AL KITABU WAL “ITRA” KO AL KITABU WAS “SUNNAH”? 4 (Dr mansur sokoto)


AL KITAB WAL “ITRA”
KO AL KITAB “WAS
SUNNAH”? 4
Riwayoyin Hadisin
“ITRA”
Ruwaya ta Farko:
Ruwayar sayyidina Abu
Huraira Radiyallahu Anhu
wadda Imam Al Baihaki
ya zo da ita a cikin
SUNAN AL KUBRA
(10/144), Hadisi na
20124 da Imam Al
Bazzar a cikin MUSNAD
(2/479), Hadisi na 8993.
Ga nassin Hadisin Abu
Huraira:
“ﺍﻧﻲ ﻗﺪ ﺧﻠﻔﺖ ﻓﻴﻜﻢ ﺍﺛﻨﻴﻦ
ﻟﻦ ﺗﻀﻠﻮﺍ ﺑﻌﺪﻫﻤﺎ ﺃﺑﺪﺍ :
ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻨﺘﻲ، ﻭﻟﻦ
ﻳﺘﻔﺮﻗﺎ ﺣﺘﻰ ﻳﺮﺩﺍ ﻋﻠﻲ
ﺍﻟﺤﻮﺽ ”.
Fassara:
“Hakika na bar maku
ababe biyu da ba zaku
bace ba idan kun yi riko
da su KITABULLAHI WA
SUNNATI. Kuma ba
zasu taba rabuwa da
juna ba har su same ni a
tafki (Al Kauthar).
Ruwaya ta Biyu:
Riwayar sayyidina Amr
bin Auf Al Muzani
Radiyallahu Anhu wadda
Imam Malik ya kawo ta
a cikin MUWATTA
(1/364), Kitabul Qadr,
Babi na daya, Hadisi na
1594, Ibnu Abdil Barr ya
fitar da Isnadinta a cikin
AT TAMHID (24/331)
da AL ISTIDHKAR
(8/265) haka shi ma
Imam Al Baji a cikin AL
MUNTAQA (4/278). ga
yadda take:
“ ﺗﺮﻛﺖ ﻓﻴﻜﻢ ﺃﻣﺮﻳﻦ ﻟﻦ
ﺗﻀﻠﻮﺍ ﻣﺎ ﺗﻤﺴﻜﺘﻢ ﺑﻬﻤﺎ
ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻨﺔ ﻧﺒﻴﻪ ”
Fassara:
Na bar maku wasu
al’amura biyu da ba
zaku taba bacewa ba
matukar kun yi riko da
su: KITABULLAHI WA
SANNATU NABBIYIHI.
Ruwaya ta Uku:
Riwayar sayyidina Zaid
bin Thabit Radiyallahu
Anhu wadda Imam
Muslim ya ruwaito a
cikin Sahihin littafinsa,
KITABUL FADA’IL, Babi
na hudu kan darajojin Ali
bin Abi Talib, Hadisi na
6378 da kuma Imam
Tirmidhi a cikin SUNAN,
KITABUL MANAQIB, Babi
na 32 kan darajojin
iyalan Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam, Hadisi na
3788.
Ga ruwayar:
“ﺍﻻ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﺈﻧﻤﺎ ﺑﺸﺮ
ﻳﻮﺷﻚ ﺍﻥ ﻳﺄﺗﻲ ﺭﺳﻮﻝ
ﺭﺑﻲ ﻓﺎﺟﻴﺐ ﻭﺍﻧﺎ ﺗﺎﺭﻙ
ﻓﻴﻜﻢ ﺛﻘﻠﻴﻦ: ﺍﺣﺪﻫﻤﺎ ﻛﺘﺎﺏ
ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﻬﺪﻯ ﻭﺍﻟﻨﻮﺭ،
ﻓﺨﺬﻭﺍ ﺑﻜﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ
ﻭﺍﺳﺘﻤﺴﻜﻮﺍ ﺑﻪ” ﻓﺤﺚ ﻋﻠﻰ
ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﻏﺐ ﻓﻴﻪ، ﺛﻢ
ﻗﺎﻝ“ :ﻭﺃﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ، ﺃﺫﻛﺮﻛﻢ
ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺍﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ.”
ﻗﺎﻝ ﻟﻪ ﺣﺼﻴﻦ: ﻭﻣﻦ ﺍﻫﻞ
ﺑﻴﺘﻪ ﻳﺎ ﺯﻳﺪ؟ ﺃﻟﻴﺲ ﻧﺴﺎﺅﻩ
ﻣﻦ ﺍﻫﻞ ﺑﻴﺘﻪ؟ ﻗﺎﻝ: ﻧﺴﺎﺅﻩ
ﻣﻦ ﺍﻫﻞ ﺑﻴﺘﻪ، ﻭﻟﻜﻦ ﺍﻫﻞ
ﺑﻴﺘﻪ ﻣﻦ ﺣﺮﻡ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ ﺑﻌﺪﻩ.
