LAKANI MAI YAWA DAGA FIYAYYEN HALITTA


Wani lakani ne zan bayar
wanda nake fatar in samu
lada mai wanda yayi aiki
da shi shima ya samu
lada. Wanda kuma ya
turawa dan uwansa shima
ya samu lada.
HADISI NA FARKO
Manzon Allah (S.A.W) ya
na cewa Wanda ya
karanta Qulhuwallahu
Ahad kafa 10x Allah ya yi
masa Alkawarin zai gina
masa kata faren gida a
gidan Aljanna sai
Sayidina Umar ya ce Ai to
in haka ne sai mu dinga
yawai tawa sai Manzon
Allah ya ce Allah shine
mai yawaitawa Allah shine
mai tsabtacewa.
HADISI NA BIYU
Manzon Allah ya na cewa
duk wanda ya karanta
suratul Kahfi a ranar
jumaa Allah zai cika masa
hasken sa har zuwa wata
jumaa mai zuwa yana
cikin haske yana cikin
farin ciki.
HADISI NA UKU
Annabi Muhammad (S.A.W)
ya ce duk wanda ya
haddace ayoyin goma na
farkon kahfi Allah zai
kiyayeshi daga fitinar
dujal.
HADISI NA HUDU
Manzon Allah yana cewa
Wanda ya karanta ayatal
kursiyu bayan kowace
Sallah ta farillah ba
abinda zai hana shi shiga
Aljanna sai in bai mutu
ba.
HADISI NA BIYAR
Idan kazo zaka kwanta a
shimfidar ka da daddare
to ka karanta kulya
ayyuhal kafirun to
bazaka mutu mushriki ba
a idan ka mutu a wannan
dare.
HADISI NA SHIDA
Wanda ya yi alwala,
bayan ya kare alwala sai
ya ce Ash-hadu
wahadahu lasharika lahu
wa anna muhammadan
Abduhu wara suluhu.
Allahumma Jaalni
minattauwabina wajaalni
minal mutadhahhirina.
Duk wanda ya fadi
wannan bayan gama
Alwalar sa to zaa bude
masa kofofin Aljanna
guda takwas ya zabi
wadda ya ke son shiga.
HADISI NA BAKWAI
Wanda ya yi alwala
bayan ya kammala
alwalar sa kaf, sai ya ce
Subhanakallahumma
Wabihamdika ash-hadu
allah Ilaha illallah anta
astagfiruka waatubu
ilaika.
Zaa rubuta wannan acikin
wata takarda bazaa bude
ba sai ranar lahira ya ga
alkhairin da ke cikin ta.
HADISI NA TAKWAS
Wani sahabi ya ke cewa
wata rana muna tare da
manzon Allah Sallallahu
Alaihi wasallama sai wani
mutum daga cikin
sahabbai ya ce Allahu
Akbar kabira,
Walhamdulillahi kasira,
Wasubhanallahi bukratan
waasila, Sai manzon Allah
ya ce wanene cikin ku ke
fadar wannan kalma sai
ya ce ni ne Ya rasulullah
sai manzon Allah ya ce
nayi mamakin wadan nan
kalma da ka fada, anbude
rofofin sama gaba daya
saboda wannan kalma da
ka fada. Sai Abdullahi Dan
Umar ya ce tun daga
wannan rana kullum sai
na fadi wannan kalma,
ban taba tsallake wata
rana ko wani lokaci da
bana fadar wannan kalma
ba.
HADISI NA TARA
Wata rana mun kasance
muna Sallah a bayan
manzon Allah (S.A.W) da
Annabi ya dakko daga
rukuu sai ya ce Samiallah
Liman Hamidahu sai wani
mutum daga cikin
sahabbai ya ce Rabbana
Walakal Hamdu, Hamdan
Kasiran Mubarakan Fihi
da aka gama sai Manzon
Allah ya waiwayo sai ya
ce Wanene ya fadi
wannan sai mutum ya ce
Ni ne ya manzon Allah Sai
manzon Allah ya ce Naga
malaika talatin da yan kai
suna rigagato wazai
rubuta wannan aiki yaje
ya gayawa Allah.
HADISI NA GOMA
Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallam ya ce Wanda
ya yi sallar nafila rakaa
goma sha biyu tsakanin
dare da rana Allah zai
gina masa gida a cikin
gidan Aljanna.
HADISI NA SHADAYA
Wanda ya kiyaye yanayin
nafila rakaa hudu kamin
sallar azahar da kuma
rakaa hudu kamin sallar
laasar to Allah zai
haramta masa shiga wuta.
HADISI NA SHA BIYU
Manzon Allah Yana cewa
Allah ya jikan wanda ya
jikan wanda ya yi sallar
nafila rakaa hudu kamin
laasar.
