WASIKAR MALLAM NASIR EL-RUFA’I (MEMO) ZUWA GA SHUGABA BUHARI A MAHANGAR ADALCI


Daga
Imam Murtadha Muhammad
Gusau
Lahadi, Maris 19, 2017
Bismillahir Rahmanir Rahim
Allah Ta’ala yace:
“Ya ku wadanda suka yi imani!
Ku kasance masu tsayuwa da
adalci, kuna masu shaida saboda
Allah, kuma ko da a kanku ne ko
iyayen ku da ‘yan uwanku
makusanta, ko ya kasance
mawadaci ko talaka, Allah ne
mafi cancanta da al’amarinsu,
kada ku bi son zuciya, har ku
karkata (ga rashin adalci). Kuma
idan kuka karkatar da magana
(saboda son zuciya), ko kuka kau
da kai (daga gaskiya), to, lallai
Allah ya kasance masani ga abin
da kuke aikatawa.” (Surah Nisa’,
4:135)
Kuma Allah Madaukaki yace:
“Ya ku wadanda suka yi imani!
Ku kasance masu tsayuwa domin
Allah, masu shaida da adalci.
Kuma kada kiyayya da wasu
mutane ta hana ku kuyi masu
adaci. Kuyi adalci. Shine mafi kusa
ga tsoron Allah. Kuma ku bi Allah
da takawa. Lallai Allah masani ne
ga abin da kuke
aikatawa.” (Surah Ma’idah, 5:8)
Allah ya jikan Mallam Sa’adu
Zungur yana cewa: “In zaka fadi,
fadi gaskiya, Ko me taka ja maka
ka biya!”
Ya ku ‘yan uwana masu girma!
Lallai wadannan ayoyin Alkur’ani
mai girma suna karantar da mu
umurnin Allah na yin adalci ga ko
wane mutum. Kar ka yarda
sabanin akida, ko sabanin addini,
ko sabanin yare ko harshe, ko
sabanin gari, jiha ko yanki, ko
sabanin launin fata, ko sabanin
siyasa, kai ko wane irin
banbance-banbance su hana ka
tsaida adalci ga wani mutum ko
wasu mutane. Duk yanda kuke
da sabani, yi kokari kaga cewa ka
yiwa kowa adalci. Yin hakan
shine za ya sa ka kubuta daga
afkawa cikin fushin Allah da
azabar sa.
Ya ku masoyan gaskiya da adalci!
Alal hakika Allah (SWT) ya
shar’anta muna yin nasiha, kuma
Annabi (SAW) ya ba ta
muhimmanci babba, har ya kai
ga fassara Addini da Nasiha,
saboda yadda nasihar take
daukar dukkan bangarori na
Addinin.
An karbo daga Tamim Bin Aus Al-
Dari, yace, Annabi (SAW) yace:
“ADDINI NASIHA NE.” SAI MUKA CE
GA WA? SAI YACE: “GA ALLAH, DA
LITTAFINSA, DA MANZONSA DA
SHUGABANNIN MUSULMAI, DA
GAMA GARINSU (TALAKAWA).”
Kuma Annabi (SAW) yace:
“WANDA YA GA MUMMUNAN ABU
DAGA CIKIN KU TO YA CANZA SHI
DA HANUN SA, IDAN BA ZAI IYA BA
TO YA CANZA SHI DA BAKIN SA,
IDAN BA ZAI IYA BA TO YA KI
ABUN A ZUCIYAR SA…”
Wadannan hadisai sun nuna
muna wajabcin yin nasiha ga
kowa da kowa, ko meye
matsayinsa, kai har da shugaba.
Kuma kalmar shugaba kalma ce
mai fadi, domin ta hada kowane
irin shugaba. Shugabannin
Addini ne, Shugabannin siyasa
ne, Shugabanni masu sarauta ne,
kai ko wadanne irin shugabanni.
Wajibi ne idan har an gano
kuskure a tattare dasu, ayi masu
nasiha.
Babu wani shugaba da aka ware
aka ce ban da shi a wurin yin
nasiha. Dole ne ayi ma shugaba
nasiha ko wanne irin matsayi
yake dashi a cikin al’ummah. A
Musulunci, babu wanda yafi
karfin doka, haka babu wanda
zai ce shi ya wadatu da nasiha ko
baya bukatar nasiha, matukar
alkhairi ne manufarsa. Kuma idan
shugaba ya karbi nasihar da
akayi masa, to zai amfana kuma
jama’ar da yake shugabanta su
amfana. Amma idan an yi masa
nasiha sai yayi fushi, kuma ya
dauki wanda yayi masa nasiha a
matsayin makiyi, saboda wasu
‘yan kanzagi da suka zuga shi, to
wannan shugaba zai cutu kuma
ya cutar da wadanda yake
shugaban ta.
