Gamewar Da’awar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi wallafar Dr. Abdullahi Getso.


Takaitaccen Bayanin Abinda littafin ya
kunsa Wannan littafi ya kunshi takaitaccen
bayani a game da tarihin rayuwar
mashahurin malamin nan, kuma
mujaddadi, wato Shaikh Abubakar
Mahmud Gumi. Bayan nan ya kunshi irin bangarorin da
ya yi da’awarsa zuwa gare su, da kuma
gwagwarmayarsa da fadi tashinsa wajen
yada akida sahihiya da kuma ceto
al’umma masu tarin yawa a kasar nan,
bayan da sun riga sun gurbata addininsu da al’adu da kuma bidi’o’i, bayan da’awa
ta mujaddadi Shehu Usman dan Fodiyo
Allah Ya yi masa rahama. Daga karshe, wannan littafi ya yi bayanai
game da irin salon da’awar malam, da
kuma inda ta sa gaba, musamman ma
yadda da’awar ta shafi kowane jinsi na
mutane, ba tare da kebance ta ga wani
bangare guda ba, sannan kuma littafin ya karkare da bayanin irin yadda da’awar ta
samu karbuwa, da kuma irin tasirin da ta
yi ga al’ummar wannan kasa, mazansu
da matansu. Gabatarwa Dukkan godiya ta tabbata ga Allah
Madaukaki, muna gode masa, muna
neman taimakonsa da gafararsa, kuma
muna neman tsari daga gareshi game da
sharrin kawunanmu da kuma munanan
ayyukanmu, duk wanda Allah Ya shiryar babu mai batar da shi, duk kuma wanda
ya batar, to babu mai shiryar da shi. Ina
shaidawa babu abin bautawa a bisa
cancanta sai Allah, shi kadai, ba shi da
abokin tarayya, kuma ina shaidawa
Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne, Allah Ya kara tsira da aminci ga
Annabi Muhammad, da alayansa, da
sahabbansa, da kuma duk wadanda suka
bi tafarkinsu har zuwa ranar sakamako. Bayan haka, wannan dan bincike da na yi
akan “Gamewar Da’awar Sheikh
Abubakar Mahmud Gumi ga dukkan
sassan rayuwa” na rubuta shi ne a
sakamakon amsa bukatar majalisar
daliban arewacin Nigeria masu karatu a mataki na koli a jami’ar Musulunci ta
Madina. Ina ganin ban cancanta in yi wannan
bincike wanda ya shafi babban malami
irin wannan ba, musamman ma saboda
raunina da kuma karancin lokaci, amma
duk da haka na amince na amsa
bukatarsu, saboda na karfafi himmarsu da kwazonsu na fito da ayyuka na irin
wadannan malamai nagari, don irin mu
‘yan baya mu yi koyi da su. Su dai malamai kamar yadda Manzon
Allah (SAW) ya fada magada Annabawa
ne, don haka girmamasu da koyi da
manhajinsu ya zama wajibi ga dukkan
musulmi nagari, da ma dukkan mai son
ya kama tafarkinsu na da’awah. Babban abin la’akari a nan shi ne, ita dai
da’awar magabata nagari wacce malam
yayi koyi da ita, kuma shi ma ya zama
abin koyi ga ‘yan baya, shi ne, ilimi da aiki
da shi, rabuwar abubuwan nan guda biyu
ga mai son ya yi da’awah (wato kiran mutane su yi daidai) ba karamar illa ba
ce, inda za a sami mai da’awa ba ilimi, ko
kuma mai da’awah da ilimi amma ba aiki
da shi. Shi dai wannan tafarki na da’awar malam
wanda zamu yi magana a kai, tafarki ne
na da’awah wanda ya shafi dukkan sassa
na rayuwar dan adam : akidarsa,
ibadarsa, mu’amalarsa, zamantakewarsa,
siyasarsa, tattalin arzikinsa, da sauransu. Haka kuma shi wannan tafarki na
da’awah bai bar wani jinsi na mutane ba
face ya taba shi, abin nufi anan shi ne,
da’awar ta shafi masu mulki da masu
kudi, sarakuna, da talakawa, musulmai
da kafirai, ‘yan bidi’a da ahlus-sunnah da makamantansu. To irin wannan da’awah mai cike da
himma da tsoron Allah ita ce wacce
Annabawa suka gadar wa malamai
magabata, sannan su kuma suka gadar
wa da duk wani malami nagari a
zamaninsa, sabanin a yau yadda ta kasance a mafi yawanci malamai
wadanda za a ga suna da’awah ne a
wani bangare guda, ban da sauran
bangarorin, ko kuma ga wani jinsi guda
na mutane ban da sauran, a sakamakon
son zuciya, ko kuma rashin cikakkiyar fahimtar da’awar magabata. {okarin wadannan dalibai na zakulo
manhaji na da’awa ta wannan babban
mujahidi, wanda kusan a iya cewa
mujaddadi ne shi a lokacinsa, wato
Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, yana da
matukar amfani wajen a yada shi ga dalibai masu sha’awar da’awah nan
gaba, domin su yi koyi da shi. Amma kasancewar abu ne na tarihi ina
fata ‘yan uwana dalibai zasu yi man uzuri
saboda raunina na karancin ilimi da
rashin lokaci a bisa duk wani kuskure da
ya bayyana a gare su daga gareni, kuma
su sanar da ni domin in gyara a bugu na gaba. Daga karshe, ina rokon Allah Ya sa
wannan aiki da na gabatar ya zama don
shi, ya yi mana kyakkyawan sakamako da
ni da duk wadanda suka ka taimaka aka
buga shi ko suka karanta suka amfana da
shi. Godiya Ina mika godiyata ga daliban da suka
zama sababin rubuta wannan littafi
wanda asalinsa takarda ce da aka
gabatar a taron kara wa juna ilimi. Ina
rokon Allah (SWT) Ya saka masu da
alheri. Hakanan ina mika godiya ta musamman ga dan uwa Muhammad Sani
tsarkaka da ya taya ni rubuta wannan
littafi duk da uzurorinsa, tare da wanda
yayi ta dawainiya wajen bugawa malam
Rabi’u Umar Rijiyar lemo da dan uwa
malam Usman Abdullahi Deba, Allah (SWT) Ya saka masu da alheri. Har wa
yau ina mika godiya ta musamman ga
Iyalan Sheikh Abubakar mahmud gumi
da suka amince a buga wannan littafi da
ya shafi rayuwar mahaifinsu domin
al’umma su amfana kuma su yi koyi da kyawawan halayensa musamman
daliban ilimi masu yin da’awah a wannan
zamani. Godiya ta musamman ga AMB.
(DR) CAPT. (Rtd) Muhammad Usman
Barkabali hakimin Daro fai wanda ya
dauki nauyin buga wannan littafi domin kishinsa da addinin musulunci da son
taimaka masa da yada ilimi a ban kasa.
Allah Ya saka masa da alheri kuma ya yi
wa dukiyarsa albarka da zuriyarsa baki
daya, kuma Ya yi masa jagora a cikin
dukkan al’amuransa. Takaitaccen Tarihinsa Da Neman
Iliminsa Sunansa: Ash-sheikh Abubakar Mahmud
Gumi. Nasabarsa: Abubakar, dan Mahmud, dan
Malam Muhammad Marina, dan Sheikh
Aliyu Barau Al-Badawi. {abilarsa : Shi sheikh Abubakar Mahmud
Gumi yana jingina nasabarsa ga kakansa
na biyu, wato sheikh Aliyu Barau Al-
badawi, wanda yake shi asalinsa
balarabe ne dan kabilar Badawi,
wadanda suke yawo da dabbobinsu a daji, sai dai babu cikakken bayanin
yadda yazo kasar Sakkwato, amma dai
zuwan nasa ba zai rasa nasaba ba da irin
abubuwan da suka yi sanadin zuwan
larabawa kasar hausa, musamman ma
bayan karni na goma sha biyar miladiyya. (1500 CE) Haihuwarsa : An haifi malam a garin
Gumi dake jihar zamfara a arewacin
Nigeria. A ranar Juma’a karshen watan
Ramadan na shekarar 1344 Hijirar
Annabi (SAW), wanda ya yi daidai da 7
ga watan Nuwamba na shekarar 1924 ta Miladiyya(). Tasowarsa da neman iliminsa : Malam ya
taso a hannun mahaifinsa a bisa
kyakkyawar tarbiyya da kame kai, kuma
ya fara karatu a hannun mahaifinsa tun
yana dan karami, mahaifinsa ya damka
kulawar karatunsa a hannun daya daga cikin almajiransa mai suna malam Musa.
