Ina Na San Nafilolin Rawatib? Dr Jamilu Yusuf Zarewa


*Tambaya* Salaamoon alaykoom, malam Dan
Allaah ina son ingancin wadannan
sallolin nafilan 1- raka’ah 12 a wuni
Allaah zai gina wa mutum gida a
aljannah 2- raka’a takwas kafin sallan
azahar da bayan sa wuta ba zai ci shi ba 3- raka’ah hudu kafin sallan la’asar *Amsa*
Wa alaikum assalam, tabbas hadisi ya
tabbata cewa: (Duk wanda ya yi
sallolin nafila raka’ioi 12 Allah zai gina
masa gida a cikin aljanna. Zaid bin Arkam daya daga cikin
sahabban Annabi (SAW) ya fassara
wadanann nafiloli da Sifa kamar haka:
Raka’a biyu kafin sallar asuba, raka’a
hudu kafin sallar Azahar, raka’a biyu
bayanta, raka’a biyu bayan sallar Magriba, sai kuma raka’a biyu bayan
sallar Isha. Ragowar abin da ka fada ban san shi
ba a hadisai a ingantattu, rashin sanina
kuma baya nuna babu shi. Allah ne mafi sani *Dr Jamilu Zarewa* 13/02/2018

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s