ME YA FARU A KARBALA? 4 (Dr mansur sokoto)


ME YA FARU A
KARBALA? 4
ASHURA, HUSAINI,
YAZIDU DA KARBALA 4
A cikin babban kundin
tarihin da Ibnu Asakir ya
wallafa ya kawo hadisai
masu dinbin yawa a kan
zagin Yazid kamar
yadda ya al’adanta a
duk wadanda yake
kawo tarihinsu. Sai ka
ga ya kawo ruwayoyi
masu yawa a kan
yabon mutum, sai kuma
ya kawo wasu irin su na
sukar sa. Muradin
mawallafa a wancan
lokaci shi ne tabbatar da
riwayoyin kowane
bangare na masoya da
masoka. Don haka ya
zama dole kowace
ruwaya a jingina ta ga
inda aka ji ta don mai
karatu ya zan cikin
basira. Basu san za a kai
ga irin wannan lokaci da
nassin kawai ake kallo
ba, ba a ma san su
wane ne maruwaitansa
ba.
Wannan shi ya sa sai ka
ga mai yabo ya damfare
ma wadannan riwayoyi,
mai suka kuma yana ta
cika baki da wadancan.
Malaman Sunnah kadai
ne ke iya tantancewa,
su cire aya su raba ta
tsakuwa, kowane
mutum kuma suyi
masa adalci, su ajiye shi
inda ya cancanta.
Wannan ya sa suka
kasance mafi adalcin
al’umma.
Dubi yadda Ibnu
Taimiyyah ya yi wa ‘yan
Shi’ah adalcin cewa,
gara ma akidarku da ta
Khawarij, sai dai
banbancinku da su, ba
sa karya (don sun dauki
yin karya kafirci ne) ku
kuma kuna shara ta
(don a wurinku halas ce
in an yi ta da sunan
Taqiyyah, kamar yadda
Zina take halas a
wurinku idan an yi ta da
sunan Mut’ah).
Kada mu je da nisa.
Hadisan Ibnu Asakir na
zagin Yazid
kaffataninsu Made in
Iraq ne. Ka ga kuwa ga
adalci bai kamata
shugaban da ya ke
Sham a karbi shedun
mutanen Iraqi kadai a
kan sa ba. Ko ba kome
akwai dadaddiyar
adawa a tsakani. Kai
wasu ma in ka sa
hankali kana gane cewa
zuki ta mallau ne. Kamar
Hadisin da ya ce wai
Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam
ya ga Mu’awiyah ya
dauki Yazid, sai ya ce
“Ga dan aljanna can ya
dauko Dan wuta”. To,
ina Mu’awiyah ya ga
Yazid a zamanin Manzon
Allah? Mutumin da a
lokacin ko uwarsa ma
ba a aura ba!
Haka dai makaryata ke
yin lamarin nasu. A
hadisan yabo ma zaka
yi ta ganin irin wannan.
Dubi wani Hadisi da aka
yi ta yawo da shi
kwanan nan a Facebook
wai Annabi Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam
ya daga Hasan da
Husaini ya ce, “Da
wadannan ku ke shiriya,
kuma da su ake maku
kaza da kaza…”. To, ka
ga yaran da aka haifa
bayan an saukar da fiye
da rabin Alkur’ani, an
sha gwagwamarya da
arna, an ci azabarsu, har
an yi hijira kuma an
buga da su ba wuri guda
ba har an ci zarafinsu, a
ce wadannan yaran su
ne zasu shiryar da
wadannan da ke tare da
Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi
Wasallam, wadanda
suka kwashe shekaru
kusan 20 suna dibar
shiriya daga wurinsa, ka
ga wannan ba maganar
da mai hankali ke
saurarawa ce ba. Falalar
da Hasan da Husaini
suka samu ta yin
shahada, da shedar da
kakansu ya bayar cewa
su ne Allah ya basu
mukamin shugabancin
matasa a aljanna,
wannan ya wadatar da
su daga irin wannan
shirme.
Haka zaka ga aya ta
sauka a Makka amma
‘yan Shi’ah su jajirce Ali
take nufi tare da Hasan
da Husaini. In ka ce a’a,
a dai duba domin lokacin
ba a ma aurar da
mahaifiyarsu ba, sai su
ce, ji shi, makiyin
Ahlulbaiti!
To, Yazidu dai wasu
riwayoyi sun zarge shi
da shan giya, wasu
kuma sun wanke shi
tsabal daga wannan
tuhuma. Daga cikin
wadanda suka wanke
shi din kuwa har da
kanin sayyidina Husain,
Muhammad bin Ali bin
Abi Talib Wanda aka fi
sani da Ibnul
Hanafiyyah. Nan gaba
zamu kawo cikakkiyar
maganarsa a kan Yazid
in Allah ya so.
Ku dakace mu an Nima
kadan. In sha Allahu

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s