MARABA DA WATAN RAMADAN ••••••••••••••••••••[01]


MARABA DA WATAN
RAMADAN
.
•••••••••••••••••••••[1]
••••••••••••••••••••
.
KWADAITARWA AKAN
AZUMIN WATAN
RAMADAN !!!
.
Haqiqa shari'ar
musulunci ta qarfafa
kwadaitarwa akan
azumtar watan
Ramadan tare da
bayyana falalarsa da
kuma daukakar
darajarsa.
.
Da ace mai Azumi zai
kasance yana da
zunubai (qanana) kuma
ace yawansu ya cika
sama da qasa to za a
gafarta masa wannan
zunubai don Albarkar
wannan ibada ta Azumi.
.
Saboda haka zamu
taqaita wannan bayani
akan abubuwa guda
uku domin
Kwadaitarwa akan
azumi, kamar haka:
.
• GAFARTA ZUNUBAI:
Manzon ALLAH (SAW)
Yace:"Dukkan wanda ya
azumci watan Ramadan
yana mai imani da
ALLAH kuma yana mai
Neman lada, to an
gafarta masa ayyukan
da ya gabatar na
zunubansa"
.
(Bukhary 4/99, Muslim
Hadith No.759)
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace:" Salloli biyar da
jumma'a zuwa wata
jumma'a da watan
Ramadan zuwa
Ramadan suna kankare
zunuban dake tsakanin
su, matuqar an nisanci
kaba'ira (manyan
zunubai)
.
(Muslim 233)
.
• KAR6AR ADDU'A DA
'YANTARWA DAGA
WUTA:
.
Ana kar6ar addu'ar bayi
a watan Ramadan cikin
ko wani lokaci na watan
Ramadan.
.
Manzon ALLAH (SAW)
Yace:"Lallai Allah (SWT)
yana da bayi abin
'yantawa daga wuta ko
wani yini da dare na
watan Ramadan, kuma
ko wani musulmi da ya
roqi ALLAH yana da
wata addu'a da idan
yayi ana kar6a masa"
.
(Ahmad 2/254)
.
• MAI AZUMI YANA
CIKIN MASU GASKIA DA
SHAHIDAI:
.
Wani Mutum yazo wurin
Manzon ALLAH (SAW)
sai Yace: Ya Manzon
ALLAH shin ko kana
ganin idan na shaida
babu abun bautawa da
gaskia sai ALLAH, kuma
na shaida kai Manzon
ALLAH ne, kuma nayi
salloli biyar na bada
zakkah kuma nayi
azumin watan
Ramadan kuma nayi
tsayuwarsa, cikin wani
Matsayi nake? Sai
Manzon Allah (SAW)
Yace:" cikin masu
gaskiya da shahidai)
.
(Ibn Hibban Hadith No.
19)
.
WAJABCIN AZUMIN
WATAN RAMADAN !!!
.
•ALLAH (SWT) Ya
wajabtawa musulmi
axumin watan
Ramadan kamar yadda
ya wajabtawa
al'ummomin da suka
gabata….
.
(Surah ta 2 aya ta 183)
.
Amma farkon wajabta
azumin watan
Ramadan ya kasance
akan za6i ne tare da
kwadaitarwa akan
yinsa, saboda yin azumi
abu ne mai wahala ga
wadansu sahabbai (RA)
saboda haka sai aka
bada za6in cewa wanda
bazai yi azumi ba to
yayi (Fidya) wato duk
ranar da bazai yi azumi
ba ya cigar da mabuqaci
daya.
.
• ALLAH (SWT) Yace:"
kuma akan wadanda
suke yin sa da wahala
akwai fansar ciyar da
matalauci (miskini),sai
dai wanda ya qara
alheri, to shine nafi
alkhayri agare shi, kuma
kuyi azumi da (wahalar)
shine mafi alkhayri
agareku idan kun
kasance masu sani"
.
(Surah ta 2 aya ta 184)
.
Amma an shafe
wannan sauqin saboda
ayar data zo bayanta,
sahabbai biyu wato
Abdullahi dan Umar da
Salmatu dan Ak'wa'u
(RA) sun bada labarin
cewa ayar data zo
bayan zuwan wannan
aya ta shafeta. Ayar
data shafeta farkon
itace:
.
• Fadar ALLAH (SWT):
"Watan Ramadana ne
wanda aka sauqar da
alqur'ani acikinsa wanda
ya kasance mazaunin
gida daga cikinku acikin
watannan to lallai ya
azumce shi"
.
(Surah ta 2 aya ta 185)
.
• Da fadarsa ALLAH
(SWT):" Yaku wadanda
suka bada gaskiya ga
ALLAH da Manzonsa an
wajabta azumi akanku
kamar yadda aka
wajabta ma wadanda
me gabanninku, Ko zaku
ji tsoron ALLAH?"
.
(Surah ta 2 aya ta 183)
.
Dangane da bayanan da
suka gabata na ayoyi
da hadithan Manzon
ALLAH (SAW) zamu
fahimci lallai azumin
watan Ramadan wajibi
ne akan musulmi maza
da mata baligai sai dai
idan an samu wani uzuri
Wanda shari'a ta yarda
da Barin azumin
dominsa.
.
ALLAH Yasa mu dace
(Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis
(Bintus-sunnah)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s