ARBA’UNA HADITH (24) HADISI NA ASHIRIN DA HUDU


ARBA'UNA HADITH (24) HADISI NA ASHIRIN
DA HUDU
An karbo daga Abu zarri Al’gifari R.A daga
Annabi s.a.w cikin abin da Annabi ke
rawaitowa daga wurin Ubangijinsa lallai
Allah madaukakin Sarki yace, yak u bayina
na haramta wa kaina zalunci kuma na
sanya zalunci ya zamas abin haramtawa a
tsakanin ku yaku bayina dukkaniku batattu
ne, sai fa wanda na shiryar da shi ku nemi
shiryarwata ni kuma in shiryar da ku yak u
bayina dukkaniku mayunwata ne sai wanda
na ciyar dashi, don haka ku nemi
shiryarwata ni kuma in shiryar da ku don
haka ku nemi ciyarwata, ni kun azan ciyar
daku yaku bayina, kowanenku tsirara yake
ba tufafi sai wanda na suturta ku nemi
suturata, zan suturtar da ku, yaku bayi zan
suturtar daku ku. Ya bayina ! kuna yin laifi
dare da rana ni kuma I nagafarta zunubai
gaba dayansu ku nemi gafarata ni kuma
zan yi muku gafara din nan yaku bayina ba
ku isa ku cutar dani ba ballantana kuce
zaku cutar dani baku isa ku amfanar dani
ba, ballantana kuce zaku amfanar dani yaku
bayani da ace na farkonku da na karshenku
da mutanenku da aljannunku ku kasance a
bias ga zuciyar wani mutum daya cikinsu
mafi jin tsoran Allah hakan ba zai kafa
komai a cikin mulkina ba, yaku bayina da
ace na farkon ku da na karshen ku da
mutanen ku da aljannuku ku kasance a bias
zuciyar daya mafi fajirci hakan ba zai rage
komai dangane da mulkina ba, yaku bayina
da ace na farkon kuda na karshen ku da
mutanen ku da aljanunku su tsaya a bigire
daya, ni kuma kowanne ya roke ni kuma
kowanne daya daga cikinku in bashi abin
day a roka hakan ba zai rage komai daga
cikin abin kee wurina ba sai fa
gwargwadon abin da allura ta rage idan an
tsoma ta cikin rowan teku yak u bayina
kadai ayyukan ku nake kididdige wasu
agare ku sannan in na cika muku ladanku.
Wadanda ya samus alheri, ya gode wa Allah.
Wanda ya sami wanin haka, kar ka ya zargi
kowa sai kansa.
Muslim ne ya rawaito shi.
SHARHI
Wannan hadisil kudisi kenan shi ma wahayi
ne daga Allah. Bambancinsa da ayar
Alkur’ani shine alku’ani ana karanta shi a
acikin sallah amma hadisin kudisi ba zai
yiwu ka karanta shi kayi sallah ba. Dole sai
Alkur’ani duk da cewa kowanne daga allah
s.w.t yake ana samun lada ta hanyar tilawar
Alkur’ani mai girma an bautar dam u mu
karanta Alkur’ani mu sami lada amma
hadisul kudusi ba haka bane, Alkur’ani an
kalubalanci duniya da su kawo irinsa a yi
takara dashi amma hadisul kudisi ba ‘ayi
kalubale dashi ba.
Akwai bambaci da wadansu suke fada sai
suce Allah yayi alkawarin kare Alkur’ani
amma baiyi alkawarin kare hadisul kudusi
ba. Wanan kuskure ne Ubangiji Ta’ala yayi
alkawarin kare shari’ar musulunci shari’ar
musulunci kuma itace Alkur’ani da sunnah
yadda Allah yayi Alkawarin kare Alkur’ani
haka yayi alkawarin kare hadisi.