A sakamakon haka ne wata rana malam
Musa zai je ganin gida can garinsu
Ambursa, wanda yake nisan tafiyar
kwana uku ne daga garin Gumi, sai ya
nemi mahaifin malam cewa a barsu su tafi tare, nan take mahaifinsa ya amince,
a wannan lokaci malam bai wuce dan
shekara biyar zuwa shida ba. A nan ne wata rana malam ya je bara
wani gida sai ya ji matar gidan tana ce
wa ‘yarta ta kori Ungulu dake cin wani
sauran abinci da aka rage, zuwa can
(malam yace) sai na yi bara, sai na ji ta
ce, ga almajirai can a ba su, da jin haka sai na yi sauri na gudu(). Bayan dawowarsu ne daga Ambursa ya
ci gaba da karatun sa inda a nanne ya
sauke Alkur’ani mai girma tare da
haddace wasu surori da dama, kuma ya
fara karatun littattafai, kamar su Ahlari da
sauransu(). Bayan malam ya kai shekaru tara da
haihuwa, a shekarar 1933 mahaifinsa ya
yanke shawarar kai shi makarantar boko,
wacce ake kira “Elemantare” a wancan
zamanin a garin Dogon Daji inda ya yi
shekaru biyu cur. A Shekara ta 1936 zuwa 1942 malam ya
ci gaba da karatunsa na boko a
makarantar “Midil” dake garin Sakkwato. Duk da karatun boko da malam ya sa
gaba a wannan makaranta bai manta da
ci gaba da karatun litattafan Addinin
musulunci ba, inda a nanne ya karanci
littattafai kamar su: Risala, Mukhtasar,
Askari, Mu’allakatis Sitta, da Mukamatul hariri, a hannun malamin su na kimiyya
wato malam Shehu. Daga nan ne malam ya tafi makarantar
Alkalai ta Sakkwato a tsakiyar shekarar
1942 domin yin karatu na shekara daya. Bayan da shekarar ta kare sai malam ya
tafi karo ilimi a makarantar koyon
harkokin shari’a ta Kano, wacce ake kira
da suna (S.A.S) a yau, inda ya kammala
karatunsa a tsawon shekara biyu, a
karamin sashe na makarantar, sannan ya ci gaba da karatunsa a babban sashi na
makarantar shima tsawon shekara biyu. Malam ya sami takardar karo karatu a
makarantar cibiyar koyon aikin malanta
ta Bakht Er-Rida dake can kasar Sudan,
da shi da abokan karatunsa, su bakwai a
shekarar 1954. A can ne suka karanta
babbar Diploma a fannin koyarwa, inda suka kare karatunsu a cikin nasara,
sannan suka dawo gida a shekaran
1956(). Matsayin iliminsa : Malam ya samu
takardar shaidar babban Diploma a
fannin koyarwa a can makarantar cibiyar
koyan aikin malanta dake Bakhtur-El-rida
dake kasar Sudan. Sai dai abin lura a nan
shi ne, wannan takarda da malam ya samu a wancan lokaci daidai take da
takardar digiri na uku a yau, koma
matsayin farfesa, saboda ingancin ilimi a
wancan zamanin da ikhlasin masu yin sa. Takardun shaidar yabo da malam ya
samu : Malam ya samu takardun shaidar
yabo a cikin gida Nigeria da wajenta,
saboda iliminsa da kuma gwagwarmayar
sa wajen kira ga addinin Allah, ga wasu
daga cikinsu : A shekarar 1963, malam ya sami takardar
girma mawa daga gwamnatin kasar
Masar zamanin mulkin Jamal Abdul-
Nasir. A shekarar 1965, malam ya sami takardar
Dakta na shaidar girmamawa daga
Jami’ar Ahmadu Bello da kuma Jami’ar
Ibadan. A ranar 8 ga watan 7 shekarar 1407
bayan hijira, wanda yayi daidai da
shekarar 1987, 8 ga watan 3, malam ya
sami takardar shaidar yabo don yi wa
musulunci hidima ta sarki Faisal wadda
gidauniyar sarki Faisal dake Saudiyya ta bashi. Mazhabarsa : Yana daga dabi’ar dan
adam ya tasirantu da abin da ya tashi
cikinsa, saboda haka malam ya karanta
littattafan Malikiyya a hannun malaman
da suke bin mazhabar malikiyya, kuma ya
tasirantu da ita, domin ita ce mazhabar da ta mamaye Afirka ta yamma. Duk da
haka malam ya kan girmama sauran
mazhabobi. Misali idan kana sauraron
karatunsa idan ya ci karo da hadisin da
ya sabawa mazhabarsa yakan ce,
“wannan hadisin malikiyya ba su yi aiki da shi ba” ko kuma ya ce, “wannan
hadisin ya sabawa malikiyya”. Wasu Daga Cikin Malamansa: 1- Malam ya fara karatunsa ne a hannun
mahaifinsa, wato malam Mahmud na
Gumi, kasancewarsa dama shi ne
shahararren malami a garin Gumi. 2- Malam Musa na Ambursa: Shi ma yana
daya daga cikin almajiran mahaifin
malam, wanda daga bisani mahaifinsa ya
danka kulawar karatunsa a hannunsa. 3- Malam shehu: Wannan malamin
kimiyya ne a makarantar Midil ta
Sakkwato, wanda kuma malami ne
masanin addini, don haka malam ya
karanci wasu littattafai a wajen sa. 4- Sheikh Junaidu wazirin Sakkwato: shi
ma malam ya fara karatun ” kitabul
Nazmul Kubra ” a hannunsa. 5- Sheikh Nasiru Kabara: shi ne malamin
da Sheikh Junaidu ya turo malam
wurinsa don ya ci gaba da karatun
wannan littafi na Nazmul Kubra a
hanunsa. 6- Sheikh Sadik Zaria: Shi ma an ambata
shi daga cikin malamansa. 7- Sheikh Bashir Sudani : Shi ne farkon
shugaban makarantar (S.A.S) a wancan
zamanin. Halayensa : Yana daga cikin halayensa
da dabi’unsa nagari: malam ya kasance
mai hakuri da kame kai, da juriya da
jarumta, da tsantseni da kau-da-kai daga
jahilai. Haka nan kuma ya kasance mai
kunya ne da zurfin tunani, da natsuwa cikin gudanar da al’amuransa, sannan
kuma mai iya zama ne da mutane,
sawa’un na kusa ne ko na nesa, haka
malam ya kasance mutum ne mai dogaro
da Allah. Misalin hakurinsa da kuma kau-da-kai
daga jahilai da wadanda basu fahimci
da’awarsa ba: wata rana malam yana kan
hanyarsa ta tafiya, sai wasu wawaye
suka ce masa, “Malam ka kafirta” take
malam ya yi kalmar shahada, sannan ya tambaye su ya ce, “na dawo?” shi kenan,
ya kama hanyarsa ya tafi. Misalin rashin damuwarsa da abin
duniya: Sau da yawa akan kawo wasu
abubuwa da zai iya rike su a matsayin
mallaka, amma sai ya mika ga kungiyoyin
musulunci domin yin ayyukan musulunci,
kamar motoci da kyautar da sarki Faisal ya ba shi, da makamantansu. Hakanan wadatuwarsa daga barin karbar
zakkah, shi ma misali ne na musamman. Misalin juriyarsa da jaruntarsa: Malam
shi ne malami na farko wanda ya yi fito-
na-fito da dukkanin shehunai da
malaman sufaye na nan kasar, a lokacin
da ake cewa duk wanda bai riki wani
shehi ba daga cikin shehunan darika to shaidan ne shaihinsa, kuma ya tsaya
tsayin daka akan haka har Allah ya
bayyana gaskiya. Misalin kyautarsa: Malam ya bai wa
