ARBA’UNA HAADITH (36) HADISI NA TALATIN DA SHIDA


ARBA'UNA HAADITH (36) HADISI NA TALATIN
DA SHIDA
An karbo daga Abu hurairata (R.A) daga
Annabi yace, wanda duk yakutar wa
mumini wani bakin ciki daga bakin cikin
duniya to Allah zai kautar da masa da wani
bakin ciki daga bakin cikin irin bakin
kiyama duk wanda ya kawo sauki ga
wanda yake cikin tsanani, Allah zai kawo
masa sauki a duniya da lahira, wanda ya
suturce musulmi to Allah zai yi masa sutura
a duniya d alahira lallai Allah yana cikin
taimakon bawa matukar bawan ya kasance
mai taimakon dan uwansa musulmi wanda
duk ya kam wani tafarki yana neman ilmi a
wannan tafarkin Allah zai saukaka masa
hanyar shiga aljanna babu wasu mutane da
zasu taru a cikin wani daki cikin dakunan
Allah sun karanta littafin Allah, sun
darasinsa a tsakaninsu da juna, face sai
nutsuwa ta sauka kansu, rahama ta lullube
su, (mala’iku sun kewaye su) sai kuma Allah
ya ambace su fadarsa. Wanda duk aikinsa
ya yi sanda da shi, to dangatakarsa ba zai ta
yi gaggawa ba zatayi gaggawa da shi ba.
Muslim ne rawaito shi (2699) da wanan
lafazi.
SHARHI;
Manzon Allah yace, wanda duk ya kautar wa
mumini wani bakin ciki daga dangin wani
bakin ciki da ke iya samun mutu ma duniya
to Allah zai kautar masa da wani bakin cikin
daga cikin bakin cikin da kan iya riskar
bawa a gobe kiyama misali wni mutum
mumini yana fama da matsala ta rayuwa sai
ka taimaka masa ka yaye masa wannan
bakin cikin ; an rubuta masa magani a
asibiti bashi da kudin da zai saya sai kaje ka
sayo ka bashi, an bashi notis a gidan haya
sai kazo ka bashi kudin da ake binsa ka
kara masa kudin ko aka sallame shi daga
gidan haya, sai kazo ka bashi kudin da ake
binsa ka kara masa kudin hayar na wata
hudu a kai masu zuwa. Duk wanda yayi
wannan Allah zai yaye masa wani bakin ciki
daga cikin bakin cikin dangin bakin cikin da
ke iya samun mutum a ranar tashi kiyama.
Sai acan lahira ba ana zai yaye masa ba, a
can zai yaye masa, a inda ba mai yayewa sai
shi (Allah) sanan manzon Allah ya sake cewa
duk wanda ya kawo sauki ga duk mutumin
da yak e cikin tsanani Allah zaikawo mas
asauki a duniya da lahira misali mutu mne
ake cikin tsanani si ka bashi sauki kamar
mutum ne ana bin sa bashi sai ka taimaka
masa ka biya ka ga cikin tsananin kenan
yake, kai kuma sai ka kara masa lokaci kace
bari sai wata na gaba in yai ka biya ko wata
biyu, ko wata uku masu zuwa. Domin ba
cewa bari sai lokacin da ka samu ka kawo,
ba ayin wanan dole sai an kayyade lokaci
sai daif nyasa, sai a kara masa wani lokacin,
ba aa yin bashi da cewa in kasamu ka
kawo, Allah yana cewa
ﻭ ﺍﻥ ﻛﺎﻥ ﻭ ﻋﺴﺮﺓ ﻓﻨﻈﺮﺓ ﺍﻟﻰ ﻣﻴﺴﺮﺓ ﻭﺍﻥ ﺗﺼﺪ ﻗﻮ
ﺧﻴﺮ ﻟﻜﻢ ( ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ 280
(ida mutum yana cikin tsanani to ayi masa
jinkiri zuwa lokaci da ya smau, wanda kuwa
yafe, to wanan shi ne yafi alheri.
Fadin manzon allah cewa wanda duk ya
kama wani tafarki yana neman ilmi a
wannan tafarki zai saukaka masa hanyar
shiga Aljanna wannan yan nuna falalar
neman ilmi kenan duk wanda ya kama
hanayr neman ilmi to sai Allah ya saukaka
masa shiga Aljanna ta cikin ruwan sanyi ba
wahala. Duk wanda ya tsaya a jahilci kuwa,
to sai an rufe masa kofar gidan Aljanna a
nan ba ya nufin sai ka zamanto tun safe
zuwa dare kana neman ilmi, alal akalli k
ataso daga karfe biyar kaje ahalari kaje ka
koya, ba karamin Alheri bane kada kace kai
ka yi girma da koyan karatu, wanan itace
hanyarka ta shiga aljanna.
A karshe hadisin manzon Allah yace wanda
duk aikinsa yai sanda da shi to
dangatakarsa ba zata yi gaggawa dashi ba.
A ranar tashin alkiama baabin nufi anan
gidan duniya za a ce wane dan wane ne za
yi masa alfarma a lahira babu alfarma sai
dai wa yazo da imani da aikin na gari ba
mai tsira sai wanda yake ye jewa Allah da
imani da aiki na gari wanan shi ake bukata
don haka duk dangatarkar mutum, ba zata
karamasa komai ba shi yasa Annabi yace
cewa ku ‘yayan banu Abdulmudallii ku
tsamar da kanku daga wuta domin ba zan
amfana muku koma ba ku ‘yayan banu
hashim ku tsamar da kanku daga wuta ya
Fadimatu bintu Muhammad tambaye ni abin
da kike so a cikin dokiyata ba zan iya
wadatar miki da komai ba a ranar alkiyama
(Duba sahih Al-Bukhari) sahih Muslim (204)
don haka dangantaka bata da amfani a
gidanlahira sai in ka yi aiki na gari in kaga
dangataka tayi amfani to an shiga Aljanna
idan da da iyayensasun shiga aljanna wani
benen sama kamar uba yana sama yaro na
benen kasa sai ace bari a dadada wa
ubanin sai a tura dan yaje wajen ubansa
duk da dan bai yi aikin da zaije gurin da
uban yake ba Allah yace
ﻭ ﺍﻟﺬ ﻳﻦ ﺀﺍﻣﻨﻮ ﻭﺍﺗﺒﻌﻬﻢ ﺫﺭﻳﺘﻬﻢ ﺑﺎ ﻳﻤﻦ ﺍﻟﺤﻘﻨﻨﺎ ﺑﻬﻢ
ﺫﺭﻳﺘﻬﻢ )16 ( ﺍﻟﻄﻮﺭ
(Wanda suka yi imani kuma zuriyarsu tabi
su akan imani mun riskar da su tare dasu)
Addur 21)
Amma in uba yana cikin aljanna da yayi
aikin d za kaishi wuta to ba a fito dashi
daga wuta don mahaifinsa matukar ya
mutu kafiri zai dauwama a wuta mahaifinsa
ba zai iya tsamo shiba.
(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI
SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s