
kuruciya, don ba a dauka sun kai lokacin
mutuwa ba. Rayuwar dan adam ba ta da
tsawo. Akwai halittu na daji da ke kai
shekaru 200 zuwa 300 ko abinda ya fi haka.
A bishiyoyi ma akwai wadanda su ke kunne
ya girmi kaka. Su duwatsu ba a ma maganar
su. Don haka babu mamaki ka ga
shekarunka sun kare nan take. Samu wata
rana ko da a cikin wata ne ka je ziyara
makabarta kai kadai ka tsaya ka kalli
wadanda ke kwance. Ka tambaye su, mene
ne gurinku? Me kuke fata a yau? Ba zasu ba
ka amsa ba. Amma ka sani da zasu buda
baki da zasu ce, muna son mu dawo duniya
mu ci ribar lokaci. 7. Sanin cewa bayan
mutuwa akwai tambaya. Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce:
“Ba wanda zai daga kafarsa a ranar
alkiyama har sai ya amsa tambayoyi guda
hudu: Ta farko: Rayuwarsa a ina ya karar da
ita? Ta biyu: Kuruciyarsa a kan me ya tafi da
ita? Ta uku: Abinda ya sani ko ya yi aiki da
shi? Ta hudu: Dukiyar da ya samu a duniya,
ta ina ya same ta kuma ta yaya ya kashe ta?
Ya ku ‘yan uwa musulmi! Muna gaf da shiga
wani wata mai albarka wanda masu dabara
suke cin kasuwar lahira a cikinsa. Watan
Ramadhan wanda ayyukan lada suka fi komi
kadari a cikinsa. Watan da ke da Lailatul
kadari a cikinsa. Wane irin shiri muka yi
domin tarbonsa? Wace ajenda muka sanya
ma kanmu don ganin mun amfana da shi
watakila shi ne na karshen da wasunmu
zasu gani? Wasu an yi na bara da su amma
ba za ayi na bana da su ba. Wasu ma daga
cikinsu yanzu an rabe dukiyoyinsu, an aure
matayensu, an rufe shafin tuna su. Suna can
a tsakanin ayyukansu da suka shuka a nan
duniya. Mu ja damara ya ku ‘yan uwa, mu sa
himma, mu shirya ma wannan wata duk
abinda muke iyawa. Mu yi tattali na yin
azumi da tarawihi da halartar tafsiri da yin
sadaka da sada zumunta da yin umra ga
masu hali da I’itikafi da duk abinda muke
fatar ya sada mu da Allah. Ya Allah ka yi
muna dace, ka sa mu cikin bayinka salihai,
ka isar da mu wannan wata, ka sa ya zama
watan diyautawa da gafara a gare mu.
DAGA MASALLACIN SAYYIDINA ABU HURAIRA
( RA), SOKOTO Yan uwa da muke tare a
wannan dandali yau ma ba ni a garin
Sokoto, kuma Na’ibi na daya Sheikh
Muhammad Sani Abdullahi zai jagoranci
sallar jumu’ah. Na debo maku daga cikin
taskar hudubobin da suka gabata wacce
aka gabatar a ranar 21 ga Sha’aban 1432H
(22/7/2011) mai taken:

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s