SAKON KHUDUBAR JUMU’AH DAGA MASALLACIN MANZON ALLAH (SAW) DA YAKE MADINAH DAGA BAKIN DR SALAH BN MUHAMMAD AL-BUDAIR (HZ) TA YAU JUMU’AH 26/04/1437AH (05/02/2016CE).


SAKON KHUDUBAR JUMU’AH DAGA
MASALLACIN MANZON ALLAH (SAW) DA YAKE
MADINAH DAGA BAKIN DR SALAH BN
MUHAMMAD AL-BUDAIR (HZ) TA YAU JUMU’AH
26/04/1437AH (05/02/2016CE).
FASSARAWAR DAN’UWANKU ISA ALI PANTAMI
Wannan Matashin limamin mai shekaru 46
yayi khudubar Jumuah bayan sama da wata
uku da yayi yana fama da jinya ta rashin
lafiya. Yayi khudubar kan “FITINTINUN
MATASA DA WAJIBCIN HADUWAR AL’UMMAH
DA BIYAYYA GA SHUGABANNIN MUSULMAI.”
Ga sakon a takaice:
1) Limamin yayi Muqaddimah da fara
godiya
ga Allah (SWT) akan Ni’imominsa wadanda
suke da yawa, sannan yayi salati da yabo ga
AnnabinSa (SAW) da addu’ar alheri ga
Sahabbansa (RA).
2) Ya tunatar da masallata Musulmai akan
ILMI, da TAQWAH da FAHIMTAR ADDINI na
hakika sune hanyar tsira daga dukkan
fitintinu. Wato dole muyi riko da su don mu
tsira.
3) Sannan yayi bayani kan yarda wannan
kasa mai Albarka “Mamlakah” take dore
akan addini da shari’ar Musulunci.
4) Ya bayyana cewa lalle haduwar al’ummah
(akan gaskiya) RAHAMA CE. Sannan
rarrabuwa sharri ne.
5) Duk da wannan kokari na “MAMLAKAH”
an samu jama’ar da suka yi tawaye suka
fice
daga karkashin shugabanci, sun kashe
Musulmai da wandanda ba musulmai ba.
6) Masu wannan fahimtar duk wanda yayi
magana da (sunan addini) suna bin sa
kawai (ba tare da cikakken ilmi ba).
7) Duk wanda ya taimakawa masu irin
wannan aqidah ta tawaye da barna, tabbas
ya taimaki ‘barna.
8) Sannan masu irin wannan fahimta ta
‘barna galibinsu masu karancin shekaru ne.
9) Limamin ya karanta hadisai na Manzon
Allah(SAW). Daga cikin su, ya karantar cewa
Annabi (SAW) yana cewa: Wanda ya fita
daga Jama’ah, ya raba Jama’ah in ya mutu
yayi mutuwar Jahiliyyah (Muslim ne ya
ruwaito).
10) Masu wannan fahimtar, Jama’ah ne
batattu kamar yadda Sunnah ta bayyana.
11) Limamin yayi bayani akan hatsarin da
iyaye ke abkawa na barin ‘ya’yansu suna
afkawa cikin wadandan fitintinu, da bin
kowa, yara suna kwana a waje, ba tare da
iyayensu sun sani ba, kuma iyayen ba sa
bincike. Duk uban da ya bar ‘ya’yansa haka
lalle yana cutar al’ummah.
12) Akwai hatsari sosai cikin masu zagi da
yawan aibata daular musulunci ta Saudi
Arabia.
13) KHAAWAARIJ (wadanda suke fita daga
yiwa jagororin addinin musulunci biyayya
su
dauki makami) batattun mutane ne.
14) KHAAWARIJ (masu tawaye) kala biyu ne.
1) Akwai wadanda suke zaune, 2) akwai na
tsaye, wadanda suke fita da makamai.
15) Wadanda ke zaune suna karantar da
matasa kashe kawunansu a kasuwanni da
masallatai da sauran wurare.
16) Sannan wadandan matasa masu
karancin shekaru suna aikata irin
wadandan
munanan ayyuka.
17) Limamin yayi kira ga masu raba
Jama’ah
(da kawo irin wadannn fitintinu) da cewa
cin amanar addini ne.
18) Limamin ya tunatar da cewa “Idan mun
yi TAQAWAH (kyakykyawar biyayya ga Allah)
za’a karemu a tunkude mana fitina daga
garemu.
19) Yaku Musulmi ku bi littafin Allah da ya
saukar muku.
20) Sannan yayi tsokaci kan abunda ke
faruwa a Syria da sauran kasashe yadda
ake
kashe musulmai, yara da manya da mata.
21) A Syria yau ana koran mutane daga
gidajen su suna gudu zuwa jeji. Ana koran
tsofi, kuma ana kashe su.
22) Wajibi ne kokari wajen kawo karshen
wadannan fitintinu.
23) Limamin ya yiwa Annabi (SAW) Salati.
24) Yayi adduar Allah ya hadamu a Aljannah
gaba daya.
25) Limamin yayi addu’ar Allah ya taimaki
Musulunci da Musulmai.
26) Yayi addu’ar Allah ya rusa makiya addini
da sauran Daqutai.
27) Limamin yayi addua wa al-Ummar Syria
da Palestine.
28) Yayi adduar Allah ya datar da Imam
kuma Shugabanmu “Khaadimul Haramayn”
da mataimakansa biyu zuwa ga abunda
Allah yake so ya yarda da shi.
29) Yayi adduar Allah ya taimaki sojojin
Musulmai dake filin daga.
30) Yayi adduar Allah ya samu cikin masu
Taqawah.
31) Daga karshe yayi adduar cewa “Yaa
Allah ka amsa mana addu’o’inmu,…
Daga karshe muna addu’ar Allah ya amsa
mana wadannan addu’o’inmu sannan ya
bamu ikon aiki da khudubar,…
(You may wish to share it to get reward.
May
Allah reward you immensely for sharing).

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s