Labbaika Bello kyautar gidansa dake
unguwar sarkin musulmi dake Kaduna,
da ya yi amfani da shi a matsayin ofishin
Jama’atu Nasril Islam na farko(). Kuma na sha gani wani ya zo ya tambaye
shi wani abu na bukata, sai ya aika dansa
Nuruddeen zuwa gida domin ya karbo
masa wani abu na kudi ya ba wannan
mabukacin. Akidarsa: Malam ya kasance a bisa
akidar magabata na gari, wato akidar
Ahlus-Sunnah Wal Jama’ah, mabiya
Alkur’ani da Sunnah a bisa fahimtar
magabata. Allah ya yi masa rahama
(Amin). Sai dai a karshen rayuwarsa ya shiga cikin masu tattaunawa game da
rashin dawowar Annabi Isa (A.S) Allah ya
gafartawa Malam. Amin. Almajiransa: Almajiran malam Allah ya yi
masa rahama suna da yawa, yadda ba
zamu iya ambaton adadinsu ba. Amma
ga kadan daga cikinsu: Malam Zakariyya Yawale. Malam lawal Abubakar. Malam Ibrahim Tahir. Malam Usman Muhammad (Tsohon
Alkalin Alkalan Jahar Katsina). Sheikh Muhammad Sunusi Gumbi. Alh Tanimu Saulawa, Jakadan Nigeria a
{asar Algeria. Malam Bello Bindawa. Malam Tukur Katsina. Malam Armaya’u Katsina Ni ma na zauna na wani dan lokaci a
wurinsa na yi karatu. Rasuwarsa : Allahu Akbar! Allah ya yi wa
sheikh Abubakar Mahmud Gumi rasuwa
ranar Juma’a 14 ga watan Rabi’ul Auwal
Hijira ta 1413 daidai da 11 ga watan
Satumba na shekarar 1992. Da’awarsa Zuwa Ga Tauhidi Da Riko Da
Sunna Da Basu Kulawa Ta Musamman Hakika malam (Allah ya yi masa rahama)
kusan a iya cewa tun lokacin zamanin
mulkin mallaka shi ne mutum na farko da
ya fito karara yake yaki da shirka da
bidi’a, kuma yake kira zuwa ga tauhidi da
riko da sunnah, da kuma basu kulawa ta musamman. Zan iya buga misali da littafinsa na Al-
Akidatus Sahiha wanda ya rubuta shi a
wancan lokacin. Shi dai wannan littafi na Akidatus-Sahiha
yana bayani ne akan cewa dole ne
musulmi ya bautawa Allah shi kadai a
bisa tsarin koyarwa ta Manzon Allah
(S.A.W). Ga kadan daga cikin abin da ya
fada: “ﺇِﻥَّ ﻣَﻌْﺮِﻓَﺔَ ﺍﻟﺪِّﻳﻦِ ﺗَﻌْﺘَﻤِﺪُ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﻌْﺮِﻓَﺔِ ﻣَﻌْﻨَﻰ ﻛَﻠِﻤَﺘَﻲِ ﺍﻟﺸَّﻬَﺎﺩَﺓِ ﻭَﻫُﻤَﺎ ﻻَ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺍﻟﻠﻪُ ﻣُﺤَﻤّﺪٌ ﺭَّﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠﻪِ، ﻓَﻤَﻌْﻨَﻰ ﻻَ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺍﻟﻠﻪُ – ﻭَﺍﻟﻠﻪُ ﺃَﻋْﻠَﻢُ : – ﻻَ ﻣَﻌْﺒُﻮﺩَ ﺑِﺤَﻖٍّ
ﺇِﻻَّ ﺍﻟﻠﻪُ، ﻭَﻣَﻌْﻨَﻰ ﻣُﺤَﻤَّﺪٌ ﺭّﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠﻪِ ﺃَﻱْ ﺗِﻠْﻚَ ﺍﻟْﻌِﺒَﺎﺩَﺓِ؟
ﻻَ ﻳَﺴْﺘَﺤِﻘُّﻬَﺎ ﺇِﻻَّ ﺍﻟﻠﻪُ ﻻَ ﺗَﻜُﻮﻥُ ﺑِﺮَﺃْﻱٍ ﻭَﻛَﻤَﺎ ﻳُﺤِﺒُّﻬَﺎ
ﺍﻟْﻌَﺎﺑِﺪُ، ﺑَﻞْ ﻫِﻲَ ﻛَﻤَﺎ ﻳُﺤِﺒُّﻬَﺎ ﺍﻟْﻤَﻌْﺒُﻮﺩُ، ﻭَﻛَﺬَﻟِﻚَ ﺃَﺭْﺳَﻞَ
ﺭَﺳُﻮﻟَﻪُ ﻣُﺤَﻤَّﺪًﺍ ﻟِﻴُﻌَﻠِّﻤَﻨَﺎ ﻛَﻴْﻒَ ﻧَﻌْﺒُﺪُﻩُ، ﻓَﻜُﻞُّ ﻣَﻦ ﻳُﺮِﻳﺪُ
ﺃَﻥ ﻳَﻜُﻮﻥَ ﻋَﺎﺑِﺪًﺍ ﻟﻠﻪِ ﺣَﻘًّﺎ، ﻓَﻼَ ﻳَﺴَﻌُﻪُ ﺇِﻻَّ ﺃَﻥ ﻳَﺘَﻌَﻠَّﻢَ ﺭِﺳَﺎﻟَﺔَ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ ) ، ﻳَﻌْﻤَﻞُ ﺑِﻬَﺎ ﻓِﻲ ﻋِﺒَﺎﺩَﺓِ ﺭَﺑِّﻪِ، ﺍﻟﻠﻪُ ﺍﻹِﻟَﻪُ
ﺍﻟْﻮَﺍﺣِﺪُ، ﻭَﻛُﻞُّ ﻣَﻦْ ﻋَﺒَﺪَ ﺍﻟﻠﻪَ ﺑِﻐَﻴْﺮِ ﻣَﺎ ﺟَﺎﺀَ ﺑِﻪِ ﻣُﺤَﻤَّﺪٌ ) ﻓَﻠَﻢْ ﻳَﻌْﺒُﺪِ ﺍﻟﻠﻪَ ﺣَﻘِﻴﻘِﺔً ”. Ma`ana: ” Hakika sanin addini yana
dogara ne akan sanin ma`anar kalmar
shahada shine: la ilaaha illal laah
muhammadur rasuulul lahi; ma`ana: babu
wani abin bautawa bisa cancanta sai
Allah, kuma (annabi) muhammadu manzon Allah ne. Wannan ibadar wacce
Allah kadai Ya cancanta a yi masa ita, ba
ta kasancewa da ra`ayin wani ko yadda
mai bautar ya ga dama, sai dai kamar
yadda Allah Yake so. Saboda haka Ya
aiko manzonsa (annabi) muhammadu domin ya karantar da mu yadda za mu
bauta masa, duk wanda yake so ya zamo
mai bautar Allah na hakika, ba abin da
zai yalwace shi illa ya karanta sakon
(annabi) muhammadu (SAW) kuma yayi
aiki da shi wajen bautar Ubangijinsa abin bauta guda daya; duk wanda ya bauta
wa Allah ba da abin da (annabi)
muhammadu ya zo da shi ba, bai bauta
wa Allah ba hakikatan.” Misali na biyu shi ne, abin da ya fadi a
cikin mukaddimar tafsirinsa “Raddul
Azhan” “ﺍﻟْﺤَﻤْﺪُ ﻟﻠﻪِ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺣَﻔِﻆَ ﻟِﻸُﻣَّﺔِ ﺍﻹِﺳْﻼَﻣِﻴَّﺔِ ﺩِﻳﻨَﻬَﺎ، ﻭَﻻَ ﻳُﻐَﻴِّﺮُﻩُ ﺇِﺩْﺧَﺎﻝُ ﻣُﺪْﺧِﻞٍ، ﻭَﻻَ ﻳُﺒَﺪِّﻟُﻪُ ﺍﺑْﺘِﺪَﺍﻉُ ﻣُﺒْﺘَﺪِﻉٍ، ﻭَﻻَ
ﻳَﻀُﺮُّﻩُ ﺩَﺟَّﺎﻝٌ ﻛَﺬُﻭﺏٌ، ﻭَﻻَ ﻳُﺒْﻠِﻴﻪِ ﻃُﻮﻝُ ﺯَﻣَﺎﻥٍ، ﻗَﺎﻝَ ﻋَﺰَّ ﻣِﻦ ﻗَﺎﺋِﻞٍ : ﭽ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﭼ ﺍﻟﺤﺠﺮ : ٩ Ma`ana: ” Godiya da kirari sun tabbata ga
Allah wanda Ya kiyaye wa alummar
musulmi addininta, shigarwar mai shigar
da (wani abu) ba zai jirkita shi ba, haka
nan bidi`ar mai bidi`a ba za ta canza shi
ba, kuma karyar makaryaci ba zai cutar da shi ba,tsawon zamani ba zai tsofar da
shi ba. Allah (SWT) Ya ce: ” Hakika mu ne
muka saukar da ambato (Alkura`ni) kuma
hakika mu ne masu kare shi” (Al-hijr: 9) Misali na uku shi ne, bude karatunsa da
yakan yi da ayar nan da take nuni a bisa
wajabcin bin hanyar magabata, wacce ta
ginu akan bin Alkur’ani da Sunnah a bisa
fahimtar magabata, ga ta kamar haka: ﭽ ﭮ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﭼ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : ١١٥ Ma`ana: ” Duk wanda ya saba wa manzon Allah a bayan
shiriya ta bayyana a gareshi kuma ya bi
wata hanya da ba ta muminai ba zamu
jibinta masa abin da ya jibinta wa kansa
kuma mu kona shi a jahannama, kuma
makoma ta munana.” Misali na hudu shi ne, irin littattafan da
malam ya karantar da su dukkaninsu na
Sunnah ne, tun daga kan tafsirinsa da ya
rubuta da hannunsa, haka nan littattafan
hadisi da ya karantar tun daga kan Sahih
Al-Bukhari har zuwa na kasa da shi, da kuma littattafan fikihu na mazhabar
malikiyya da kuma littattafan Akida irin su
Fathul Majid. Da’awarsa Zuwa Ga Sauran |angarori na
Addini Allah ya jikan malam, duk da mai da
hankalinsa akan kira ga tauhidi da
sunnah, amma bai manta da bangaren
ibada da mu’amala da zamantakewar
al’umma ba, da sauran halaye nagari. Babban misali da zamu iya dauka shi ne,
farkon rikicinsa da limamin garin Maru a
kan mas’alar alwala da taimama, wanda
limamin da mutanen garin sukan yi sallah
da taimama a maimakon al’awala. Malam ya tsaya kai-da-fata akan wannan
mas’ala har sai da takai su ga zuwa kotu,
