ARBA’UNA HADITH (12) HADISI NA SHA BIYU


ARBA'UNA HADITH (12) HADISI NA SHA BIYU
An karbo daga Abu Hurairata yace, Manzon
Allah (S.A.W) yace, yana daga kyawun
musulunci mutum barin abinda baya da
mahimmanci, a gare shi tirmizi da Ibnu
Majah ( 2318) ( 3976).
SHARHI;
Fadin manzon Allah (S.A.W) cewa yana daga
mahimmancin kyawun musuluncin mutum
barin abinda baya da mahimmanci a
gareshi ke nuna kyautatuwar to a rabu da
shi wannan shi ke nuna kyautatuwar
musulunci ka wannan muhimmancin ta
fuskar addini ne amma ta fuskar duniya,
duk abin da bashi da mahimmanci a
duniyance to kyawun musuluncinka shi ne
barin wannan al’amarin amma duk abin da
yake mahimmanci o ta fuskar addini ko ta
fuskar duniya to wannan ana bukatar ka
neme shi, dama an halicce ka ne domin
ibada Allah yanace wa
ﻭ ﻣﺎ ﺧﻠﻘﺖ ﺍﻟﺠﻦ ﻭ ﺍﻻ ﻧﺲ ﺍﻻ ﻟﻴﻌﺒﺪﻭﻥ ( ) ﺍﻟﺬﺍ ﺭﻳﺔ :
(ban halicci mutum da Aljan ba sai don su
bauta mini) (Azzariyat)
In ta fuskar duniya ne, Allah yace,
ﻻ ﺗﻨﺲ ﻧﺼﺒﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﺪ ﻧﻴﺎ ( ﺍﻟﻘﺼﺺ88 : )
(Kada ka manta da rabonka daga duniya )
Alkasaas 77)
Amma duk abin da baya da mahimmanci a
dunia ko layhiya to yana daga kyautatar
imani mutum ya bar wannan shirmen ya
kama abin da zai amfane shi ko a duniyarsa
ko a lahirarsa wadansu suna kafa hujja da
wannan hadisin cewa idan muna
tattaunawa ni da wani ta addini sai wani
yazo ya tsoma baki sai mucew ai Annabi
(S.A.W) yace, yana cikin kyawun musulunci
mutum ya bar abin da bai shafe shi ba don
haka bad a kai muke Magana ba, don me
zaka tsoma baki ? ba haka hadisin yake nufi
baa bin da hadisin yake nufi shine lallai
mutmu ya bar abinda bashi da mahimmanci
ba wai abin da bai shafe shi ba domin
tattaunawar da kuke yi ko dai ta zamanto
tana da alaka da ibada, to ta shafe ni don ni
ma musulmi ne ina dangatuwa zuwa ga
wannan addini ko zamanto tana da alaka
da duniya in na sani dole in tsoma baki a
ciki ko ya zamanto a aikin sabo kuke, ya
wajaba a gareni in hani daga mummunan
aiki to don me za kaec bat a shafe nib a? ta
kowacce fuska maganr ta shafeni sai dai
idan asabo kuke na yi umarni kuka ki bari
sai in bar wajen, wannan hadisin Imamu
Tirmizi ya waito shi da sauran wadansu
malaami kamar Ibnu Majah da Imamu
Ahmad acikin Musnad,amma shi ya rawaito
shi ya bata fuskar Abu Hurairata bat a
fuskar hasan Bin Aliyyu Bin Abi Dalib ya
rawaitos hi Hadisi ne ingantacce.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s