HADISI NA SHA UKU
Wanda yake karanta
ayoyi goma da daddare
to bazaa rubuta shi cikin
gafalallu ba wanda ya ke
karanta ayoyi dari to zaa
rubuta shi cikin masu
bauta ga Allah, wanda
kuma ke karanta ayoyi
dubu a cikin dare kullum
to zaa rubuta shi daga
cikin masu arzikin lahira.
HADISI NA SHA HUDU
Wanda da yi Sallar nafila
a cikin duhu inda
bawanda zai ganshi to
Allah zai linka masa sau
ashirin da biyar na sallar
da zai yi wani ya ganshi.
HADISI NA SHA BIYAR
Annabin tsira ya ce
Wanda yayi sallar walha
(Sallar hantsi/Luha)
rakaa hudu kuma yayi
rakaa hudu kamin sallar
laasar, Allah zai gina
masa a cikin aljanna.
HADISI NA SHA SHIDA
Hakika malaiku suna yin
salati ga wadanda suke
cika sahun farko, idan
suka ga wata kafa a cikin
Sallah suna cikata basa
barin ta kuma Allah zai
cika darajar sa da
kimarsa da martabar sa.
HADISI NA SHA BAKWAI
Babu wani Bawa da zai yi
sujada ga Allah face Allah
ya rubuta masa lada ya
kankare masa zunubi ya
kuma daukaka masa
daraja don haka mu
yawaita sujjada.
HADISI NA SHA TAKWAS
Wanda yayi sallar asuba
a cikin jami sannan ya
zauna yana ta salati
yana ta ambaton Allah bai
bari ba harsai da rana ta
fito, sannan ya tashi yayi
sallar walha rakaa biyu
to Manzon Allah ya ce
Kamar yayi hajji
cikakkiya! Kamar yayi
umura cikakkiya! Kamar
yayi umura cikakkiya!
Kamar yayi umura
cikakkiya! hajji cikakke!
hajji cikakke! hajji
cikakke! Haka Annabi
Muhammad Sallalahu Alaihi
Wasallama ya mai maita.
HADISI NA SHA TARA
Manzon Allah ya ce
wanda ya yi Sallah arbain
a cikin jami maana kwana
takwas jami bai tsere
masa ba, sallolin nan
biyar a jere duk da shi
ake kabarta kabbarar
harama, to Allah zai
rubuta masa kubuta daga
musibu guda biyu na
farko Allah zai rubuta
masa kubuta daga wuta
bazai shiga wuta ba, na
biyu kuma Allah zai
rubuta masa kubuta daga
muna funci bazai mutu
muna fuki ba.
HADISI NA ASHIRIN
Sallar da Allah ya fi so
itace sallar asuba ta
ranar jumaa a cikin jami,
kuma duk wanda ke abin
da Allah ke so to Allah zai
so shi, idan kuma Allah
Ya so shi
HADISI NA ASHIRIN DA
DAYA
Wanda ya ce
Subhanallahil azim
Wabihamdihi, zaa dasa
masa wata bishiya a cikin
gidan Aljanna wadda zai
ginda tsinkar alkhairin ta.
HADISI NA ASHIRIN DA
BIYU
Manzon Allah ya wanda
ya ce, duk wanda ya
karanta
Subhanakallahumma
Wabihamdika Ash-shadu
Allah Ilaha Illah anta
astagfiruka waatubu
ilaika, a wajen jira ko
inda ake shiririta ko
shirme bayan sun gama
kamun su watse ya
karanta wannan zai zame
masa kaffara bisa ga
kura kuran da ya tafka a
wurin.
HADISI NA ASHIRIN DA
UKU
Manzon Allah (S.A.W) ya
ce Hakika fadar
Subhanallahi,
Walhamdulillahi, Walaila
ha Illallahu, Wallahu
Akbar, tana girgijewa
mutum zunubai kamar
yanda bishiya take
girgije ganyen da yake
zubuwa a kasa. Don haka
mai makon mutum ya
zauna yana hira to ya yi
ta fadar wannan don
Allah ya girgije masa
zunubain sa.
HADISI NA ASHIRIN DA
HUDU
Manzon Allah (S.A.W) ya
ce idan dayan ku ya
gajiye bazai iya tarawa
kansa lada dubu ba to
yayi Subhanallahi sau
dari sai a rubuta masa
lada dubu ko a kankare
masa laifuffuka guda
dubu.
HADISI NA ASHIRIN DA
BIYAR
Manzon Allah (S.A.W) ya
ce hakika Allah ya zabi
wasu kalmomi uku wanda
ya nace musu to zai samu
alkhairin duniya da lahira
sune (Subhanallah,
Walhamdulillah, Wallahu
Akbar. Wanda ya ce
Subhanallah zaa bashi
lada 20 a kankare masa
zunubi 20 Wanda ya ce
Alhamdulillah zaa bashi
lada 30 a kankare masa
zunubi 30 wanda Allahu
Akbar zaa bashi lada 20
a kankare masa zunubi
20.
