TARIHIN MARIGAYI SHEIKH Dr. ALI MUSTAPHA MAIDUGURI.


image

An haifi Sheikh Dr. Ali Mustapha a anguwar Fezzan dake Maiduguri a shekarar 1968. Mahaifin shi (Alhaji Shettima Bukar Mustapha Konduga) dan asalin Kwanduga L. G. A ne, mahaifiyar shi (Hajiya Yakaka Bukar) ‘yar asalin garin Dikwa LGA ce.
Shi dai Dr. Ya fara karatun shi na farko a wurin mahaifin shi inda yafara da karatun Tahiya, Sallah da Al-qunutu. Daga bisami yashiga makarantar Allo (tsangaya) a wajen wani malami mai suna ‘Mallam Awa’ a nan Fezzan a shekarar 1972, yayi karatu har zuwa lokacin da malamin nashi ya samu larurar tabin kwakwalwa sakamakon hatsarin mota. Hakan yasa mahaifin shi yasa shi a makarantar Islamiya mai suna ‘Madarasatul Nurul Atfan’ wadda a yanzu aka canja mata suna ‘Usman Islamiya School’ a shekarar 1975.
Bayan ya kammala Aji biyar (class 5) a wancan lokacin, sai Mallam ya garzaya zuwa High Islamic Collage Maiduguri a shekarar 1982, inda yayi shekaru hudu (4) a matakin secondary, daganan yaci gaba da karatun Diploma a Fannin Hausa, Larabci da Shari’a a wannan makarantar. Bayan ya gama a shekarar 1990, sai aka musu jarabawar daukan malamai inda yasamu nasarar zama malami a nan ‘High Islamic college a mataki na grade ll teacher.
Malam ya kwashe shekaru bakwai (7) yana karantarwa, daganan yasamu cigaba zuwa Jami’ar Musulunci ta Madina a shekarar 1997, sakamakon jinya da yayi wadda tayi sanadiyyar jinkirin zuwa, hakan yasa hukumar Makarantar ta ajiyeshi a Matakin ‘Shu’ubah’ (remedial) inda yayi shekara daya daganan yasoma karatun shi a fannin ‘Shari’a law’ da harshen larabci anan ma malam yayi shekaru hudu (4). Kammalawar shi keda wuya, sai malam yanemi damar cigaba da karatun shi na ‘Masters degree’ a Fannin Uslul Fiqihi. A jarabawar da suka rubuta, malam ne yazo na daya a cikin daliban da suka zo daga Nigeria a shekarar 2002, amma bai samu damar fara karatu a wannan shekarar ba sabo da mutum biyu (2) kacal aka dauka a cikin mutane 27 da sukaci jarabawar daga kasashe daban – daban.
Daganan malam yadawo gida Nigeria inda yafara karatun National Diploma a makarantar El kanemi Collage dake Maiduguri a fannain ‘Shari’a’ a shekarar 2003. A shekarar 2004 kuma, malam ya garzaya Jami’ar JOS inda yayi karatun shi na Masters a fannin larabci, kuma yayi nasarar kammalawa a shekarar 2006. A shekarar 2015, malam ya fara PhD a fannin larabci a Jami’ar Jahar Nasarawa (Nasarawa State University) inda ya kammala a shekarar 2017.
SASHIN AIYUKA.
* Malam ya taba zama grade ll teacher a shekarar 1990 – 1997
* Limancin Sallolin Juma’a da na Idi na tsawon shekaru 25
* Malam yayi aiki a matsayin Director Shari’a, a ministry of religions affairs Borno State. 2005 har zuwa rasuwarsa
* A mataki na kungiya kuma, Malam shine shugaban Majalisar Malamai na farko a mataki na MMC, sannan shugaban majalisar malamai na jahar Borno. Saboda himmar sa kan lamarin addini, Sheikh Ali Mustafa an zabe shi member na majalisar koli ta kasa shekaru da dama kafin Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya nadashi matsayin babban Sakataren Majalisar Malamai na kungiyar ta kasa bayan rasuwar Sheikh Dr. Al Hassan Sa’id Jos.
Sheikh Ali Mustafa ya bar mata daya da ‘ya’ya 15 a Duniya.
Sheikh Ali Mustafa mutum ne da aka sanshi da cika alkawari, kyautatawa, da rikon amana.
Muna fata Allah ya jikan sa da rahama kuma jannatul fir-dausi ya zama Shine makomarsa.
Jibwis Borno State,
23/05/2019

Advertisements

Published by Abubakar Nuhu Yahya Koso

NAME: Abubakar Nuhu Yahya Koso. DATE OF BIRTH: 09-07-1997. SCHOOL: Madarasatul Shababul Islam Koso, Gss Doguwa. IDENTITY: Islam. PURPOSE: Peace. MY LORD: ALLAH. MY ROLE MODEL: Rasulullah. MY GUIDE : Al-Qur'an. MY LIGHT: Hadith. REAL SUBJECT: Tauheed. MY PRACTICE: Sunnah. MY AIM: Jannatul Firdaus. MY MISSION: Da'awatu ilallah MY WEAPON: Du'a. MY LAW: Shari'ah. TOWN & VILLAGE: Koso, Kaduna, Nigeria. NATIONALITY: Nigeria. CONTACT ADRESS: Koso, Kaduna, Nigeria. CONTACT NUMBER: 08025298937, 08023140157. EMAIL ADDRESS: Abbakarnuhks@gmail.com, Ibnnuhks@yahoo.com NICKNAME: IbnNuhAssunnee. ALKUNYA: Abu Abdullah. AQEEDAH: Alkitab was sunnah, Ahlus-sunnah wal jama'ah min Fahmi salafus salih. MY RELIGION ORGANISATIONS: Jama'atu-Izalatil-Bid'ah Wa-Ikamatis-Sunnah MY HOBBIES: Reading & Writing MY FAVOURITE SCHOLARS: 01, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe Hafizahullah 02, Shiekh Imam Abdullahi Bala Lau Hafizahullah 03, Sheikh Dr.Isah Aliyu Ibrahim Pantami Hafizahullah.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: