KANASON ALJANNAH CIKIN SAUKI?? TO GA MAFITA……..


Abdullahi Muhammad Auwal
KANASON ALJANNAH CIKIN SAUKI??
TO GA MAFITA……..
Manzon Allaah sallallaahu alaihi wasallam
yana cewa:
( ﻣﻦ ﺳﻠﻚ ﻃﺮﻳﻘﺎً ﻳﻠﺘﻤﺲ ﻓﻴﻪ ﻋﻠﻤﺎً؛ ﺳﻬّﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻪ ﺑﻪ
ﻃﺮﻳﻘﺎً ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨّﺔ ) ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ .
A wani hadisin kuma yana cewa:
( ﻣﻦ ﺳﻠﻚ ﻃﺮﻳﻘﺎً ﻳﻄﻠﺐ ﻓﻴﻪ ﻋﻠﻤﺎً؛ ﺳﻠﻚ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻪ
ﻃﺮﻳﻘﺎً
ﻣﻦ ﻃﺮﻕ ﺍﻟﺠﻨﺔ ). ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺻﺤّﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .
Ma’ana: (Duk wanda yabi wata hanya ko ya
ri’ki wata hanya wanda yike neman ilmi a
cikinta; to Allaah zai sau’ka’ke yakuma
yassare mishi da wannan ilmin hanya zuwa
Aljannah).
Wannan hadisin ya nuna mana girma da
falala da ilmi ke dashi, daga cikin falalar –
wadda kuma itace mafi girma – shine samun
Aljannah.
Sai dai wannan hadisin yana maganane
akan ilmi na shari’ah kamar yadda wasu
malaman suka fassarashi tareda wasu
nassoshin Qur’ani da hadisi, sai dai duk
wani ilmi mai amfani wanda shari’ah ta
yarda dashi shima zai iya shiga karkashin
wannan hadisi mai girma kamar yadda
wasu malaman suka nuna hakan.
Amma mutum bazai samu wannan falalar
ba, sai da sharudda kamar haka:
1- Yi dan Allaah.
2- Bin dokokin Allaah a cikinsa.
3- Aiki da ilmin.
4- Kokarin amfanar da al’ummah da ilmin.
MUNA FATAN ALLAAH YASA MUNA CIKINSU,
WADANDA KUMA BASU KAMA HANYAR ILMI BA
ALLAAH YASA SUGANE.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s