inda a karshe dai malam ya sami nasara
(). Misali na biyu shi ne, garkuwar da malam
ya yi da babban littafin nan na fikihun
malikiyya mai suna Mukhtasar Al-Khalil
wanda kowa ya san ya kunshi hukunce-
hukuncen ibada da mu’amala, domin
yana karantar da shi a kowace rana, bayan sallar la’asar, in banda Asabar da
lahadi, ni ganau ne ba jiyau ba!. Hakanan ma ya karantar da Riyadus
Salihina wanda kowa ya sani cewa littafi
ne da ya kunshi koyar da dabi’u nagari. Kulawarsa Wajen Bada Darasi Ga
Dukkan Al’umma Allah ya jikan malam, karantarwarsa ba
ta tsaya ga daliban soro kawai ba, a’a ta
hada dukkanin al’ummar musulmi, hakan
ya samu ne ta irin damar da ya samu ta
yin karatu a masallacin sarkin musulmi
dake Kaduna, sa’annan kafofin yada labarai na jaha da
na tarayya suke dauka domin yada wa
al’umma. A sakamakon haka ne malam ya sami
dalibai daga kowane sashe na kasar nan,
har ma da dukkanin fadin Afirka ta
yamma, domin a karantarwar tasa yana
amfani da hanya mai sauki ga wanda ya
yi karatu, da wanda bai yi ba. Kebewa [aliban Ilimi Lokaci Na
Musamman Don Karantar Da Su Allah ya jikan malam, duk da damuwar sa
na karantar da al’umma gaba daya, bai
manta da kebewa daliban ilimi lokaci na
musamman ba domin karantar da su. Za a iya bada misali akan wannan da
karantarwarsa ta bayan la’asar zuwa
magariba a falon gidansa, wanda tsarin
karantarwar shi ne: Da farko za a karantar da darasin
nahawu gaba daya, ga duk wanda ya je
karatun zai saurara. Bayan nan kuma za
a karantar da Mukhtasar Al-Khalil, sai dai
kowa zai jawo inda yake ne, malam kuma
ya fassara masa, haka sauran littattafan ma akan yi, har kowa a biya masa inda
yake, kamar dai tsarin karatun zaure,
kuma a nan malam yakan gayawa
dalibansa wasu maganganu na
musamman, misali: “ya kamata ace
malami ya sami sana’ar yi domin dogara da kansa, don da haka ne zai sami damar
fadin gaskiya a wa’azinsa da
karantarwarsa”. Bin Fannoni Daban-Daban Na Salon
Karantarwa ga [aliban Ilimi Da Al’umma
Baki [aya Malam ya kan bi fannoni da hanyoyi da
dabaru iri daban-daban wajen isar da
sakon da yake so ya isar ga daliban ilimi
da kuma al’umma gaba daya. Misali inda yake nuni ga wani salon
karantarwa da ya koya a wurin
malaminsa malam Musa, wanda ake
gabatar da abin da littafi ya kumsa a
dunkule kafin a fara bayanin kowane
babi dalla-dalla(). Hakanan malam ya hada tsarin koyarwa
na da, da na yanzu, wato na da shi ne
karatun zaure da kowa zai zo ya dau
littafinsa (wato ya karantashi), ta zamani
kuwa ita ce koyarwar aji da ta halka,
wato inda malami zai bude littafinsa sannan dalibai ma duk mai sha’awa ya zo
da irinsa domin bin abin da ake
karantarwa. Har wa yau malam bai manta da ware
fagen amsa fatawoyi ba domin amsa
tambayoyin masu zuwa daga sassa
daban daban, maza da mata, wannan
kuwa ya ware shi ne daga karfe 11 na
rana zuwa Azzahar. Har ila yau malam bai bar dukkan wata
dama da ya samu ba wajen isar da sako
face ya yi amfani da ita, misali lokacin da
yake malami a makarantar Maru kuma
shine limamin dalibai, kafin kowace
sallah, yakan tabbatar da cewa ya koyar da su wasu shika-shikai na ibada(). Alakarsa Da Mu’amalarsa Ga Wadanda
Suka Sabawa Akidarsa Da Ra’ayinsa Abu ne sananne cewa Allah ya baiwa
malam matsayi da daukaka a kasar nan,
wanda har ta kai shi ga samun mukamin
Alkalin-Alkalai na jahohin Arewa. Shi dai wannan matsayi – kamar yadda
aka sani – malam zai iya amfani da shi
wajen cin zarafin, ko kuma tauye hakkin
mutanen da suka sabawa akidarsa ko
ra’ayinsa, amma ko kadan malam bai yi
haka ba, illa kawai ya yi amfani da duk wani matsayi da ya samu wajen kyautata
mu’amala ga mutane, har ma wadanda
suka sabawa akidarsa da ra’ayinsa. Misalin da zamu iya dauka anan shi ne,
karar da aka daukaka zuwa gare shi a
kaduna wacce ta kunshi rigima tsakanin
wani babban malami da iyalan marigayi
mai unguwar wata unguwa a cikin birnin
kano, inda malamin ya yi masu sama da fadi a kan filinsu na gado, wanda kotun
sarkin Kano a lokacin ta goya masa baya,
su kuma daga karshe suka daukaka kara
zuwa kotun daukaka kara a Kaduna. Wanda hakan tasa malamin ya rika zirga-
zirga wajen malam har yana kokarin yi
masa kyauta, domin dai malam ya yi
masa alfarma, har takai daga karshe dai
ya fito fili ya bayyanawa malam cewa
yana so malam ya yi masa alfarma, domin baya son rabuwa da wannan filin. Inda a nan ne malam ya nuna masa
bacin ransa har yake cewa “Ba don ina
gudun kar na bata iliminka ba, da na sa
an tsare ka”.() A karshe dai malam ya mu’amalance shi
kyakkyawar mu’amala a tsakanin shi da
shi, ba tare da ya ci zarafinsa ko
mutuncinsa ba. Wannan babban misali ne wanda yake
nuna kyakkyawar mu’amalarsa da su. Har
wa yau sabanin dake tsakaninsa da su
bai hana shi ya kai masu ziyara da nufin
yin nasiha a gare su ba, domin ta zama
sanadiyyar shiriyarsu ko kuma yankan hanzari, misali ziyararsa da ya kaiwa
malam Nasiru kabara, da sauransu. {okarinsa Wajen Amfani Da Matsayinsa
Domin Biya wa Mutane Bukatunsu Kamar yadda aka sani, bukatun mutane
dai a dunkule basu wuce neman ilimi na
addini ko zamani ba, domin kyautata
rayuwarsu duniya da lahira, ko kuma
neman abin yi domin dogaro da kai, ko
kuma siyasar su da zamantakewarsu domin kulla alaka tsakaninsu. Malam (Allah Ya yi masa rahama) ya yi
amfani da matsayinsa wajen bada
gagarumar gudummawa mai yawan
gaske ga al’ummar kasar nan a dukkanin
wadannan bangarori. bangaren bunkasa ilimin al’umma: abune
sananne ga al’umma irin yadda malam ya
jajirce tare da yin amfani da dukkanin
damar da yake da ita wajen ganin
al’ummar musulmi ta sami ilimi mai
nagarta tare da sama musu guraben karatu a gida da wajen najeriya, domin
karo ilimi, ni kaina ina daya daga cikin
misali, da kuma wasu jama`a da dama
wadanda malam ya taimaka masu a
wannan bangare. bangaren samawa mutane ayyukan yi
domin dogaro-da-kai: nan ma malam ya
bawa mutane takardu zuwa wurare
daban-daban don samun aikin yi,
sawa’un aikin ofis ko na damara ko kuma
aikin kamfani. bangaren siyasa da zamantakewar
al’umma: a nan ma malam ya karfafi
al`ummar musulmi musamman ‘yan
arewa da su shiga bangarorin siyasa da
mulki domin a dama da su, kasancewarsa
ya hangi irin matsalar da ka iya faruwa idan har basu shiga an dama da su ba,
har ma a nan ya kan ce “Siyasa tafi
sallah” amma aka kasa fahimtarsa a
wancan lokacin. Wannan janibi na taimako, ya taimaka
wa yaduwar da’awar malam matuka
wajen shigar da’awar bangarori daban-
daban na rayuwar al’umma, domin
wannan ne ya sa kowanne dalibi nasa ya
zama wani babban wakili nasa a duk inda yake. {okarinsa Wajen Zaburar Da Musulmi Da
Nuna Musu Wajabcin Shiga |angarori
Daban-Daban Na Hukuma Allah Ya jikan malam, hakika da’awarsa
ta taimaka kwarai da gaske wajen
zaburar da al’ummar musulmi da wayar
masu da kai wajen shiga bangarori
daban-daban na hukuma, domin samun
wakilci, da kuma gudun kar a danne su a mai da su saniyar ware. Malam ya yi amfani da wata ka’ida wacce
take sananniya a wurin daliban ilimi,
wacce malamai magabata (Malaman
usuulul fikh) suka sa, inda suke cewa
“Addharuuratu Tubiihul Mahzuuraat”
ma’ana “larura takan halatta haramun” Kamar yadda aka sani cewa turawan
mulkin mallaka sun zo sun mulki kasar
nan kusan shekara dari, kuma duk sai da
suka kakkabe duk wani tsari na ilimi dana
gudanarwa na addinin musulunci, suka
sanya nasu, a bisa harshen su na turanci, wanda wannan ne ya sanya mummunar
kyama da musulmi ke yi wa ilimin boko,
da kuma amfani da akan yi da shi bayan
an yi shi. Wannan ne ya sa malam ya harara ya
hararo ya ga cewa ba yadda za a yi
musulmi a dama da su face sai sun yi
karatun zamani da kuma amfani da shi,
ba don komai ba, sai don da shi ne ake
shiga dukkan ayyuka na kasa. To wannan ne yasa malam ya tashi
haikan ba dare ba rana wajen zaburar da
musulmi, a cikin dukkan karatuttukansa
cewa su tashi su yi karatun boko, amma
su hada shi da tarbiyyar addinin
musulunci, domin su shiga dukkan fagage na rayuwa, saboda a dama da su. Alhamdu lillahi, mun godewa Allah,
sa’annan mun godewa malam domin ba
don wannan fadakarwar da aka samu ba,
to da bamu san inda zamu tsinci kanmu
ba a yau. To anan ya kamata ga masu da’awa na
yau da su rika koyi da wannan manhaji
na malam, wajen sanin yanayin da suke
rayuwa a cikinsa, kuma su san yadda za
su warwareshi. {okarinsa Wajen Hada Kan Musulmi da
Masu Da’awa Malam ya taso a yammacin Africa a kasar
hausa inda mafi yawancin musulmin
wurin suke bin darikun sufaye masu
bautar shehunansu, kuma wanda kowa
ya san irin barnar da take cikin wadannan
hanyoyi, to Allah a cikin ikonsa ya haskaka wa malam zuciyarsa wajen gane
barnansu da kura-kuransu, kuma ya yi iya
iyawarsa wajen nunawa malaman
wannan zamani irin kura-kuran
wadannan littattafai na sufaye a cikin
ruwan sanyi, kuma a boye ba tare da mabiya sun gane ba, domin samun hadin
kan musulmi, amma ina! Hakan ya ci tura,
saboda soye-soyen zukantansu, kamar
yadda ya fadi hakan a cikin littafinsa Al-
Akidatus Sahiha, in da ya ce: “ﻭَﻣَﺎ ﻛِﺪﺕُّ ﺃَﻛْﺘُﺒُﻬَﺎ ﻣِﻦْ ﺧَﻮْﻑِ ﻭُﻗُﻮﻉِ ﺍﻟْﻔِﺘَﻦِ؛ ﻟَﻮْﻻَ ﻣَﺎ ﻗَﺎﻝَ ﺍﻟﻠﻪُ ﻓِﻲ ﻛِﺘَﺎﺑِﻪِ ﺍﻟْﻌَﺰِﻳﺰِ : ﭽ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﭼ . () ﻭَﻓِﻲ ﺍﻟْﺤَﺪِﻳﺚِ ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ ﻫُﺮَﻳْﺮَﺓَ ) ﻗَﺎﻝَ : ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠﻪِ ) “ : ﻣَﻦ ﺳُﺌِﻞَ ﻋَﻦْ ﻋِﻠْﻢٍ ﻓَﻜَﺘَﻤَﻪُ، ﺃُﻟْﺠِﻢَ
ﻳَﻮْﻡَ ﺍﻟْﻘِﻴَﺎﻣَﺔِ ﺑِﻠِﺠَﺎﻡٍ ﻣِﻦ ﻧَﺎﺭٍ ”(). Ma`ana: “Na yi kusa in ki rubutashi
saboda tsoron aukuwar fitina, ba don
abinda Allah Ya fada a cikin littafinsa
mabuwayi ba: (lallai wadanda suke boye abinda muka
saukar na hujjoji da shiriya bayan Mun
bayyanasu ga mutane a cikin littafi,
wadannan Allah Yana la`antarsu kuma
masu la`anta na la`antarsu. Sai dai
wadanda suka tuba kuma suka gyara kuma suka yi bayani, to wadannan zan
karbi tubarsu, Ni mai yawan karbar tuba
ne mai jinkai. ( ya zo cikin hadisi daga
Abu Huraira (RA) ya ce: manzon Allah
(SAW) ya ce: “duk wanda aka tambaye
shi wani ilimi, sai ya boye; za a yi masa linzami na wuta ranar Alkiyama”. Abin da malam ya bayyana daga baya na
kura-kuransu, ba raba kan musulmi ba
ne, a’a hada kansu ne da maida su zuwa
ga tushe na asali, saboda fadin Allah
Madaukakin Sarki: “Ku yi riko da igiyar
Allah gaba daya kada ku rarrabu” Yana daga cikin misalin da ke nuna
kokarin malam na son hada kan musulmi,
kasancewarsa wakili a cikin wakilai na
farko da suka assasa majalisar hadin kan
musulmi ta duniya dake Makkah a
shekarar 1962. Abu na uku da ba zan manta ba na
kokarin da malam ya yi ta yi wajen dinke
barakar da ta faru a cikin kungiyar
Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa Ikamatus
Sunnah, na kiran taron sulhu da ya yi,
domin kokarin hada bangarorin guda biyu masu da’awa, su ci gaba da tafiya tare,
domin cimma manufar da aka sa a gaba
ta da’awa. A nan ne ma, ba zan manta ba
malam yana magana yana zubar da
hawaye don bakin cikin wannan rabuwa,
wannan ya faru a shekarar 1984. Yin Amfani Da Sababbin Hanyoyi Na
Zamani A Wajen Da’awah Kowanne mai da’awah yakan so ya ga
da’awarsa ta karbu, kuma ta shiga
kowanne sako da lungu na al’umma a
cikin kankanen lokaci, duk da cewa
malam ya zo ya sami malamai a kasar
hausa ba su fiye amfani da kafafen watsa labarai na zamani ba, kai! wasu ma
suna ganin yin hakan wani laifi ne!,
amma malam da ya zo ya ci gajiyar
kafafen watsa labarai na gani da na ji, da
na karantawa, kuma sun taimaka masa
kwarai da gaske wajen yaduwar da’awarsa cikin kankanen lokaci. Ni kaina na fara fahimtar malam ne a
rediyo, kafin na zauna da shi. Wannan
shi ne ya sa malam yakan kirawo ‘yan
jarida da mujahidai, saboda yadda suke
taimakawa wajen yada da’awa a cikin
kankanen lokaci. {okarinsa Wajen Samar Da {ungiyoyi Da
Kuma Gudummawar Da Ya Bayar Domin
Tabbatar Da Ayyukansu Kasancewar malam (Allah ya jikansa) ya
taso a wata kasa da take da’awar kin
daukar wani addini a matsayin tsarin
gudanar da mulkinta, ballantana ta dauki
nauyin dukkan ayyukan musulunci da
yada shi, wannan ne ya sa malam ya ga ya kamata a samar da kungiyoyi na
addinin musulunci, wanda za su maida
hankali wajen kula da kira zuwa ga
musulunci, da yada shi, da kuma ilmantar
da wadanda suke cikinsa. Wannan ne ya sa malam ya hada kai da
firimiya Ahmadu Bello Sardaunan
Sakkwato wajen kafa kungiyar Jama’atu
Nasril Islam, a shekarar 1962, kuma ya
bata duk wata gudummowa mai yawan
gaske(). Malam ya yi aiki tukuru a karkashin
wannan kungiya shi da Sardauna da
sauran ‘yan kungiya wajen musuluntar
da kiristoci da maguzawa, wanda
wannan ne ya sa arnan cikin gida da na
waje suka shirya makirci wajen yi masa kisan gilla. {ungiya ta biyu wacce aka kafata da
malam, ita ce kungiyar hada kan musulmi
ta duniya, dake Makkah, kuma malam ya
rika halartar taronta na shekara-shekara
har Allah ya yi masa rasuwa. {ungiya ta uku ita ce, kungiyar Jama’atu
Izalatul Bidi’a Wa Ikamatus Sunnah
wacce malam ya kasance uba gareta, tun
da aka kafata a shekarar 1978(), kuma
malam ya ba ta gagarumar gudummawa
da shawarwari nagari ga shugabanninta, domin ci gabanta, musamman ma kafin a
samu sabani a cikinta. Kiransa ga Sarakuna da Masu Mulki da
Irin Mu’amalar da yayi da su Allah Ya jikan malam, da’awarsa bata
tsaya ga kauda kura-kuran da talakawa
da almajirai sukan yi kawai ba, ta hada
har da sarakuna da masu mulki, inda ya
kiraye su zuwa ga aiki da hukunce-
hukuncen shari’a da yin adalci a cikin mulkinsu. Babban misali na farko da zamu dauka
shi ne, rikicin da ya faru tsakanin malam
da hakimin Maru da kuma limamin garin
Maru, wanda har ya hada da sarkin
musulmi a shekarar 1950, akan mas’alar
yin sallah da taimama ba tare da wani uzuri na shari’ah ba, wanda ya yadu a
kasar Sakkwato a wancan lokacin. Malam ya yi iya iyarwarsa ya ga cewa an
kauda wannan mas’ala a cikin ruwan
sanyi, amma abin ya ci tura, har sai da ya
kai ga bijirar da mas’alar zuwa ga
sarakunan arewa gaba daya, malam dai
bai yi kasa a gwiwa ba, ya tsaya tsayin daka har sai da aka kai ga cin nasara na
kauda wannan mas’ala, ta yin sallah ba
alwala a garin Sakkwato(). Misali na biyu shi ne, wasika ta sirri da
malam ya aikawa sarkin musulmi domin
yi masa gyara a wani kuskure da ya ga ya
yi a cikin jawabinsa na sallah da ya
gabatar wa al’umma. Kuskuren kuwa shi ne, hada Allah ya yi
da sarkin Ingila a cikin godiya, inda yake
cewa kamar haka, “Ina so in fara da
godiya ga Allah Madaukakin Sarki da
Annabinsa Muhammad (S.A.W) da Shehu
Usman [an fodiyo, wanda ya jaddada mana addininmu a nan kasar, tare kuma
da sarkin Ingila wanda muke karkashin
tutarsa ta adalci”(). Duk da wannan wasika da malam ya yi ta
a sirri domin gyara, amma sai ga shi cibi
ya zama kari, inda har ta kai ake kokarin
ladabtar da malam, amma Allah a cikin
ikonsa ya kare bawansa, haka dai sunnar
Allah take ba ta canzawa. Misali na uku kuma shi ne, malam ya yi
mu’amala da sardauna kyakkyawar
mu’amala tun kafin ya zama firimiya,
wanda abu ne sananne ba sai mun fada
ba, ya bashi shawarwari masu yawa
game da taimaka wa addininsa. Misali malam ya ba shi shawara lokacin
da yake siyasa akan cewa: ya rika kashe
ko da kashi daya ne daga cikin goma
akan addini daga irin kudaden da yake
kashewa a siyasa, wanda hakan ya jawo
masa farin jini, ba ma ga mabiyansa ba har ma da mahaliccinsa(). Hakazalika malam ya baiwa sardauna
shawara na a ilimantar da mutane
addininsu, a sakamakon abin da suka
gani a aikin haji na jahilcin ‘yan Nijeriya
wurin aikin jifan shaidan da manya-
manyan duwatsu da takalma. Nan take sardauna ya karbi shawararsa, kuma
suna dawowa Nigeria ya aiwatar da ita(). Alakar malam da sardauna a takaice tana
da yawan gaske kuma ta taimaka matuka
wajen yada da’awar malam din, domin
Sardauna ya taimaka da mulkinsa da
kujerarsa, shi kuma malam ya taimaka da
iliminsa da takawarsa. Wadannan abubuwa guda biyu idan suka hadu ba
karamar nasara akan samu ba. Da Allah
ya sa Sardauna ya sami tsawancin
kwana, to da an yi daula irin ta Ali Sa’ud
da ke kasar Sa`udiyya. Misali na karshe da zan iya kawowa a
yanzu shi ne, mu’amalar da malam ya yi
da Janar Buhari, shi Buhari a wancan
lokaci ya zo da wani tsari na son yin
gyara a bisa barnar da ya tarar na rashin
bin doka da oda, wanda kokarinsa na yin gyara shi ma ya auka cikin wasu kura-
kurai da suka saba wa shari`ar
musulunci, amma duk da zafin da ya zo
da shi, malam bai fasa fada masa kura-
kuransa ba, da nufin ya gyara. Daga cikin abubuwan da malam ya
fadawa Buhari a wancan lokaci a
matsayin shawara shi ne, “na roke shi ya
sake duba al’amarin mutanen da aka
tsare, na bayyana masa a fili cewa ni ba
na goyon bayan aikata kowace irin rashin gaskiya, amma kuma har ila yau ina
ganin babu adalci a tsare mutum ba tare
da yi masa shari’a ba. Saboda haka lallai
ne a yi wa wadanda aka kama shari’a ba
tare da wani jinkiri ba. Daga cikin su
wadanda aka samu sun aikata laifi a kwace dukiyarsu gwargwadon laifinsu a
mayar wa gwamnati, domin kuwa dukkan
mai iyali wanda aka tsare har tsawon
lokaci ba tare da an yi masa shari’a ba, to
kuwa ba shi kadai aka tsare ba, har ma
da iyalinsa da sauran wadanda yake taimaka wa”(). Har ila yau abin da ya faru a kasuwar
Kaduna na bada umarni da hukumomi
suka bayar, duk wanda yake da rumfa ba
bisa ka`ida ba yasan na yi, ba tare da an
bashi wani wurin ba, kuma da lokaci
isasshe. Anan ma malam ya nuna masu wannan ya saba wa shari`a. A kokarin malam na gaya wa masu mulki
gaskiya da nufin su gyara bai tsaya ga
kasarsa kadai ba. Domin lokacin da
shugaban kasar Libiya mu`ammar kazzafi
ya bayyana mummunar akidarsa ta
inkarin Hadisi a wurin wani taron maulidi da ya yi a shekarar 1978AC. inda ya fito
fili yace: “Babu yadda za`a yi duniyar
musulmi ta cigaba har sai an kona
dukkan littattafai an bar Al-kur`ani kadai”. Bayan Gaddafi ya bayyana wannan akida
ne, sai kungiyar Rabidatul Alamil Islami
da ke da cibiya a kasar Saudi Arebiya
suka tura masa wadanda za su yi masa
nasiha, wanda a cikinsu akwai malam,
