ARBA’UNA HADITH (3) HADISI NA UKU


ARBA’UNA HADITH (3) HADISI NA
UKU
An karbo daga abu Abdurrahman, Abdullahi
dan Umar (R.A) yace na ji manzon Allah
(S.A.W) yana cewa “An gina musulunci a kan
abubuwa guda biyar shaidawa abin
bautawa bisa cancanta sai Allah, kuma
Annabi Muhammad Manzon Allah ne da
tsayar da zakka da azumin watan Ramadan
Bukhari (8) Muslim (16).
SHARHI
Abdullahi dan umar yana ciki mutane
bakwai da suka fi kowa haddace hadisin
Annabi (S.A.W) abin da aka tambayi Annabi
(S.A.W) musulunci sai ya kawo abubuwa
guda biyar kuma su sune dai aka kara
kawowa a nana bin da yake bako a nan
gurin gudabiyu ne: na farko a wancan
hadisin da aka fadi kalmar shahada sai
sallah sai zakka sai hajji sannan akace azumi
sai aka azumi ya zamto karshe to a nan
wurin babu wani bambamci tsakanin can da
nan, domin in aka jeranta abubuwan
wadanda suke iya kididdiguwa da harafin
wawun to wannan harafin ya z one don
tattare wadannan abubuwan wuri guda,
amma ba don nuna wannan na farko bane,
wannan na karshe abu na biyu a hadisin
farko an ambaci wadancan abubuwan guda
biyar kuma sai yace “ an gina musulunci
akan abubuwa biyar sakon da aka isar anan
gurin ana so a nuna shine ayyukan zahiri
ana fassara musulunci dasu wato ayyukan
gabbai kawai da akace ginshikin guda biyar
bay a nuna martabarsu daya: kalmar shada
tafi kowanne karfi, domin duk wanda yaki
kalmar shahada bai yi furuci da ita ba bay a
zama musulmi. Amma mutumin day a yarda
da kalmar shahada sai yazo ya ki sallah
wadansu malamai sukace ya kafirta, akwai
sabani a anan can kuwa ba sabani haka
mutumin da baya bayar da zakka, yana nan
a matsayinsa s na musulmi bai kafita ba sai
dai akwai sabani anan can kuwa ba sabani
haka mutumin dab a sai dai sai in inkarin
wajabcin ya yi amma rashin bayar da ita,
baya fitar dashi daga musulunci kila yace
Allah yace,
ﻭﻳﻞ ﻟﻠﻤﺸﺮ ﻛﻴﻦ )7 ( ﻓﺼﻠﺖ :
(Azabata tabbata ga mushrikai )
Su waye mushrikai a nan sune
ﺍﻟﺬ ﻳﻦ ﻻ ﻳﻮ ﺗﻮﻥ ﺍﻟﺰ ﻛﻮﺓ ﻭ ﻫﻢ ﺑﺎ ﺍﻻ ﺧﺮﺓ ﻫﻢ ﻛﻔﺮﻭﻥ
)7 )
(wadanda bas a bad a zakka kuma sun
kafirce wa ranar tashin alkiyama (Fussilat 7)
Ka ga wannan yana nuna dalilin zamansu
kafirai shi ne kayataw ranar tashin alkiyama
wadanda Abubakar R.T.A) ya yaka ya yake
sun e don ladabtar da sub a wai don saboda
kafirci ne hana zakka ba, a’a don saboda ya
ladabtar da su su dawo musulunci kar su
karya wani rukuni daga cikin rukunan
musulunci.
Musulunci shi ne ayyukan zahiri imani kuwa
kudiri n na zuci sai dai wani lokaci sun
sarkakewa wannan ya dauki ma’anar
wannan kamar yadda za ka gain da dama a
hadisin Annabi S.A.W) kamar yadda Annabi
S.A.W) yake cewa “ Imani yanki ne daidai har
sittin da doriya ko saba’in da doriya mafi
girman shi ne la’ila ha illal lahu, wada yafi
zama na kasa, shi ne gusar da cuta daga
hanyar mutane, (Bukhari (9) Muslim (9) wato
kaga kusa ka dauke jefar don ka da wani ya
taka kaga kwalba ka dauke daga kan hanya
wannan yanki ne na imani kaga wannan
aiki ne gabbai ba kudiri amma Annabi S.A.W)
ya fassara shi da imani don haka suna
sarkakuwa da juna idan sun rabu in sun
hadu kowanne sai yaci gashin kansa.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s