ARBA’UNA HADITH (4) HADISI NA HUDU


ARBA'UNA HADITH (4) HADISI NA HUDU
An karbo daga abu Abdurrahaman
Abdullahi dan Mas’ud (R.A) yace manzon
Allah (S.A.W) ya bamu labari shi ne mai
gaskiya cikin dukkan al’amuran da yake
kuma abin gasgatawa yace lallai kowanne
dayanku ana tara halittarsaa cikin
mahaifiyarsa, tsawon kwana arba’in yana
maniyyi sannan , ya canja ya zama gudan
jinni kwatankwacin wannan sannan ya juya
ya zama tsoka kwatankwacin wannan
sannan, ya juya ya zama tsoka
kwatankwain haka, sai a aiko mala’ika ya
busa masa rai a umarce shi da rubuta
kalmomi guda hudu: A rubuta arzikinsa da
ajalinsa dad a ayyukansa da kuma dan wuta
ne ko aljanna na rantse da wanda babu
wani abin bautawa da gaskiya lallai
dayanku zai yi aiki irin na ‘yan Aljanna har
ya zamanto baa bin da ke tsakaninsa da
Aljanna sai zira’I daya sai rubutun can ya
rigaya shi yayi aiki irin na ‘yan wuta, sai ya
shige ta lallai dayannku zai yi aiki irin na
‘yan wuta har abin da ke tsakaninsa da ita
bai zira’I daya ba sai littafi ya rigaye shi si
yayi aiki irin aikin yan aljanna sai ya shige ta
Bukhari ( 3208) Muslim (2643).
SHARHI
Abdullahi bin mas’ud (R.T.A) yana cikin
sahabban farko da suka musulunta kuma
suka yi hijira shi mutum ne wanda yake mai
karamar halitta har wata rana yah au kan
wata itaciya sai sahabbai suke dariya
saboda gashi gajere ga kuma kwaurin
Abdullahi dan Mas’’ud keke yi dariya, na
rantse da wanda ran Annabi Muhammadu
(S.A.W) hannunsa kwaurin nasa guda biyu
in an dora akan mizani sun karfin dutsen
uhudu “ (Iman Ahmad ne rawaito shi ) shi
mutum da Annabi (S.A.W) yace “Karanta min
Alqur’ani sai Abdullahi dan Mas’ud yace, “Ai
kai aka saukarwa “ sai yace, ni aka
saukarwa amma ina so in ji daga bakin
wanina karanta min in ji sai ya karanta
masa suratun Nisa’I zuwa wajen fadin Allah
s
ﻓﻜﻴﻒ ﺍﺫ ﺟﻌﻨﺎ ﻣﻦ ﻛﻞ ﺃﻣﺔ ﺑﺸﻬﻴﺪ ﻭ ﺟﻌﻨﺎ ﺑﻚ ﻋﻠﻰ
ﻫﺆ ﻻ ﺀ ﺷﻬﻴﺪﺍ )41 ). (yaya matsayin mutane zai
zama idan muka zo da kowacce al’umma
tare da mai mata shaida kai kuma zo da kai
kana mai yin shaida kan wannan al’ummar
Abin da ake nufi da cewa sai littafinsa ya yi
rinjaye shi ne sai rubutun can da ka yi tun
yana ciki sai ya rinjaye shi sai yazo yayi aikin
da shi aka rubuta sai ya shi ga ciki masu iri
wannan aikin abin wannan hadisin ke
nunawa idan ka ganka a ayyukan da’a kana
aiki na da’a ka roki allah dorewa har zuwa
mutuwa akan wannan aikin don ba ka san
karshen wannan ya sa Annabi (S.A.W) yake
cewa “Ya Allah mai jujjuya zukata! tabbatar
da zuciyata akan addinnka (Tirmizi ya
rawaito shi (2140) da Imam Ahmad, saboda
haka kullum ka ganka ka a cikin alheri sai
ka rinka yi wa kanka addu’a a cikin dare
sannna kuma idan mutum ya yi aiki barna
kar ya debe tsammani yace, to ai yanzu ni
da nayi aikin barna iri kaza, watakila ko na
tuba ba za’a karba ba Allah yace,
ﻗﻞ ﻳﻌﺒﺎﺩﻯ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﺳﺮ ﻓﻮ ﻋﻠﻰ ﺍﻧﻔﺴﻬﻢ ﻻ ﺗﻘﻨﻄﻮ ﻣﻦ
ﺭﺟﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬ ﻧﻮ ﺏ ﺟﻤﻴﻊ ﺍﻧﻪ ﻫﻮ
ﺍﻟﻐﻔﻮﺭ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ )53 ( ﺍﻟﺰ ﻣﺮ :
Kace ‘ya ku bayina wadanda suka yi wa
kansu barna! Kada ku yanke kauna daga
rahamar Allah hakika Allah yana gafarta
zunubai gaba daya hakika shi (Allah) mai
yawan gafara ne mai jin kai (Azzumar 53)
Don haka ba a so ka debe tsammani duk
yawan zunubanka in ka tuba Allah zai
gafarta maka zunubi na karshe shi ne
shirka, amma idan mutum ya tuba Allah zia
canza munanan ayyukanasa, su zamamto
kyawawa wannan hadisin abin da yake
nunawa kenan.
