ARBA’UNA HAADITH (31) HADISI NA TALATIN DA DAYA


ARBA'UNA HAADITH (31) HADISI NA TALATIN
DA DAYA
An karbo daga Abu Abbas Sahlu dan sa’ad
Assa’idi (R.A) y ace “Wani mutum ya zo
wajen Annabi (S.A.W) ya ce “Ya Manzon
Allah! Nuna min aikin da idsan na aikata shi,
Allah zai kaunace ni, mutane ma za su
kaunace ni.” Sai (Annabi (S.A.W) ya ce ”Ka yi
zuhudu cikin lamarin duniya, sao Allah ya
kaunace ka, kuma ka nisanci abin da ke
hunnun mutane, sai mutane su kaunace
ka” (1) Ibnu Majah ne ya rawaito shi (#
4102) da waninsa ta hanyoyi masu kyau.
SHARHI;
Su mutane, idan za ka mika hannu, sai su
tsane ka; yau ka tambaya gobe ka tambaya,
jibi ka tambaya. Amma in ka kame
hannunka shi kenan, sai ka tsira lafiya a
gurinsa. To abin da ake nufi da, “Ka yi
zuhudu cikin lamarin duniya….” Shi ne ya
kasance mutum ya dauki duniya ba komai
ba, abin da kawai zai bukata a cikin duniya,
shi ne dukk abin da yake wajibi, larurar
zrayuwa, abin da rayuwa take bukata kafin
ta gudana a gidan duniya, wanda zai zamar
maka dole a rayuwa shi ne ake bukata,
lalurar ayuwa ne ya kasance mutum ya
samu halin da zai yi aure, don ya sami
matar da za ta katange shi daga afkawa
cikin laifi, larura ce ta rayuwa ka sami cid a
sha; larura ce ta rayuwa samuns gida
mahallin da za ka zauna, ba sai ka zauna
haya ba. Idan gari yana da girma, ba zai
yiwu ba dole sai kana daabin hawa. Saboda
haka abin da ake nufi da suhudu, shi ne
abin da yake dolene a rayuwa ya kasance
ka same shi, kar ka ce ka damu da nafilar
rayuwa. To idan ka yi haka, sai Allah ya so
ka. In ka fifita duniyarka a kan lahira, to
wannan karshenta zargi ya zo. Duk dinda
aka zargi duniya, to ana zargin ne a
mutanen da suka fifita lahira akan duniya,
insun samu duniyasuna amfani da komai,
amma da wani abu yazo na lahira, suna
fifita shi sama da komai. To wannan shi ne
karshen zuhudu. Ba kamar yadda muke
daukar yadda sufaye suka kawo zuhudu ba,
cewa shi ne idan ka sami abinci mai kyau
kar ka ci, sai kwannne ya fara wari, wai
saboda gudun duniya. Wannan bay a cikin
abin da yake zuhudu wanda shari’a ta
amince ka yi zuhudu a cikinsa.
(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI
SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s