KUSAKURAN DA SUKA YADU A BAKUNAN MUTANE


NURULHUDA
KUSAKURAN DA SUKA YADU A
BAKUNAN MUTANE 1
Cewa: AN HALICCI DUNIYANE
DOMIN MANZON ALLAH ‏
Wannan kuskure ne ya sabawa
nassin Alqur’ani..
Allah ya halicci duniya tun kafin
ya halicci manxon ‏Allah.. kuma
ya halicci manzon Allah ﷺ da
duniya domin Bautarsa ne kawai.
Allah yace cikin suratul kahfi:
( ﻗُﻞْ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﺃَﻧَﺎ ﺑَﺸَﺮٌ ﻣِّﺜْﻠُﻜُﻢْ ﻳُﻮﺣَﻰٰ ﺇِﻟَﻲَّ ﺃَﻧَّﻤَﺎ
ﺇِﻟَٰﻬُﻜُﻢْ ﺇِﻟَٰﻪٌ ﻭَﺍﺣِﺪٌ ۖ ﻓَﻤَﻦ ﻛَﺎﻥَ ﻳَﺮْﺟُﻮ ﻟِﻘَﺎﺀَ
ﺭَﺑِّﻪِ ﻓَﻠْﻴَﻌْﻤَﻞْ ﻋَﻤَﻠًﺎ ﺻَﺎﻟِﺤًﺎ ﻭَﻟَﺎ ﻳُﺸْﺮِﻙْ
ﺑِﻌِﺒَﺎﺩَﺓِ ﺭَﺑِّﻪِ ﺃَﺣَﺪًﺍ ﺍﻟﻜﻬﻒ )110 ).
“Kace ni ban kasance ba face
mutum kamar ku, ana wahayi
gareni cewa lallai Allahnku Allah
dayane, duk wanda yake burin
haduwa da Ubangijinsa. Toh ya
aikata aiki NA gari. Kuma kada ya
hada bautar ubangijinsa da
kowa “.
Wannan ayar ta nuna mana..
Annabi mutum ne kamar kowa..
Banbancin mu dashi kawai shine
shi Anai masa wahayi.
Abinda yake daidai shine: Allah
ya halicci duniya da abinda ke
cikinta har da annabi Muhammad
(SAW) ba don komi ba sedan su
bauta masa.
Dalili shine fadin Sa madaukakin
sarki.
( ﻭَﻣَﺎ ﺧَﻠَﻘْﺖُ ﺍﻟْﺠِﻦَّ ﻭَﺍﻟْﺈِﻧﺲَ ﺇِﻟَّﺎ ﻟِﻴَﻌْﺒُﺪُﻭﻥِ (
ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ )56 )
“Ban halicci Aljanu da mutane ba
FACE dan su bautamin”.
Ayar taxo da siga mai gamewa..
sannan ayar da muka kawo a
sama ta nuna mana cewa
Manzon Allah dayane daga cikin
mutane, dan haka ya shiga cikin
wadanda Allah yake cewa bai
haliccesu se dan bautansa.
A wani wajen Allah yacewa
manxon Allah ‏
ﻭَﺍﻋْﺒُﺪْ ﺭَﺑَّﻚَ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﺄْﺗِﻴَﻚَ ﺍﻟْﻴَﻘِﻴﻦُ.
Ka bautawa ubangijinka har
lokacin da yaqini
(mutuwa )zatazo maka.
Allah yace:
( ﻭَﻣَﺎ ﺧَﻠَﻘْﻨَﺎ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽَ ﻭَﻣَﺎ
ﺑَﻴْﻨَﻬُﻤَﺎ ﻟَﺎﻋِﺒِﻴﻦَ (
ﺍﻟﺪﺧﺎﻥ )38 )
Kuma bamu halicci sammai da
qassai ba domin wasa… se yace:
( ﻣَﺎ ﺧَﻠَﻘْﻨَﺎﻫُﻤَﺎ ﺇِﻟَّﺎ ﺑِﺎﻟْﺤَﻖِّ ﻭَﻟَٰﻜِﻦَّ ﺃَﻛْﺜَﺮَﻫُﻢْ
ﻟَﺎ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ (
ﺍﻟﺪﺧﺎﻥ ) 39
Bamu haliccesu ba sedan
gaskiya.sedai dayawa daga
cikinsu basu sani ba.
Dan haka Allah ya halicci
duniyace domin gaskiya wanda
itace ake ganin girman Allah da
ikonsa da yadda yake jujjuya Al-
amura. Da rahamarsa.. badan
komai ba sedan agane cewa shi
kadai ya cancanci bauta.
Nassosi akan wannan suna da
yawa
Muna rokon Allah ya shiryi masu
waccar fahimtar. Ya dawo dasu
kan gaskiya, mu kuma ya
tabbatar damu akanta.
Allah yasa mudace .
©SA’AD ALBANY
3/7/2016.

Advertisements

Published by Abubakar Nuhu Yahya Koso

NAME: Abubakar Nuhu Yahya Koso. DATE OF BIRTH: 09-07-1997. SCHOOL: Madarasatul Shababul Islam Koso, Gss Doguwa. IDENTITY: Islam. PURPOSE: Peace. MY LORD: ALLAH. MY ROLE MODEL: Rasulullah. MY GUIDE : Al-Qur'an. MY LIGHT: Hadith. REAL SUBJECT: Tauheed. MY PRACTICE: Sunnah. MY AIM: Jannatul Firdaus. MY MISSION: Da'awatu ilallah MY WEAPON: Du'a. MY LAW: Shari'ah. TOWN & VILLAGE: Koso, Kaduna, Nigeria. NATIONALITY: Nigeria. CONTACT ADRESS: Koso, Kaduna, Nigeria. CONTACT NUMBER: 08025298937, 08023140157. EMAIL ADDRESS: Abbakarnuhks@gmail.com, Ibnnuhks@yahoo.com NICKNAME: IbnNuhAssunnee. ALKUNYA: Abu Abdullah. AQEEDAH: Alkitab was sunnah, Ahlus-sunnah wal jama'ah min Fahmi salafus salih. MY RELIGION ORGANISATIONS: Jama'atu-Izalatil-Bid'ah Wa-Ikamatis-Sunnah MY HOBBIES: Reading & Writing MY FAVOURITE SCHOLARS: 01, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe Hafizahullah 02, Shiekh Imam Abdullahi Bala Lau Hafizahullah 03, Sheikh Dr.Isah Aliyu Ibrahim Pantami Hafizahullah.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: