Sunayen Ahalus Sunna A Wajen ‘Yan Shi’a – Matsayin Musulmi a wajen ‘Yan Shi’a Dr. Umar Labdo


Babi Na daya
Ma’anar Ahalus Sunna A
Wajen Rafilawa
Mai karatun littafan Shi’a
zai lura da wasu sunaye,
ko kuma laqabai, da suke
kiran Ahalus Sunna da su.
Wadannan lakabai suna
cikin littafan malamansu
na farko da malamansu na
zamani. Ba safai sukan kira
su da sunan Ahalus Sunna
ba sai nadiran. Sunayen
dukkaninsu suna nuna
kazafi da vatanci da
wulakanci. Zai yi kyau mu
fara bayani da wadannan
sunaye kafin mu shiga
magana a kan ma’anar
Ahalus Sunna a wajen
Rafilawa.
Sunayen Ahalus Sunna A
Wajen ‘Yan Shi’a
Akwai sunaye guda uku da
Rafilawa suke amfani da
su don ambaton Ahalus
Sunna a cikin littafansu da
maganganunsu wadanda
suka hada da
hudubobinsu da laccocinsu
da wa’azozinsu.
Wadannan su ne:
1. Nasibawa. Asalin sunan
da Larabci nasib, jam’insa
nawasib, watau mai kulla
gaba, ko wanda ya kafa
kiyayya. Abinda suke nufi
gaba da kiyayya ga Ahalul
Baiti, musamman Ali binu
Abi Dalib da Fadima, Allah
ya kara musu yarda, da
kuma imamai goma sha
biyu daga zuri’arsu.
Wannan suna shi ne mafi
muni kuma mafi yaduwa a
tsakaninsu wanda suke
ambaton Ahalus Sunna da
shi.
Malaminsu mai suna
Hussain Aali Usfur
Addarazi Albahrani, yana
cewa, “Al’ada ta gudana,
kai har ma da hadisan
imamai, a kan cewa nasibi
shi ne wanda a wajensu
suke kira Sunni.”[1]
A wajensu, yana nufin a
wajen Ahalus Sunna.
Amma su a nasu wajen
nasibawa suke ce da su.
Dubi yadda ya yi nuni ga
Ahalus Sunna da lamirin
“su” domin ya bambance
su da “mu” wanda a
zancensa yake nufin ‘yan
Shi’a. Wannan kawai ya isa
ya nunawa mai karatu
yadda dan Shi’a yake
daukar kansa da Ahalus
Sunna; watau abin mu ne
da su.
Malamin Shi’a na wannan
zamani wanda ya shahara
da tsaurin kai, Muhammad
Tijjani Samawi, yana cewa,
“Abu ne da ba ya bukatar
a fadi cewa mazhabin
nasibawa shi ne mazhabin
Ahalus Sunna wal
Jama’a.”[2] Haka yake
kamar yadda malamin ya
fadi. Wannan abu ba ya
bukatar a fadi saboda ya
shahara a tsakanin
Rafilawa kuma a cikinsu
babu mai ja a kai.
2. Amawa. Wannan shi ne
suna na biyu da Rafilawa
ke kiran Ahalus Sunna da
shi. Asalinsa da Larabci
aami, jam’insa awaam,
watau gama-gari, ko
tarkacen mutane. Kuma
sunan kishiyar lafazin
khaas ne (jam’insa
khawaas), wanda yake
nufin na musamman, ko
na-gari. Watau ‘yan Shi’a
su ne na musamman,
masu nagarta, Ahalus
Sunna kuwa tarkace,
gama-gari. Daga cikin
malaman Shi’a da suka yi
amfani da wannan suna
akwai Alhurrul Amili
wanda ya rubuta wani
babi mai taken “Babin
Hani Ga Barin Riko Da
Abinda Ya Dace Da
Amawa” a cikin littafinsa
mai suna Alfusulul
Muhimma. A qarqashin
wannan babin, ya ruwaito
imaminsu na shida, Ja’afar
Sadik, yana cewa idan aka
samu hadisai guda biyu
masu karo da juna, to a
dauki wanda ya saba wa
ra’ayin Amawa, a kyale
wanda ya dace da su.[3]
3. Suna na uku shi ne
Jumhur. Wannan suna
haka yake ko a Larabci,
kuma ba shi da tilo sai
jam’i kawai. Ma’anarsa ta
yi kama da gama-gari
koda yake a wani yayi
yana nufin agalabiya,
watau mafiya yawa, masu
rinjaye, ko kuma majorati,
kamar yadda ake fadi da
kalmar Turanci ta aro.[4]
Wadannan sunaye su ne
‘yan Shi’a suke amfani da
su wajen ambaton Ahalus
Sunna a cikin littafansu,
maganganunsu, laccocinsu
da hudubobinsu. Kuma
ma’anarsu a fili take; suna
nuna yadda ‘yan Shi’a suka
dauki masu bin tafarkin
Sunna a matsayin abokan
gaba masu kiyayya ga
imamai, bare waxanda ba
na gida ba, kuma koma-
baya wadanda suke
gama-gari ne su, tarkace.