kuma yana daya daga cikin malaman da suka kausasa masa magana saboda
tsananin kishinsu da sunnah da kuma
sanin hadarin wannan akida da wajabcin
gaya wa shugaba gaskiya. Haka dai malam ya yi ta gyara da ba da
shawara ga masu mulki, kan yadda za su
taimakawa addininsu da al’ummarsu. Kiransa ga Masu Dukiya da Irin
Mu’amalarsa da su Da’awar malam (Allah ya yi masa
rahama) ruwan dare ce game duniya, ta
shafi kowa da kowa, saboda haka masu dukiya ma malam bai barsu a baya ba, ya
yi iya iyawarsa akan ya ga ya kira su
zuwa ga hanya madaidaiciya,
musamman ma kasancewar a wancan
lokacin akwai masu amfani da tsafe-tsafe
da canfe- canfe wajen neman dukiyarsu, da kuma amfani da dukiyarsu wajen yada
darikun sufaye. Don haka malam ya yi
kokari iya iyawarsa wajen yi masu wa’azi,
ba tare da ya ji tsoron kasancewar su
masu dukiya ne ba, ko kuma ya yi
kwadayin abin hannunsu wurin bin son zuciyarsu. Hakanan wadanda suke
neman dukiyarsu ta hanyar haramun, su
ma malam bai yi shakkar yi musu wa’azi
ba. Wani abu da ya kara sa da’awar malam
ta samu karbuwa a wajen masu kudi shi
ne, fitowarsa da ya yi fili ya bayyana
cewa shi baya bukatar zakkah, haka nan
kana’arsa da wadatar zuci da Allah ya ba
shi. Wadannan abubuwa ba karamin tasiri
suka yi a zukatan masu kudi wajen
karbar da’awar malam ba. [aya daga misalan da zamu iya dauka shi
ne da’awar da malam ya yi zuwa ga daya
daga cikin shahararrun masu kudin kasar
nan, wato Alh Ahmadu Chanchangi. Shi
dai wannan mutum da yana sana’ar
dakon giya, amma kuma a karshe Allah ya taimake shi ya tuba, ya bari, ta hanyar
wa’azin malam. Kiransa ga Sauran Mutane da Irin
Mu’amalarsa da su Kiran malam kuwa ga sauran mutane,
nan ya fi yawa, dalili kuwa yana kira ne
zuwa ga gaskiya da fitar da mutane daga
kangin bautar wanin Allah zuwa bautar
Allah Makadaici, da kuma wayar masu da
kai a cikin al’amuran addininsu, da kuma matsalolin rayuwarsu. Shi kuma dabi’ar
dan adam a koda yaushe yakan so fita
daga dukkan wani kangi na wahala da
bauta, zuwa wani abu mai sauki. Wannan
ne ya sa tun malam yana matsayin dalibi
a kananan makarantu zuwa manya, dalibai talakawa suke baibaye da shi,
domin jin dadin wa’azinsa da
karantarwarsa. Hakanan ma duk mai halartar
karatuttukansa na yau da kullum zai ga
kusan kashi tamanin bisa dari talakawa
ne, kuma wannan ita ce sunnah wacce ta
gabata tun zamanin Annabawa, cewa
talakawa galibi su ne suka fi karbar gaskiya. Kiransa ga Wadanda ba Musulmi ba Da’awar malam ga wadanda ba musulmi
ba, ta yi tasiri kwarai da gaske,
musamman ma idan aka yi la’akari da
yadda mabiya addinin kirista da
maguzawa suka rika shiga addinin
musulunci tawaga- tawaga a lokacin da’awarsa. Kiran malam ga wadanda ba musulmi ba,
a karon farko ya samu karbuwa a
sanadiyar hadin kai da goyon baya da ya
samu daga wajen Firimiya Ahmadu Bello
Sardaunan Sakkwato, domin sun hada
kai, shi Sardauna ya yi amfani da kujerarsa ta mulki, shi kuma malam ya yi
amfani da iliminsa, samun haduwar
wadannan abubuwa guda biyu, ya
taimaka kwarai da gaske wajen yada
musulunci ga wadanda ba musulmi ba a
Nijeriya. Babban misali akan wannan shi ne,
jawabin da Firimiya Alh Ahmdu Bello
Sardaunan Sokoto ya gabatar wa taron
musulmi na duniya da aka yi a Makkah a
shekarar 1965, in da ya yi cikakken
bayani bisa nasarar da suka samu a Nigeria, sakamakon kokarin da’awarsu, in
da aka sami a kalla mutane 176 zuwa
930 sun shiga addinin musulunci a
tsakanin shekara ta 1963 – 1965(). Karo na biyu kuwa bayan kashe
Sardaunan Sokoto, da’awar malam ta
dan sami tawaya, amma duk da haka bai
yi kasa a gwiwa ba, ya ci gaba da
karantarwa da wa’azantarwa cikin hikima
da basira, wanda hakan ya jawo wadanda ba musulmi ba, suka rika zuwa
da kansu suna shiga musulunci a
wuraren karatunsa, musamman ma da
azumi a lokacin tafsirin Alkur’ani. Allah
kadai ya san iya adadin da suka
musulunta ta hanyar karantarwarsa. Samun Ilimin Zamani da yayi, da Kuma
Amfanarwarsa da shi Malam dai (Allah ya ji kansa) ya yi
karatun boko a mataki na farko da na
biyu. Na farko shi ne karatunsa da ya yi a
makarantar Elemantari ta Dogon Daji a
jihar Sokoto shekarar 1933, in da ya yi
shekara biyu. Mataki na biyu kuma shi ne, karatunsa a makarantar Midil a shekarar
1936 – zuwa 1942, shi ma dai a garin
Sokoto, bayan nan kuma malam ya tafi
makarantar koyon alkalanci ta Sokoto
domin yin karatu na shekara daya(). Wannan karatu na boko da malam ya yi,
ya sa ya amfana, kuma ya amafanar
kwarai da gaske, zamu iya kasa amfanin
kashi biyu : 1 – Kashi na farko shi ne, Amfanuwarsa
shi kansa. 2 – Kashi na biyu shi ne, Amfanuwar sa da
ya yi da shi. Misalai na farko su ne : Ya iya magana da harshen kasa
(Turanci). Yin abokai da manya-manyan ma’aikata
da shugabanni wadanda makaranta ta
hada su. Samun damar rike babban mukami a
kasa, kamar alkalin alkalai. Samun damar shiga tarurruka na
gwamnati. samun damar gogayya da cudanya da
mutane daban-daban. Wannan ya koya masa bin tsari na tafiyar
da da’awarsa da al’amuransa. Misalai na biyu kuwa su ne: Samun damar wallafe-wallafe da hausar
boko. Yin wa’azi da yaren turanci ga wadanda
ba sa jin hausa. Rubuta wasiku zuwa sassa daban-daban
na gwamnati da ma’aikatu da kamfanoni
don bukata ta da’awa, ko taimakawa
wani. Yin magana da kusoshin gwamnati da
kuma fada musu gaskiya. Ta sanadiyyar sa manya-manyan ‘yan
boko na jami’an gwamnati da na
al’umma sun karbi da’awarsa, kuma sun
ba shi goyon baya. Gudummowar da ya Bayar Wajen
Wallafe-Wallafe Allah ya jikan malam, ya bada
gudummowa gagaruma ta hanyar
wallafe-wallafen da ya yi a fannonin
addinin musulunci daban-daban,
musamman ma wadanda ya yi da
harshen hausa, domin ni a iya sanina shi ne malami na farko a kasar nan da ya
fara rubutu da harshen hausa da sunan
raya addini kai tsaye. Malam ya wallafa littatttafai da dama a
bangarori daban-daban, kamar: Akida,
Hadisi, Fikihu, Mu’amala, Siyasa, Tattalin
arziki, Tarbiyya, da sauransu. Littattafan, wasu sun kasance da
harshen larabci, wasu kuma da hausa.