Wadansu kuma suka zo wajen Annabi
(S.A.W) suka ce dashi in dai ya zamanto an
rubuta komai tun mutum na ciki to me ya
sa za a samu muyui aiki ? a kyale mu tsaya a
kan rubutun da aka yi tun muna ciki mana!
Sai Annabi (S.A.W) yace “ Ku yi aiki kowanne
da sannu za a karkatar da shi izuwa ga abin
da aka rubuta shi akai”
{Duba Bukhari (6217) Muslim (2647)
saboda haka za ka kafa hujja ne da abin da
Allah yace, ba abinda Allah ya rubuta ba,
don abin day a rubuta ya Riga ya rubuta
amma bai fada maka a inda ya rubuta ka
ba? Amma a Alkur’ani mai girma yace, kayi
sallah kayi zakka kayi imani ka kyautata w
iyaye to sai kabi wannan umarnin na
Alkur’an ma girma yace “kayi sallah kayi
zakka kayi imani ka kyautata wa iyaye to si
ka bi wannan umarnin ka Al’kur’ani don shi
ne tabbas don waccan rubutun ba ka san
inda aka rubuta ba.
Haka nan wannan hadisi yana nuna
matakan halittar dan Adan: matakin farko
digon maniyyi, mataki na biyu ya zama dan
Adam sai ya kai wata hudu sannna yake
zama dan adam amma a wancan lokacin
duk wadansu zango ne na daya da na biyu
da na uku wanda ba a riga an busa rai ba
shi yasa sa malaman fikihu suke bayani
dangane da wanda yayi yunkurin da mace
cikinta ko ya doke ta har cikinsa ya zube
akwai wata hudu saboda in ba a kai wata
hudu ba, bai riga ya zama rai ba in an kai
wata hudu sya riga ya zama rai. Sai dai
akwai hadisi a cikin sahihu Muslim (2645)
wanda yake nuna a cikin halittar dan Adam
to yaya umartar mala’ikan ya sawwara
halittar dan Adam. To yaya za ayi a hada su?
sai wadansu suke ce ai can taswira akace,
babu busa rai taswira daban, busa rai
daban
A wadansu ayoyin sai aka nuna matakai
guda bakwai ake bi wasu kuma suna nuna
guda biya r a karshe zaka ga sun kai guda
bakwai Allahi yace,
ﻭ ﻟﻘﺪ ﺧﻠﻘﻨﺎ ﺍﻻ ﻧﺴﻦ ﻣﻦ ﺳﻠﻠﺔ ﻣﻦ ﻃﻴﻦ )12 ( ﺛﻢ
ﺟﻌﻠﻦ ﻧﻄﻔﺔ ﻓﻰ ﻗﺮﺍﺭ ﻣﻜﻴﻦ )13 ( ﺛﻢ ﺧﻠﻘﻨﺎ ﻋﻠﻘﺔ
ﻓﺨﻠﻘﻨﺎ ﺍﻟﻌﻠﻘﺔ ﻣﻀﻐﺔ ﻋﻈﻤﺎ ﻓﻜﺴﻮﻧﺎ ﺍﻟﻌﻈﻢ ﻟﺤﻤﺎ ﺛﻢ
ﺍﻧﺸﺄ ﻧﻪ ﺀﺍ ﺧﺮ ﻓﺘﺒﺮﻙ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﺣﺴﻦ ﺍﻟﺨﻠﻘﻨﻲ ) 14 ( ﺍﻟﻢ
ﻣﻨﻮ 13- 12 :
(Hakika mun halicci mutum daga tsantsar
tabo sanna muka sanya shi digon maniyyi a
cikin wata matabbata amintacciya. Sai muka
kashi sannan muka lullube kashin da nama,
sannan muka samara da shi a wata halitta
dabam. Albarkar Allah wanda ya fi kowa iya
halitta ta yawaita ) Amu’uminun: 12-14
Wannan hadisi ya kawo guda hudu ashe sai
ka dauki nan ka dauki can, sannan ka hada
dan Adam gaba daya. In ka dauki wuri daya
sannan ka hada dan Adam gaba daya in ka
dauki wuri daya ba zaka iya hadaba

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s