Guzuri ga Maniyyata aikin Hajji


Guzuri ga
Maniyyata aikin
Hajji Category: Ra'ayoyin Jama'a Published on Friday, 12 September 2014 00:00 Written
by Sheikh Abdullahi Bala Lau Hits: 355 Ya kai dan’uwana Alhaji, wanda Allah Ya
zabe shi a tsakanin miliyoyin Musulmi,
domin ziyarar dakinSa mai alfarma, ina
rokon Allah da ya jibinci al’amuranka a
Duniya da Lahira, kuma ya sanya ka mai
albarka duk inda kake. Ya kai dan’uwa mai girma, ya kai wanda
ka gamu da wahalhalun tafiya, kuma kayi
hakuri da su, kuma ka fitar da dukiyarka,
kuma ka bar gidanka, ka yi bankwana da
iyalinka da ‘ya’yanka, ba don komai ba
sai domin sauke faralin da Allah ya dora maka, na ziyarar dakinSa mai alfarma,
Allah ya sanya hajjinka karbabbe ne,
kuma ya gafarta maka zunubanka, ya
rufa maka asiri tare da mu gaba daya.
Ya dan’uwana Alhaji, saboda son da
nake maka da sha’awar da kake ba ni, tare da farin cikina da zuwanka, da jin
dadina da kubutarka, ya sa na fuskance
ka da wasu sakonni, saboda in sauke
wani wajibi da ya hau kaina, game da kai,
kuma in kasance na bi umurnin Allah da
ya ce: “Kuma suka yi wa juna wasiyya da gaskiya, kuma suka yi wasiyya da hakuri”.
(asr 3)
Kuma in bi umurnin masoyinmu,
shugabanmu, abin koyinmu, Annabinmu
Muhammad (SAW) da yake cewa:
“Misalin Muminai wurin soyayyarsu da jin kan junansu, da suke yi, kamar misalin
jiki daya ne, idan wata gaba ta kamu da
cuta, sai sauran jikin ya kamu da zazzabi
da rashin barci”. Manzon Allah (SAW) ya
sake cewa: “Mumini ga dan uwansa
mumini, kamar gini ne sashinsa ne ke karfafa sashi”.
dan’uwana Alhaji, kar ka manta da abin
da ya kawo ka wannan gari, wato hajji,
ka sani cewa shi hajji da ma sauran
ayyuka baki daya, Allah ba ya karba, sai
aikin ya zama domin shi a ka yi, da haka ne za ka samu ladan aikin, Allah yana
cewa:
“Kuma ba a umurce su da kome ba, face
su bauta wa Allah, suna masu tsarkake
addini gare shi, suna masu karkata zuwa
addini gaskiya…” (bayyinah 5) Kuma kafin a karbi aiki dole ne ya zama
an yi aikin daidai, bisa sunnar Manzon
Allah (S.A.W), Manzon Allah (S.A.W)
yana cewa: “Duk wanda ya aikata wani
aiki (don kansa) ba tare da umurninmu
ba, to an mayar masa da aikinsa.” Ya kamata tunaninka kullum ya kasance:
Shin an karbi aikinka ko ko a’a?
Maganar aikin hajji kuwa Manzon Allah
(S.A.W) yana cewa: “Ku koyi aikin
hajjinku a wurina”. Wato duk abin da na
yi a cikin aikin hajji to kuma ku yi irin sa, kada ku kago wani abu daga wurin ku.
Aikin hajji mafi kyau da Musulmi zai yi,
shi ne ya yi shi yadda Manzon Allah
(SAW) ya koyar, don ya yi katari da
soyayya daga Allah tare da gafararSa.
Allah yana cewa: “Ka ce: idan kun kasance kuna son Allah,
to ku bi ni, Allah zai so ku, kuma ya
gafarta muku zunubbanku”. (Al Imran 31)
Saboda haka ya wajaba a kanka – ya kai
dan uwa Alhaji – ka koyi hukunce-
hukuncen aikin hajji, kuma ka tambayi malamai kafin ka fara, domin ka yi dace
da sakamako mai kyau a wurin Allah.
Haka zalika Shugaban ya ja hankalin
mahajjata da cewa Su kula sosai yayin
zaman su a birnin Makkah da Madina,
domin Falalar da ke cikin sallah a masallachin Makka da Madina, a duk
lokacin da ka tsinci kanka a wadannan
wurare.