Ya ku bayin Allah! Lallai duk
wanda yake bin abin da ke kai
kawo a sha’anin kasar nan tamu
mai albarka, Nigeria, yana sane
da labarin dake yawo a wurin
‘yan jaridu, kafafen yada labarai,
da sauran jama’a na wata wasika
da ta bulla satin da ya wuce, mai
take kamar haka: “IMMEDIATE
AND MEDIUM TERM IMPERATIVES
FOR PRESIDENT MUHAMMADU
BUHARI”, wasikar da take dauke
da shafuka talatin (30), wadda
Gwamnan Jahar Kaduna Mallam
Nasir Ahmad El-Rufa’i ya rubuta
wa Shugaba Muhammadu Buhari
yana mai bashi shawara da yi
masa nasiha a kan lallai ya gyara
sha’anin tafiyar da Mulkin sa,
kasancewar halin da ake ciki a
Nigeria da yanda ya hango
abubuwa suna gudana a cikin
gwamnati.
Ya ku jama’ah! Da farko, abunda
ya kamata ku fahimta shine,
wannan wasika ba fa a satin da
ya gabata aka rubuta ta ba, ko
watan da ya wuce, a’a. Wannan
wasika fa an rubuta ta ne tun
ranar September 22, 2016, wato
shekara daya da ta gabata, bayan
da farko gwamnan ya rubuta
wasu shawarwari da za su
taimaka wa shugaba Buhari
wajen gudanar da mulkin sa, a
shekarar 2015 bayan anci
nasarar zabe, kafin ya shiga
office. A cikin wasikar, Mallam
Nasir El-Rufa’i yake cewa: “A
matsayina na yaron ka, mai yi
maka da’a da biyayya, masoyinka
mai kaunar ka, mai fatan alkhairi
zuwa ga reka, mai son ci gaban
ka, ina fatan wannan nasiha za ta
taimaka. Amma idan ta bata
maka rai, ina rokon don Allah
kayi hakuri, ka yafe ni. Wajibi ne
in fada maka gaskiya, kuma ni
bani da wata manufa face ci
gaban jam’iyyar mu, ci gaban ka
a matsayin ka na shugaban kasar
mu, ci gaban gwamnatin mu da
ci gaban kasar mu.”
In dai fayyace maku, El-Rufa’i yayi
bayani dalla-dalla, cikakke na
inda ya hango matsaloli a cikin
gwamnatin Shugaba Buhari,
kuma yayi kira da a gyara domin
ci gaban kasar mu Nigeria.
A wannan wasika da ni na
karanta ta daga farko har
karshen ta, tsakani da Allah babu
inda Nasir El-Eufa’i ya soki Buhari
ko ya zage shi ko yaci mutuncin
sa. Kawai dai ya bashi
shawarwari ne game da sha’anin
kasa, da inda yake ganin akwai
kura-kuran da sune ummul
haba’isun da suke kawo tarnaki
wajen samar da canjin da aka
yiwa ‘yan Nigeria alkawarin
samarwa, da hanyoyin da za’a bi
domin magance su.
Bullar wannan wasika ke da
wuya, kawai sai wasu mutane da
suke ganin wai su masoya
Shugaba Buhari ne, Wadanda ba
gaskiya da adalci ne a gabansu
ba, suka yi caa a kan Gwamna El-
Rufa’i. Suka ce da wa aka hada
mu ba da shi ba? Mai zagi nayi,
mai batanci da cin mutunci nayi,
mai kage da karya da kazafi nayi.
Alhali wadannan mutane sun
manta, Shugaba Buharin da a da
can yasha alwashi kuma ya yanke
shawarar ba zai sake tsaya wa
takara ba, amma su El-Rufa’i suka
yi ruwa suka yi tsaki har suka
shawo kan sa ya amince ya tsaya
takara, kuma suka taimaka a
wurin kamfen matuka, takarar da
a wannan karon Allah yasa a kayi
nasara.
Wadannan mutane da suka yi caa
a kan El-Rufa’i, suna son su nuna
muna cewa Nasir El-Rafa’i baya
kaunar Shugaba Buhari, ko
Shugaba Buhari baya laifi, baya
kuskure ko duk abunda yayi dai-
dai ne, ko su kai shi matsayin
Allah, ko matsayin Annabta. Suna
son su nuna muna shi ma’asumi
ne, shiyasa suke yi masa irin
wannan makauniyar soyayyar da
za ta cutar da imanin su, tauhidin
su, akidar su da Musuluncin su.
Yanzu wadannan mutane suna
nufin sun fi El-Rufa’i son Shugaba
Buhari ne ko yaya? Suna nufin
Shugaba Buhari yafi karfin a
bashi shawara? Ko yafi karfin ayi
masa nasiha? Suna nufin su ce
muna soyayya ce da kauna ga
Shugaba Buhari irin wadda idan
yayi kuskure ayi shiru kar ayi
masa nasiha? Wadanne irin
mutane ne wadannan da suke
neman su halakar da shugaba da
sunan soyayya? Wallahi duk
Shugaban da ya rasa masu yi
masa nasiha da masu bashi
shawara ta gari, kuna ganin bai
yi hasara ba? Ta yaya Shugaba
zai ci nasara idan ba’a bashi
shawara kuma ba’a yi masa
nasiha?
