SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!! . ________FITOWA TA 3________


SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!!
.
______FITOWA TA 3________
.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
.
KADAN DAGA CIKIN RABAUTAR DA MAI KIYAYE
SALLAH ZAI SAMU:
.
Haqiqa sallah ginshiqi ce ta rukunnan
musulunci, kuma babu mai kiyayeta face
mumini.
.
Idan ki/ka kiyaye sallarka ka kyautata kamar
yadda aka umurce ka, to Annabi (SAW) Yace:
.
"Farkon abunda za'ayiwa bawa hisabi dashi
ranar alqiyama na daga ayyukansa shine
sallah, idan tayi kyau haqiqa ka rabauta
katsira idan kuma ta 6aci to haqiqa ka ta6e
kayi hasara"
.
[Tirmizi da Dabarani suka ruwaito shi]
.
Saboda haka kenan wannan hadith yana
tabbatar mana idan mun kyautata sallar mu
zamu samu rabauta na daga sauran
ayyukanmu.
.
Annabi (SAW) Yace: "salloli biyar ALLAH Ya
wajabta su skan bayi, wanda yazo dasu bai
tozarta wani abu daga cikinsu ba don
wulaqantawa da haqqin su ba, to akwai
wani alqawari da ALLAH Yayi masa na shigar
dashi Aljannah"
.
[Nasa'i Ya ruwaito shi]
.
Hadith yazo daga Abdullahi dan Umar (R.A)
daga Annabi (SAW) cewa shi watarana ya
ambaci Sallah sai yace:
"wanda ya kiyayeta zata kasance gare shi a
matsayin haske da hujjah da tsira ranar
alqiyama, wanda kuwa bai kula da ita ba
babu wani haske ko hujja ko tsira da zasu
tabbata gare shi ranar alqiyama kuma zai
kasance ne tare da Qaruna, da Fir'auna da
Hamana da Ubayyu dan khalaf"
.
[Ahmad ya ruwaito shi]
.
Daga Abu-Hurayrah (R.A) daga Annabi (SAW)
Yace: "Yanzu da ace akwai wata qorama a
kofar gidan dayan ku, wanda yake wanka a
kowace rana sau biyar acikinta shin kuna
ganin wata dauda zata wanzu a jikinsa? Sai
suka ce: ko kusa babu wata dauda da zata
wanzu a jikinsa, sai yace: wannan shine
misalin salloli biyar, wadanda ALLAH yake
wanke zunubai dasu"
.
[Malaman Hadith sun ruwaito shi banda Abu
dawud]
.
Ya 'Yan uwa shin akwai wata rabauta mafi
farin ciki fiye da samun aljannah???
.
Aljannah ba zata samu ba face sai an kiyaye
ayyuka da kula dasu kamar yadda aka
buqata duk da kasancewar ayyukam mutum
baza su shigar dashi Aljannah ba face sai
ALLAH yaso.
.
Amma kuma ALLAH ne yayi alqawarin idan
mun kiyaye zai shigar damu aljannah.
Saboda haka sai muyi qoqarin kiyayewa
domin mu kasance cikin masu rabauta.
.
Sallah mafificiya ce dole ne a koyi yadda ake
yinta a wajen malamai, ko wanda ya iya,
domin a yau qalu bale ne ga mutanen da
suke gabatar da sallah ba tare da ingantata
ba.
.
Suyita dungurawa wai da sunan suna sallah,
wanda zai yi sallah dole ne yasan hukunce-
hukuncen tsarki da alwala dashi kanshi
Sallah.
.
ALLAH Yasa mu dace Ya kuma bamu ikon
kiyayeta da ingantata. (Ameen)
.
Mu hadu a Fitowa ta 4 inshaa ALLAH.
.
Daga Yar'uwarku:
Faridah Bintu Salis
(Bintus~sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s