Allah Madaukakin sarki yana cewa a cikin
Alkurani maigirma, “LALLAI dAKIN
BAUTA NA FARKO WANDA ALLAH YA SANYA SHI GA MUTANE DON BAUTA
SHI NE, WADDA YAKE GARIN MAKKA
MAI ALBARKA A KUMA SHIRIYACE GA
DUKKAN HALITTU, CIKINSA AKWAI
AYOYI BAYYANANU…… (suratu Aliimran
96-97). Kamar su makama Ibrahim , Hajarul aswad, dutsen Safa da Marwa,
ruwan Zamzam. Wadannan duk a
bayyane suke, kuma dukkan Masallatan
Duniya babu inda za ka je ka samu
wadannan sai masallacin Haram na
Makkah. An karbo hadisi daga Jabir dan Abdullah
Allah ya kara masa yarda yache Annabi
(S.A.W) ya ce: SALLAH A CIKIN
WANNAN MASALLACINA (MASALLACIN
MADINA), YA FI SALLAH DUBU A CIKIN
WANI MASALLACIN DA BASHI BA, SAI DAI MASALLACIN MAKKA,
(MASALLACIN KA’ABA), DUK WANDA
YAYI SALLAH A CIKIN MASALLACIN
KA’ABA NA MAKKA YANA DA LADA
DUBU DARI (100,000). Ibn Maja:1406.
Shugaban ya ce Amma abin takaici duk da wannan Falala da ke tare a wannan
masallaci, za ka ga wasu sun maida
bakin harabarsa wurin hiran Duniya,
kamar bakin wani otel mai inuwa a bakin
Masallacin, wanda ake kira Daruttauhid,
za ka ga mutane daba-daba ana tattauna matsalar duniya, Wasu na hirar ’yan
kwallo, wasu na hirar siyasa, wasu na
kulla kasuwa, wasu ma suna gidajjen su
suna sharar barci a nan cikin garin
Makkah, in ka musu magana sai su ce
maka ai duk garin Makkah Harami ne, sai su kafa maka hujja da wannan ayar
“Tsarki ya tabbata ga wanda ya tafiyar
dare da bawanSa daga masallaci mai
alfama (Ka’aba) zuwa masallaci mafi nisa
(Baitul Mukaddas) Surah Isra’i 1)).
Masana lissafi sun yi lissafin cewa duk wanda ya yi Sallah a masallacin Ka’aba
koda raka’a biyu ne da kai wanda ba a
wannan Masallacin ka yi ba, sai ka yi
Shekaru kusan 64 kana Sallah Kafin ka
samu ladar da ya samu, ina kuma in ya
samu Sallolin farillai guda biyar? Ina kuma ga yayi ta nafilfili? Ina ma da
karatun Alkur’ani mai girma ka yi ta yi ba
tare da gajiyawa ba? ina ma da azkar ka
yi ta zabgawa da neman rahamar
ubangiji? Lallai da hakan shi ne mafi
alheri a gareka a wannan masallaci mai daraja.
Maniyyata a guji zama a bakin inuwa ana
ta bata lokaci ba tare da yin abin da aka
je yi ba, a dage da ibada, dubban mutane
suna son zuwa wannan wuri Allah bai ba
su dama ba, kai da ka samu dama kada ka yi wasa da damar ka.
Da fatar ni ma da nake wannan rubutu ba
za ku manta da ni ba a wajen addu’oin ku
na alkhairi.
Muna addu’ar Allah ya kai duk wanda bai
je ba ya je ya yi Sallah a wannan masallaci mai tarin daraja, wanda yaje
kuma Allah ya maida shi.
Ina rufewa da Hadisin Manzan Allah
(SAW), inda ya ce “Duk wanda ya yi Hajji,
be yi rafasu ba – wato bai yi Jima’i a
cikinsa ba- kuma bai yi fasikanci ba –wato sabon Allah- zai koma mara laifi kamar
ranar da mahaifiyarsa ta haife shi”
Bukhari da Muslim.
’Yin aikin Umurah zuwa Umurah ana
kankare zunubbai da ke tsakaninsu, shi
ko aikin Hajji karbabbe baya da sakamako se Aljanna.) Bukhari da
muslim”.
“yayin da aka tambaye shi game da
mafificin ayyuka, sai ya ce “ Imani da
Allah da manzonSa” aka ce sai me
kuma? Ya ce “sai jihadi don daukaka kalmar Allah” aka ce sai me kuma? Ya ce”
sai aikin Hajji karbabbe”. Bukhari da
Muslim”.
Muna addu’ar Allah ya karbi ayyukan
Hajjin mu.Wannan rana ita ce shugabar
ranakun Shekara, kuma mafificiya cikin yini, Allah yana saukowa kusa da
bayinSa yana bada garabasar (Bonus)
din Karbar addu’a, shi ya sa Annabi
(SAW) ya ce: “Mafificiyar addua’a,
addu’ar ranar Arfa”. Ina Mana tuni da mu
sanya kasarmu cikin addu’an Allah ya yaye mana musibar da ta addabemu, tare
da rokon zaman lafiya da kwanciyar
hankali a kasar mu da sauran kasashen
Musulmi.
Sheikh Abdullahi Bala Lau.
(National Chairman Jibwis Nigeria). jibwisnigerian@yahoo.com

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s