Dangane da fadin Allah s.a.w da yazo a
wannan hadisin cewa, yaku bayina na
haramta wa kaina zalunci kuma nasanya
zalunci ya zama abin haramtawa a
tsakaninku, wannan ya na nuna nufin bai
halattar wani yayi zalunci wani a cikinsu ba,
kada bada dama zalunci iri biyu ne. na farko
shine zalunci mafi tsananis wato shirka,
bauta wa wanin Allah. Domin Asalin kalmar
zalunci na karshe, kenan a duniya kamar ka
kirayi wani ba Allah ba. Da nufi ya baka
amfani ko ya kore maka wata cuta don
haka Allah yace
ﻭﻻ ﺗﺎﺩﻉ ﻣﻦ ﺩﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎ ﻻ ﻳﻨﻔﻌﻚ ﻭﻻ ﻳﻀﺮﻙ ﻓﺈﻥ
ﻓﻌﻠﺖ ﻓﺈﻧﻚ ﺇﺫ ﻣﻦ ﺍﻟﻈﻠﻤﻴﻦ
(Kar ka kirayi wani wanda ba Allah ba,
wanda bashi cutar dakai, bashi iya amfanar
daka idan kuwa ka aikata to kai ka zama
cikin Azzalumai) Yunus 106.
Don haka Allah yace,
ﺇﻥ ﺍﻟﺸﺮﻙ ﻟﻈﻠﻢ ﻋﻈﻴﻢ
(hakika shirka zalunci ne mai girma)
Lukman 13)
Na biyu kumna shi ne zalunci karami aikata
ayyukan sabo kamar shan giya, da zina da
caca duk wadannan zalunci ne, wanda duk
yayi wannan ya zalunci kansa, amma
girman wannan bai kai wancan kashin na
farko ba. Wannan zalunci ne wanda in
Ubangiji yaga dama ya yafe ma laifin da kayi
din wannan tsakaninka da shi in ya ga
dama ya dandana maka maka azaba
gwargwadon yadda ka cancanta sannan
daga karshe a cire ka a kai aljannah. Don a
cikin ‘yan aljanna akwai azzalumai wadanda
sun zalunci kansu, amma dai daga karshe
za a kasu aljanna.
Da Allah yace, yaku bayina dukkaninku
batattu ne, sai fa wanda na shiryar dashi ku
nemi shiryarwata ni kuma in shiryar daku,,,
wani zaai kai kamar yaci karo da wani
hadisin daban don yace dukkaninku battatu
ne sai fa wanda na shiryar dashi amma a
hadisin bukhari (Bukhari) 1358 da Muslim
kuma daga Abu Huraira cewa yayi, duk
wani wanda aka haife shi ne akan
musulunci ko a akan fidira wanna kuma
yace, dukkaninku batattu ne¸sai fa wanda
na shiryar, dashi bacin karo da juna a
tsakanin su malamai suka ce tsarkin yana
nan amma tsarkin kadai ba zai wadatar ba
sai idan wahayi ya zo an karba waahayi to
kuma kana nan cikin bata da shi in kakai
karbar wahayin to kuma kana nan cikin
bata da dimuwa har sai lokacin da ka koyi
wahayin wannan shi ne abin da Allah yake
nufi da dukkaninku batattu ne sai wanda
na shiryar dashi sai dai zai iya lalacewa idan
mutum ya tsaya a wurin da jahilci ya yi
yawa sai ya cakude ya gamu da duhu ba,
yadda za ‘ayi ya samu haske sai in hasken
wahayi ya zo sai ya zamanto haske akan
haske,
Shi kuwa fadin Allah hakan ba zai rage
komai dangane da mulkina ba, yana nuna
bunkasar mulkin Allah ta’ala kenan duk mai
mulki yana bunkasa ne da dawaki da
fadawa amma Ubangiji haka yake shi kadai
bashi da abokin tarayyabaya bukatar komai
shi kuma fadinsa cewa ayyukanku ina
kiyaye su sannan in cika muku su yana
nufin a nan duniya zan kama ku da azaba a
sakamakon wani zunubi da kayi, sai a
doramaka ciwon kai don a kankare maka
wannan kuskuren da kayi jiya ko shekaran
Jiya ba kasami ko shekaran jiya ba ka da
laifin komai Allah ya riga ya tace ka daga
zunubi saboda wahalhalun day a dora
maka. Wadansu suka ce a’a wannan
hukuncin a lahira ne.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s