Banda wadannan sunaye,
akwai wasu lafuza da
malaman Shi’a ke amfani
da su domin nuni ga duk
wani Musulmi wanda ba
ya bin tafarkinsu, wanda
yana iya hadawa da
Ahalus Sunna da wasunsu.
Waxannan sun haxa da
almukhalif, watau mai
saba mana, da gairuna,
watau waninmu, da
munafiq, watau munafiki,
da sauransu.
Ma’anar Ahalus Sunna A
Wajen ‘Yan Shi’a
Amma idan muka koma
ga haqiqanin ma’anar
Ahalus Sunna a wajen ‘yan
Shi’a, to sai mu ga cewa
sun gina ta a kan
abubuwa uku.
1. Abu na farko: Fifita
wanin Ali binu Abi Dalib
(RA) a kansa. Dangane da
wannan ma’ana ne
malaminsu dan hayaki,
Ni’imatullahi Aljaza’iri,
yake fadin wai, “An
ruwaito daga Annabi(SAW)
cewa alamar nasibawa ita
ce gabatar da wanin Ali a
kansa.”[5] Watau wanda
ya ce wani Sahabi ya fi Ali,
ko yana gaba da shi a
wajen daraja da falala, ko
shi ne Khalifa na farko ba
Ali ba, to wannan ya zama
nasibi. Babu shakka Ahalus
Sunna suna ganin cewa
Abubakar da Umar da
Usman suna gaba da Ali a
wajen falala da fifiko da
kuma jerin khalifanci.[6]
Kai a cikin kungiyoyin
Musulunci ma kaf, ba mai
fifita Ali a kan Abubakar da
Umar sai ‘yan Shi’a (koda
yake an samu wasu
wadanda suka fifita shi a
kan Usman). Saboda haka
a kan wannan, duk wanda
ba dan Shi’a ba nasibi ne
ke nan.
2. Abu na biyu: Yarda da
amincewa da khalifancin
Abubakar da Umar, Allah
ya kara musu yarda.[7]
Watau ko da mutum bai
fifita su ba, idan dai ya
yarda da cewa su khalifofi
ne, to ya zama nasibi.
3. Abu na uku: Jibintar
Jibtu da Dagutu, kamar
yadda suke fadi.[8] Abinda
suke nufi da Jibtu da
Dagutu su ne Abubakar da
Umar, Allah ya kara musu
yarda. Watau ba fifita su
ba, ba yarda da
khalifancinsu ba, ko
jibintar su ma kawai,
watau son su da daukar su
a matsayin ‘yan uwa
Musulmi, yana mai da
mutum nasibi.
Yana daga cikin akidun
Rafilawa sanannu cewa
mutum ba ya zama
Musulmi sai ya barranta
daga Abubakar da Umar
da manyan Sahabbai tare
da su, kuma ya barranta
daga duk mai son su, ko
jibintar su. Babban
malaminsu, Muhammad
Bakir Almajalisi, ya
tabbatar da wannan aqida
tasu inda yake cewa,
“Akidarmu ta barranta ita
ce cewa mu muna
barranta daga gumaka
hubu: Abubakar da Umar
da Usmanu da Mu’awiya;
da mataye hudu: A’isha da
Hafsa da Hindu da Ummul
Hakam; kuma muna
barranta daga dukkan
mabiyansu da magoya
bayansu; kuma muna
kudure cewa su ne mafiya
sharrin halittar Allah a
bayan qasa; kuma cewa
imani da Allah da
Manzonsa da imamai ba
ya inganta sai an barranta
daga makiyansu.”[9]
Daga wadannan bayanai
da suka gabata zai
bayyana a fili cewa a
ganin ‘yan Shi’a duk
wanda bai kudure
aqidarsu ba ta cewa Ali
binu Abi Dalib shi da
‘ya’yansa su kadai su ne
khalifofi, ko imamai, kuma
cewa Abubakar da Umar
da Usmanu ba wai kawai
su ba khalifofi ba ne a’a su
kafirai ne gumaka, wanda
duk bai kudure wannan
akida ba to shi ne nasibi
kuma imaninsa da Allah
da Manzo bai inganta ba.
Wannan yana nufi, a
takaice, duk wanda ba dan
Shi’a ba kafiri ne, tun daga
kan Abubakar(RA) har ya
zuwa ga kai mai karatun
wannan littafin, in kai ba
dan Shi’a ba ne.
To jama’a, ina karyar
hadin kai? Ina karyar
takrib da ta’aruf da “Islam
One”? Ina da’awar cewa
Musulmi duka daya ne?
Yaya masu barranta daga
Abubakar da Umar da
Usmanu da A’isha da Hafsa
da mabiyansu da magoya
bayansu za su hada kai da
wani? Shin ana hada kai
da kafiri wanda yake
goyon bayan mafiya
sharrin halittar Allah a
bayan qasa?
Amma ba a nan batun ya
kare ba. Saurari hukuncin
nasibawa waxanda suka
yarda da khalifancin
Abubakar da Umar, suka
fifita su a kan Ali.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s