ﻗﺎﻝ: ﻭﻣﻦ ﻫﻢ؟ ﻗﺎﻝ: ﻫﻢ ﺍﻝ
ﻋﻠﻲ ﻭﺍﻝ ﻋﻘﻴﻞ ﻭﺍﻝ ﺟﻌﻔﺮ
ﻭﺍﻝ ﻋﺒﺎﺱ.
ﻗﺎﻝ: ﻛﻞ ﻫﺆﻻﺀ ﺣﺮﻡ
ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ؟ ﻗﺎﻝ: ﻧﻌﻢ .
Fassara:
“Ya ku mutane, Ku
saurara! Ni fa mutum
ne da ana kusa manzon
ubangijina ya zo min da
kira in karba (yana nufin
mutuwa). Kuma ni mai
bar maku abubuwa biyu
ne masu nauyi: Na
farkonsu shi ne littafin
Allah Wanda akwai
shiriya da haske a
cikinsa. Don haka, ku
kama littafin Allah ku yi
riko da shi”.
Sai Manzon Allah
Sallallahu Alaihi WA Alihi
Wasallam ya yi ta
kwadaitarwa da Jan
hankali zuwa ga littafin
Allah. Sannan sai ya ce:
“Da kuma iyalan gidana.
Ina tunatar da ku Allah
a game da iyalan
gidana”.
Husain sai ya tambayi
Zaid, su wane ne iyalan
gidansa? Matansa ba sa
cikin iyalan gidansa?
Zaid ya ce, suna ciki
mana. Amma iyalansa
sun hada da duk
wadanda aka haramta
ma cin zakka a bayansa.
Ya ce, su wane ne? Ya
ce, su ne dangin Ali, da
na Akilu da na Ja’afar da
na Abbas.
Ya ce, duk wadannan an
haramta masu cin
zakka? Ya ce, eh.
Ruwaya ta Hudu:
Ruwayar da Adiyya Al
Ufi ya karbo daga Abu
Sa’id (Ko dai Abu Sa’id Al
Kalbi ko kuma Abu Sa’id
Al Khudri). Wannan
ruwaya tana cikin
MUSNAD na Imam
Ahmad bin Hambal,
hadisai masu wadannan
lambobin: 11119 da
11147. Da kuma
MUSNAD na Imam Abu
Ya’la (2/1021), Hadisi na
1021.
Ga ruwayar:
“ ﺍﻧﻲ ﺗﺎﺭﻙ ﻓﻴﻜﻢ ﺍﻟﺜﻘﻠﻴﻦ
ﺍﺣﺪﻫﻤﺎ ﺍﻛﺒﺮ ﻣﻦ ﺍﻻﺧﺮ :
ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﺒﻞ ﻣﻤﺪﻭﺩ ﻣﻦ
ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﺍﻟﻰ ﺍﻻﺭﺽ، ﻭﻋﺘﺮﺗﻲ
ﺍﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ. ﻭﺍﻧﻬﻤﺎ ﻟﻦ
ﻳﻔﺘﺮﻗﺎ ﺣﺘﻰ ﻳﺮﺩﺍ ﻋﻠﻲ
ﺍﻟﺤﻮﺽ ”.
Fassara:
“Hakika ni mai barin
ababe biyu masu nauyi
ne a cikinku. Dayansu ya
fi daya nauyi: Littafin
Allah da yake igiya ce
mikakkiya daga sama
zuwa kasa. Da iyalaina.
Kuma lalle ba zasu rabu
ba har sai sun zo mini a
tafki”.
Ruwaya ta Biyar:
Ruwayar sayyidina Zaid
bin Thabit Radiyallahu
Anhu wadda Imam
Ahmad ya ruwaito a
cikin MUSNAD, Hadisi na
21578 da 21654 da Ibnu
Abi Shaibah cikin AL
MUSANNAF (11/452),
Hadisi na 32337. Ga
yadda ruwayar take:
“ ﺍﻧﻲ ﺗﺎﺭﻙ ﻓﻴﻜﻢ ﺍﻟﺨﻠﻴﻔﺘﻴﻦ
ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻱ: ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ
ﻭﻋﺘﺮﺗﻲ ﺍﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ، ﻭﺍﻧﻬﻤﺎ
ﻟﻦ ﻳﻔﺘﺮﻗﺎ ﺣﺘﻰ ﻳﺮﺩﺍ ﻋﻠﻲ
ﺍﻟﺤﻮﺽ ”.
Fassara:
“Hakika ni mai barin
halifofi biyu ne a cikinku
bayana: littafin Allah da
iyalan gidana. Kuma ba
zasu rabu ba har sai sun
zo mini a tafki.
Wadannan su ne
riwayoyin Hadisin.
Wanne ne ya inganta a
cikinsu? Wanne ne bai
inganta ba? Kuma
saboda me? Sa’annan
mene ne Hadisin yake
koyarwa? Ina muka yi
sabani da ‘yan Shi’a a
game da wannan
Hadisi? Sai ku dakace
mu.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s