HADISI NA ASHIRIN DA
SHIDA
Manzon Allah (S.A.W) ya
ce Bana gaya maka wani
abu wanda ya fi haka
alkhairi? Kace
Subhanallah,
Walhamdulillah, Walailaha
Illallah, Wallahu Akbar,
zaa dasa maka bishiya a
cikin gidan Aljanna da
kowace kalma da ka fada.
HADISI NA ASHIRIN DA
BAKWAI
Manzon Allah (S.A.W) ya
ce Wanda ya yi ruwa da
kudi bai ba dasu sadaka
ba kuma ya yi rowa da
dare bai tashi yayi
tsayuwar dare ba, to ya
lazimci wannan kalma sai
ta tsaya masa a matsayin
sadakar da bai yi ba da
tsayuwar dare da ya
kasa bai yi ba
Subhanallahi Wabihamdihi
ya yi ta fadar wannan sai
ya zamu a bakacen kudin
da bai bayar ba a
bakacen daren da bai yi
tsayuwa a cikin sa ba.
HADISI NA ASHIRIN DA
BAKWAI
Manzon Allah ya ce
wanda zai shiga kasuwa
sai ya ce Lailaha illallahu
wahdahu lasharikalahu,
Lahul mulku, walahul
Hamdu, Yuhyi wayumitu,
wahuwa hayyulla ya mutu
biyadihil khairu wahuwa
ala kullhi shaiin kadir.
Allah zai rubuta masa
lada million daya ya goge
masa zunubi million daya
zaa daukaka darajar sa
million daya sannan zaa
gina masa gida a cikin
gidan Aljanna.
HADISI NA ASHIRIN DA
TAKWAS
Manzon Allah ya ce bana
gaya maka abin da ya fi
ambaton Allah ka da
daddare da rana ba?, to
kace Alhamdulillahi
Adadama khalaka,
Alhamdulillahi mila ma
khalaka, Alhamdulillahi
adada mafissamawati
wama filardhi
Alhamdulillahi adada ma
aksa kitabuk,
Walhamdulillahi ala ma
akhsa kitabuk,
Walhamdulillahi adada
kulli shaiin,
Walhamdulillahi minha kulli
shaiin, kuma ka ce
Subhanallahi Adada ma
halaka, Subhanallahi mila
ma halaka, Adada
mafissamawati Wama
filardi, Subhanallahi ala
ma ahsa kitabuk,
Subhanallahi adada kulli
shaiin, Subhanallahi
minha kullhi shaiin,
Subhanallahi wanda ya
fadi wannan wato yafi
kowane irin ambaton Allah
da zakayi fadin duniyar
nan Inji Manzon Allah.
HADISI NA ASHIRIN DA
TARA
Manzon Allah (S.A.W) ya
ce wanda ya min salati
kafa 10 lokacin da ya
wayi gari, ya yimin salati
kafa 10 lokacin da ya
yammatu, cetona zai
riskeshi ranar Alkiyama.
HADISI NA TALATIN
Manzon Allah Salallahu
Alaihi Wasallam Ya ce
wanda ya ce radhitu
billahi rabban Wabil
Islamidinan Wabi
Muhammadin Nabiyan,
aljanna ta tabbata a
gareshi, ba wai zata
tabbata ba tariga ta
tabbatar masa don haka
muyi ta fadar wannan
kalma don Aljanna ta
tabbata a garemu.
HADISI NA TALATIN DA
DAYA
Mazon tsira ya na cewa
wanda ya yiwa dan
Uwansa kyakkyawar
Adua batare da dan Uwan
nasa ya sani ba Ya ce
Allah ga dan Uwana wane
yana da bukata iri kaza
ka biya masa, ko yana
cikin balai ka yaye masa
ko yana cikin wata fitina
ko damuwa ka dauke
masa, ba tare da shi
wancan dan uwan yasan
kayi masa adua ba koma
baka gaya masa ba.
Malaika ya na nan kusa
da kai sai ya ce amin
walaka, kai ma Allah ya
baka irin kwatan kwacin
abin da ka roka wa dan
uwanka. Kunga jamaa mu
rinka rokawa yan uwan
mu adua mai kyau saboda
muma malaiku suyi mana
adua mai kyau.
HADISI NA TALATIN DA
BIYU
Manzon Allah ya ce
wanda ya kare mutun cin
dan uwansa baya nan
(maana ana kokarin
tuzarta dan uwanka baya
nan sai kayi kakagida ka
kare masa mutuncin sa)
to ya zama hakke ne ga
Allah ya yanta ka daga
wuta.
HADISI NA TALATIN DA
UKU
Annabi Muhammad Sallahu
Alaihi Wasallam ya ce
wanda ya dauke abunda
zai cutar da mutane a
kan hanya to hakika Allah
zai rubuta masa
cikacciyar lada, wanda
kuma Allah ya rubutawa
cikakkiyar lada Allah zai
shigar dashi a Aljanna.
ALLAH YA TAIMAKE MU
Masoyin ku
Mai neman Rahamar
Ubangiji
#Viawhatsapp

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s