ARBA’UNA HAADITH (35) HADISI NA TALATIN DA BIYAR


ARBA'UNA HAADITH (35) HADISI NA TALATIN
DA BIYAR
An karbo daga Abu Hurairata (R.A) y ace
Manzon Allah Annabi (S.A.W). y ace “Kada ku
rika yi wa juna hassada, kada ku yi kore
kada ku kiyayya da juna, kada ku juya wa
juna bayanku, kada sashenku ya yi ciniki a
cikin cinikin dan uwansa. Ku kasance bayin
Allah ‘yan uwan juna. Muslim dan uwan
muslim ne, kada ya zalunce shi, kada ya
kuntatar da shi, kada ka yi masa karya, kada
ya wulakantar da shi. Tsoron Allah yana nan
(har sau uku).!! Yana nuna kirjinsa,” Ya ishi
mutum sharri, ya rika tozartar dad an
uwansa musulmi. Jinin kowanne musulmi
da dukiyarsa da mutuncinsa, haramun ne a
kan musulmi.(1) Muslim ne ya rawaito shi (#
2564).
SHARHI;
Abin da ake nufi da hassada shi ne ka rika
burin ina ma ni’imar da wane yake cikinta
taho ta barshi ina ma dukiyar wane ta ragu
jarinsa ya lalace ka rinka jin ina ma
mukamin da ka baiwa wane yazo ya rasa to
wannan itace hassad kuma siffa ce ta
yahudu sun fi kowa sanin Annabi da
siffofinsa amma hassada ta hana su yin
imani dashi don haka, kayi kokarin ka
wanke zuciyarka daga yi wa dan’uwanka
musulmi hassada. Ko da mutum yana
kokarin yin takara da kai kan wasu al’amura
na duniya kai kar kayi takara dashi lallai
mutum ya kasance ya tarbiyatar da kansa
da haka.
Dangane da cewa,''….kada ku yi cinikin zure
….''kai ne kana da rumfa a kasuwa kana
sayar da jakunkuna sai nazo zan sayi jaka
muna ciki ciniki kace naira dari biyu ni
kuma inacewa naira tamanin kawai sai
wani dan kore yazo ya dauki irin wannan
jakar yace don Allah ka sayar min da
wannan jakar dari da hamsin, “ Shi wanda
yazo yayi hakan din yayi ne fa don saboda
ni yace Dari da hamsin ka sayar ? yace ‘aa’
to dari da sittin da biyar wai dole sai ya
zurma ni na shiga a yi dakyar a sayar masa
dari da saba’in bayan kuwa ciniki ne na
bogi na karya ba gaskiya bane, don kawai
ni in kai dari da saba’in, farashinta kuwa
naira tamanin towannan shi ne kore, kuma
duk malamai sunyi ittifakin haramcinsa
dangane da yiwuwar cinikin kuwa,
wadansu suka ce yayiwu wadansu kuma
suka ce bai yiwu ba sai dai mafi ingancin
magana, cinikin ya yiwu don shi wanda
yazo wanna tayi ai ba da shi muka yi ciniki
ba wannan shi ne abin da imamu Malik Bin
Anas yace. Amma idan daga baya ka gane
cewa wancan dan kore ne to kana da dama
ka fiot ka mayar kace baka so a baka
kudinka kuma dole ne a baka. In kuma ka
ce shi kenan kai ka hakura kana son abin
haka, ba komai ya halatta.
Abu na uku Annabi yace, kada ku zamanto
masu kiyayya da juna kaje kana fushi da
wani shi ma yana fushi da kai, wannan ma
ba’a so abin fushi idan ya faru, to ayi hakuri
a rarrashi zuiciya s ta hakura da manzon
Allah yace kada ku juya wa juna bayanku
yana nufin kar ku kaurace wa junanaku, ku
yanke mu’amala da juna in dai an fara
mu’amala kar ayanke ta a ci gaba sai in an
riga an cuce ka ne to idan akazo za sake
zaunawa sai kace aa ai rannan ka cuce ni
ba zan yarda ba. Sallah dai muyi tare, da
Azumi komai ma muyi tare sai kuma
Manzon Allah yace kada sashenku yayi ciniki
acikin dan uwansa abin nufi idan mu biyu
muna da haja ta kasuwani da muke
sayarwa idan kwastoma ya shigo rumfata
muna tsaye munacinikayya na sa masa suna
yana tayi, to bai halatta ba kazo ka juye
kwastoma nan kace, zo mana in sayar maka
kasa da yadda ya baka. Bangare na biyu
idan ni saye nake a wani wuri, nazo ina
sayen kaya, an sami suna ina yin tayi bai
halatta ba wani shi ma ya shigo yace shi ma
zai sayi wannan kayan sai har ni na bari
ba’a daidaita ba
Daga kashe manzon Allah yace, ku kasance
bayin Allah ‘yan uwan juna musulmi dan
uwam musulmi ne kada ya zalunce shi kada
yayi masa karya kada ya kunyatar dashi ko
kaki taimakonsa in ya nemi taimakon ka ka
taimaka masa, kada ka wulakantar da shi
wai don talaka ne ka bashi matsayinsa da
ya dace dashi Aisha (R.A) tana cewa an
umarce mu sauke kowanne mutum a
matsayinsa. Manzon Allah ya karasa cewa “
ya ishi mutum sharrin ya rinka tozarta da
dan uwanka musulmi don talaucinsa ko
don karamin ma’aikaci ne ko don dan
makaranta ne kauda nba ko komai bane.
Snnan sai yace,''….Jinin kowanne musulmi
da dukiyarsa da mutuncinsa haramun ne a
kan musulmi.'' ma'ana, kowne musulmi
game da musulmi dan uwansa, haramunne
ya zubar da jininsa, ko ya cinye dukiyarsa,
ko ya zubar da mutuncinsa. Shi ne, ko ka
zge shi ko ka la'anceshi ko ka jefe shi da
laifin da bai yi ba ka yi gini bisa ga zato
haka kawai. To wannan duk dai bai haltta
ba.
(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI
SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s