Wasikar nan ma fa wasu miyagu
ne da basa kaunar zaman lafiya
da ci gaba suka kulla makircin
sakin ta a cikin jama’a don su
hada fitina da fada tsakanin
Shugaba Buhari da Gwamna El-
Rafa’i, ba don komai ba sai don
su cimma wata mummunar
manufa tasu ta son zuciya! Idan
ba haka ba, ta yaya wasikar da
aka yi tun wani lokaci, kuma
akayi ta a asirce, ace sai yanzu
kwatsam kawai wasu su bullo da
ita!
Ya ku ‘yan uwa! Wallahi ku sani
Shugaba​ Buhari mutum ne
kamar kowa. Yana yin dai-dai
yana yin kuskure. Inda yayi dai-
dai mu karfafe shi, muyi masa
Addu’a da fatan alkhairi. Inda
yayi kuskure kuwa, sai muyi
masa nasiha, mu bashi shawara
muyi masa Addu’ar Allah yasa ya
gyara.
Ba ma yiwa Shugaba Buhari
makauniyar soyayya ko
makauniyar biyayya. Ba mu
dauke shi marar laifi ko marar
kuskure ba. Dukkan Dan Adam
mai kuskure ne. Annabawan
Allah da Manzanni kadai ne
katangaggu daga zunubi, su
kadai ne ma’asumai. Amma duk
wanda basu ba, to ko waye shi
zai iya yin kukure.
Kuma mu sani, wallahi yiwa
shugabanni nasiha wajibi ne
kuma dole ne. Su kuma
shugabannin idan anyi masu
nasiha an basu shawara ta gari,
dole su dauka indai har da gaske
suke yi. Domin dukkan mu da su,
Allah zai tambaye mu.
Gwamna Nasir El-Rufa’i ba wai ya
rubuta wa Shugaba Buhari
wasika bane, ko ya bashi
shawara don neman wani
matsayi ba, kamar yadda wasu
shedanu suke fada. A’a, yayi
nasiha ne don a gyara. Kuma ya
sauke nauyin da ke kan sa har ga
Allah. Mu kuma Addu’ar mu har
kullun, shine, Allah ya ba Shugaba
Buhari ikon gyara wa, amin.
Ya ku Jama’a! Ba zai yiwu ba ace
duk lokacin da aka bai wa
Shugaba Buhari shawara ko aka
yi masa nasiha, kawai sai abu ya
zama bala’i. Wannan ya taba
faruwa har ma da mai dakin
Shugaban kasa, wato Hajiya
Aisha Buhari. Kawai don ta fadi
abun da ta hango zai kawo
matsala don a gyara, sai wasu
shedanu suka yi caa a kanta suna
zagi. Kuna nufin kun fi ta son
mijinta? Kun fi ta son cin nasarar
sa? Kawai don ta hango abunda
zai cutar da mulkin maigidanta
tayi magana sai abu ya zama
bala”i? Kar fa da sunan soyayya
mu kai wannan dattijo mu baro!
Wallahi ina ji muna tsoron mu
wuce gona da iri wajen soyayyar
wani, har a wayi gari mun wuce
ka’ida, ya zamanto muna yiwa
wani mutum irin soyayyar da ko
Allah da Manzonsa ba mu yiwa
ita! Don haka wallahi muyi
hankali, muji tsoron Allah a cikin
dukkanin al’amurran mu!
Dukkan wani mutum da yake mai
son ci gaba, mai kaunar Shugaba
Buhari da gaske, adili, kuma yake
kaunar adalci, wallahi dole ya
yaba wa Gwamna Nasir El-Rufa’i
a kan wannan jarunta tasa ta
yiwa Shugaban kasa nasiha. Da
yaso da sai ya zama dan amshin
shata, ya zama ba yada aiki sai
yiwa Shugaban kasa fadanci da
banbadanci, kamar yadda wasu
suka zabi yin hakan.
Sannan daga karshe, ina kira ga
Shugaba Buhari da yaji tsoron
Allah, na san zai ga wannan sako
nawa, kar ya dauki Nasir El-Rufa’i
a matsayin makiyinsa, wallahi
babban masoyinsa ne, mai
kaunar sa da gaske. Domin
mutum ba ya da masoyin da ya
kai ga wanda zai fada masa
gaskiya. Duk wanda zai zo gaban
Shugaban kasa yana fadanci, yaki
gaya masa gaskiya, wallahi ba
masoyinsa ba ne, munafuki ne.
Allah ya taimaki shugabannin mu
baki daya, ya hada kawunan su,
amin.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwanku:
Imam Murtadha Muhammad
Gusau, daga Okene Jahar Kogi,
Nigeria. Za’a iya samun sa a
wannan number:
+2348038289761.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s