Misalan na larabcin su ne : ﺭَﺩُّ ﺍﻷَﺫْﻫَﺎﻥِ ﺇِﻟَﻰ ﻣَﻌَﺎﻧِﻲ ﺍﻟْﻘُﺮْﺁﻥِ . Littafin tafsiri ne malam ya wallafa shi,
domin ya dawo da hankulan mutane
zuwa ga fahimtar ma’anonin Alkur’ani. ﺍﻟْﻌَﻘِﻴﺪَﺓُ ﺍﻟﺼَّﺤِﻴﺤَﺔُ ﺑِﻤُﻮَﺍﻓَﻘَﺔِ ﺍﻟﺸَّﺮِﻳﻌَﺔِ . Wannan littafi yana daga cikin littattafan
malam mafiya mahimanci a rayuwarsa,
domin a cikinsa ne ya bayyana cikakkiyar
akidarsa irin ta magabata nagari, kuma
malaman darikun sufaye suka sallama
masa, suka san in da ya sa gaba. ﺍﻹﺳْﻼَﻡُ ﻭَﻧَﻮَﺍﻗِﻀُﻪُ . Malam ya wallafa shi ne domin ya yi
bayanin musulunci da kuma abin da yake
warware shi. ﺍﻟﻮِﺭْﺩُ ﺍﻟْﻌَﻈِﻴﻢُ ﻣِﻦَ ﺍﻷَﺣَﺎﺩِﻳﺚِ ﻭَﺍﻟْﻘُﺮْﺁﻥِ ﺍﻟْﻌَﻈِﻴﻢِ . Malam ya wallafa shi don ya kwadaitar
da musulmi su koma kan ingantaccen
zikiri na asali, irin na Annabi (S.A.W)
kuma su watsar da zikirai na bidi’a
wadanda suka zo ta hannun malaman
darikun sufaye. ﻗَﻀَﺎﻳَﺎ ﻓِﻲ ﺍﻻﻗْﺘِﺼَﺎﺩ ﻭَﺍﻟﺘَّﻌَﺎﻣُﻞِ ﻣَﻊَ ﺍﻟْﺒُﻨُﻮﻙِ ﺍﻟﺮِّﺑَﻮِﻳَّﺔِ . Malam ya rubuta wannan littafi don ya yi
bayanin yadda tattalin arziki yake a
musulunci, kuma ya bayyana ra’ayinsa a
kan bankuna na riba. Misalan na Hausa kuwa, su ne kamar
haka : 1- Fassarar Arba’unan Nawawi, wanda
bugun farko ya kasance a shekara ta
1959. 2- Fassarar Juzu’u Tabara. 3- Fassarar Alkur’ani mai girma cikakke.
Wannan ba karamin taimakawa ya yi ba,
wajen fahimtar ma’anonin Alkur’ani da
harshen hausa. 4- Littafin matakan Musulunci, Dalilin
rubuta wannan littafi shi ne, Alh. Ahmad
Bello Firimiya shi ne ya nemi malam ya
wallafa wani karamin littafi mai saukin
karantawa da hausa, saboda sababbin
shiga musulunci. 5- Fassarar littafin (Nurul Albab) na
Shehu Usman dan Fodiyo. 6- Fassarar littafin (Usulud deen Fi
Masa’ilil Li’itikad) shi ma dai na Shehu
Usman dan Fodiyo ne. 7- Fassarar littafin (Hidayatud dullabi fi
ahammi masa’ilil deen) shi ma na Shehu
Usman dan Fodiyo ne. 8- littafin (Aikin hajji da umara). Wanda
ya wallafa a shekarar 1976. Wadannan littattafai ba karamin tasiri
suka yi ba, a cikin al’ummar musulmin
Nigeria, har ma da makwabtan su, wajen
farkar da su da zaburar da su da sanin
addininsu, da kuma riko da shi. Wanda tun daga bayan shehu Usman da
dan-uwansa Abdullahi da dansa
Muhammad Bello ba a sami wanda ya yi
ma musulunci hidima ba, da iliminsa da
alkalaminsa da lokacinsa ba kamar
Sheikh Abubakar Mahmud Gumi. Tarbiyyarsa ga Iyalansa da ‘Ya ‘Yansa a
Bisa Tafarkinsa Magana akan abin da ke tsakanin malam
da iyalansa abu ne mai wuyar sani,
amma a bisa zahiri malam ya tarbiyantar
da iyalansa tarbiyya irin ta addinin
musulunci. Kasancewar Allah ya
albarkaci malam da iyalai masu yawa, amma yawan nasu bai sa malam ya kasa
tarbiyyar su ba a bisa tsari na addini, ko
kuma ya kasa ilmantar da su ba, ko kuma
uwa-uba kasancewar sun fito daga
dakuna daban-daban bai haifar masu da
matsaloli irin na ‘yan ubanci da sauransu ba, amma dai kamar yadda bahaushe
yake fadi “Waka a bakin mai ita tafi dadi”
don haka ga abin da yake cewa da
kansa: “Gaba daya dai matana hudu da ‘ya ‘ya
ashirin da tara, wadanda daga cikinsu
akwai hafsoshin soja, da ma’aikatan
gwamnati, da likitoci da injiniya da matan
aure, da lauyoyi da malaman makaranta
da ma’aikatan banki, da kuma ma’aikatan kamfanoni, da na sauran harkokin
kasuwanci, kusan in ce babu wata sana’a
wadda wani daga cikin gidana bai iya ba.
Da na tuna duk wadannan sai na kara yin
murna da Allah (S.T.W) ya taimakeni
yadda ban taba samun wadansu matsaloli ba dangane da iyalina”(). Muna
rokon Allah ya yi masu albarka kuma ya
kiyaye daga dukkan abin ki. Amfanuwar da iyaye Mata Suka yi da
Da’awarsa Kafin zuwan da’awar malam, Mata sun
kasance a kasar hausa ba su san komai
ba, sai canfe-canfe da tsafe-tsafe da
al’adu, da kuma karatun da mata tsofaffi
kan shiga gidaje suna koyarwa da sunan
Ilimin addini, misali irin karatun kwanciyar tsakar daki, da karatun fitsari, da
makamantansu, domin tun bayan
da’awar Shehu Usman dan Fodiyo da
karantarwarsa ba a karantar da su ba, sai
dan abinda ba a rasa ba. Amma da malam ya zo ya jajirce wajen
fadakar da al’umma game da
muhimmancin ilimantar da iyaye mata
domin ilimantar da su ilimantar da
al’umma ne. alhamdulilah! A yau an wayi
gari al’umma sun fahimci muhimmancin ilimin mata har takai ga babu wani yanki
da tarin al’umma suke zaune wanda
babu makarantun koyar da iyaye mata.
Wanda a da, a kasar nan abu ne
mawuyaci a sami mace malama ta addini,
amma sai ga shi a yau akwai inda zaka sami makarantar mata, dukkan
malamanta mata ne, duk da masu suka
nayin suka! Koda yake dai an gamu da matsaloli a
wancan lokaci inda ta kai wasu mazaje
sun saki matansu kawai don suna zuwa
makaranta, su kuma matan saboda karfin
imaninsu da fahimtar addininsu, suka
zabi rabuwar auren akan zama bisa jahilci, wanda da yawa na san matan da
suka zauna gidan malam bisa wannan
dalili, har suka sami mazan aure, amma a
yau godiya ta tabbata ga Allah, duk irin
wannan ya kau, sai abin da ba a rasa ba. Kammalawa Wannan shi ne dan abin da na iya
rubutawa dangane da wannan babban
mashahurin malami, mujaddadi, muslihi a
zamaninsa, kuma abin koyi ga ‘yan baya.
Allah nake roko ya yi masa rahama, ya
gafarta masa, kuma ya saka masa dabin da yakan saka wa bayinsa nagari, Allah
yasa Aljanna ce makomarsa. Amen Daga abin da ya gabata zamu ga yadda
da’awar malam ta shiga kowane sashe
na rayuwa, babu inda malam bai ba da
gudummawa ba, wannan wani kalu-bale
ne ga masu yinda’awa a yau, a kan su
fadada da’awarsu ta shafi dukkan sassan rayuwa gaba daya, kamar yadda malam
ya yi, musamman ma a wannan lokaci da
ake fuskantar kalu-bale daban-daban ta
fuskar tsaro, tattalin arziki, tarbiyya, ilimi,
ballantana akida ingantacciya da yau
take fuskantar barazana ta kowane bangare. Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga
Allah, wanda ya bani ikon rubuta wannan
dan littafi duk da raunina da karancin
lokaci na. Tsira da aminci su kara tabbata
ga shugaban halitta Annabi Muhammad
(S.A.W) da iyalan gidansa, da sahabbansa, da kuma duk wadanda suka
bi tafarkinsa har izuwa ranar sakamako. Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa
Barakatuhu Dan uwanku a musulunci Abu Jabir Abdullahi Muhammad Getso Mai karantarwa a tsangayar ilimin
addinin musulunci ta kwalejin Sa’adatu
Rimi, Kumbotso, Kano, Nigeria. Email: getso1973@yahoo.com Phone: 08023032008 17/01/1433AH = 12/12/2011AC.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s