ARBA’UNA HAADITH (49) HADISI NA ARBA’IN DA TARA


ARBA'UNA HAADITH (49) HADISI NA ARBA'IN
DA TARA
An karbo daga Umar dan Khaddab (R.A)
daga Annabi yace da ace kuma dogara ga
Allah hakikanin dogaro da shi da Allah ya
azurta ku kamar yadda yake azurta
tsuntsaye. Suna sammako da yunwa amma
suna dawo wa da yamma suna koshe.
Imam Ahmad da Tirmizi da nasa’I da Ibnu
Majah, da Ibnu Hibban da Imam Ahmad da
Tirmizi da nasa’I da Ibnu Majah da Ibnu
Hibban da Ahmad (2344) da Nasa’I a cikin
sunan Alubra (J8/sh 79) Da hakim (418)
Tirmizi yace, hadisin ne ingantacce.
SHARHI;
Tsuntsu ba ya ajiye abincin gobe. In yaje
yau. Yayi kiwo shi kenan gobe kuma ya bar
ta ga hannun Allah. A nan ba wai ana nufin
kada mu ma mu ajiye abincin gobe. Ba ba
haka hadisin yake nufi ba. Abi da hadisin
yake nufi ,irin yadda tsuntsu ya dauka cewa
in ya fita da safe,Allah zai bashi to lallai ka
dauka cewa in ka fita ka nema, lallai
Ubangiji na iya baka irin yaddayake wa
tsuntsu Ma’ana ya zamanto zuciyarka ta
rayayu da cewa Allah zai baka, ban dashi ba
mai baka, kuma gabbanka suna aiki tukuru
don neman abin gurin Allah. Wannan shine
tawakkalin da ake so.
(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI
SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s