ARBA’UNA HAADITH (46) HADISI NA ARBA’IN DA SHIDA


ARBA'UNA HAADITH (46) HADISI NA ARBA'IN
DA SHIDA
An karbo daga dan Abu Burda daga
babansa daga Musal Ash’ariy (R.A) yace
Annabi ya tura shi kasar Yemen sai ya
tambaye shi dangane da wani abin sha da
ake yi acan sai yae menene abin? Sai yace “
Albit’u da Almizru “ sai akace da Abu burda
menene Albit’u sai yace, wani tsimi ne da
ake yi da zuma, almizru kuwa wani tsimi ne
da ake yi da alkama. Sai Annabi yace, duk
abu ma sa maye haramun ne Bukhari ne
rawaito shi. (4343) .
SHARHI;
Da manzon Allah yace duk abu mai sa maye
haramun ne sai malamai suka ce abin da
yake sa maye abu biyu ne: awaki abin da
yake sa maye ya kuma sa ka walwala da jin
dadi, giya tana sa maye tana sa walwala da
jin dadi wani farin cikin na babu gaira ba
dalili to wannangiya kenan ittifakin
haramun ne amma akwai abin da zai sa
kamaye ba walwala suka ce wannan bai
zama haramun ba. Idn za ayi wa mutum
aiki a asibiti likitoci ai suna dirka masa
allura yaji bai san ida yake ba. A wannan
lokacin ai bashi da hankali dun dangi an
yarda bai san ind ayake ba shi ma haka bai
san yadda yake cikin ba amma
bambancinsa da dan giya dan giya sha da
gwangwajewa da yake yi shi kuwa ba ya
cikin jin dadi, yana cikin wahala akwai
mgabatan da suke cwa duk abin da yake sa
maye ko yasa walwala ko bai sa walwala ba
shi ma haramun ne wadansu suna da
wannan fatawar cikin manyan malamai da
suka gabata, cikin sahabbai, da tabi’ai da
tabi’ut tabi’in a gaskiyar al’amari duk abin
da zai sa maye din na wato na tilas ba na jin
dadi ba y adauke maka hankali to wannan
ba giya bane, wadanda suka haramta shi
galibi suna cewa ba a so mu bude kofa, in
mun bude kofa din sai mutum ya sa a kawo
masa barasa ya sha, to wannan shi ya sa
suke haramtawa.
(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI
SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s