BA DUKKAN HADITHAI BA NE IMAM MALIK YA SANI, WANNAN KUMA BA AIBI BA NE:


BA DUKKAN HADITHAI BA NE IMAM MALIK YA SANI, WANNAN KUMA BA AIBI BA NE:

image

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

1. Ba dukkan hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah ba ne Babban Malamin Hadithi da Fiqhu Imam Malik ya sani, a’a ya dai san mafi yawansu amma kuma bai san dukkansu ba, wannan kuma ita ce siffar dukkan wani malami cikin wannan Al’ummah tun daga zamanin Sahabbai har zuwa karshen Duniya.

2. Lalle a cikin hanyoyin da ‘yan bidi’ah ke bi domin neman raba mutane da bin sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah a cikin mas’alolin Aqeedah, da Ibadah, da Mu’amalah akwai nuna musu cewa: Wannan hadithin Sahabi wane bai yi aiki da shi ba, ko Taabi’iy wane bai yi aiki da shi ba, ko Taabi’ut Taabi’iy wane bai yi aiki da shi ba, ko Imam Abu Hanifah bai yi aiki da shi ba, ko Imam Malik bai yi aiki da shi ba, ko Imamush Shaafi’iy bai yi aiki da shi ba, ko Imam Ahmad bai yi aiki da shi ba, ko Waliyyi Shehu wane bai yi aiki da shi ba, ko uban tafiya Malam wane bai yi aiki da shi ba; saboda haka lalle da yin aiki da shi wannan hadithin ya halatta to da kuwa ba a sami wani daga cikin irin wadannan manyan mutane da zai yi watsi da shi ya kuma ki yin aiki da shi ba!!

3. A nan ga shaidar cewa: a cikin almajiran Imam Malik ma akwai wanda ya san hadithin da shi Imam Malik bai sani ba, kuma wannan ba nakasa ba ce ga shi Imam Malik din, a’a abu ne da ke kara fito da irin mutuntakarsa:-
Baihaqiy ya ruwaito hadithi na 364 daga Ahmad Bin Abdirrahman Bin Wahb ya ce:-
((سمعت عمي يقول: سمعت مالكا يسال عن تخليل اصابع الرجلين في الوضوء فقال: ليس ذلك على الناس.  فتركته حتى خف الناس فقلت له: يا ابا عبد الله سمعتك تفتي في مسالة في تخليل اصابع الرجلين زعمت ان ليس ذلك على الناس؛ وعندنا في سنة. فقال: فقال: وما هي؟ فقلت: حدثنا الليث بن سعد، وابن لهيعة، وعمرو بن الحارث عن يزيد بن عمرو المعافري، عن ابي عبد الرحمن الحبلي عن المستورد بن شداد القرشي قال: رايت رسول الله صلى الله عليه وسلم يدلك بخنصره ما بين اصابع رجليه. فقال: ان هذا حديث حسن، وما سمعت به قط الا الساعة. ثم سمعته يسال بعد ذلك فامر بتخليل الاصابع)).
Ma’ana: ((Na ji baffana yana cewa: na ji Malik ana tambayar shi game da tsettsefe yatsun kafa cikin alwala, sai ya ce: ba wajibi ba ne a kan mutane. Sai na bar shi har mutane suka ragu, sannan na ce: Abu Abdillah, na ji ka kana ba da fatawa game da wata mas’alah, game da tsefe yatsun kafa, ka riya cewa hakan ba wajibi ba ne a kan mutane, lalle mu muna da sunnah. Sai ya ce: wace ce? Sai na ce: Laith Bin Sa’ad, da Ibnu Luhai’ah, da Amr Bin Haarith sun gaya mana daga Yazid Bin Amr Al-Ma’aafiriy, daga Abu Abdurrahman Al-Hubuliy, daga Mustaurid Bin Shaddad Al-Qurashiy ya ce: Na ga Manzon Allah mai tsira da amincin Allah yana goge tsakanin yatsun kafarsa da karamar yatsarsa”. Sai ya ce: Lalle wannan hadithi mai kyau ne, amma ban taba jin shi ba sai wannan lokacin. Daga bayan wannan sai na ji ana tambayar shi kuma yana ba da umurni da goge yatsu)).

4. Ga shi dai karara wannan mas’ala ce muhimmiya daga cikin mas’alolin da suka shafi alwala kuma wacce Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi umurni da ita cikin ingantaccen hadithi amma kuma ga shi Imam Malik bai san hadithin ba, wannan ma shi ne ya sa ya yi fatawa da sabanin abin da Annabi ya yi umurni da shi, to amma alhamdu lillahi almajirinsa Abdullahi Bin Whab ya koyi hadithin daga waninsa, da kuma ya gaya masa nan da nan ya bar ra’ayinsa da ijtihadinsa ya koma a kan abin da Annabi ya yi umurni da shi. Madalla da wannan hali na Imam Malik, saboda wannan abin da ya yin shi ne dukkan ahlussunnah na gaskiya ke yi, babu wadanda ke taka ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah su bi ra’ayoyinsu ko ra’ayoyin malamansu sai ‘yan bidi’ah wadanda ba sa ganin kimar hadithan manzon Allah mai tsira da amincin Allah.
Allah Ya taimake mu har kullum. Ameen.

Advertisements

Published by Abubakar Nuhu Yahya Koso

NAME: Abubakar Nuhu Yahya Koso. DATE OF BIRTH: 09-07-1997. SCHOOL: Madarasatul Shababul Islam Koso, Gss Doguwa. IDENTITY: Islam. PURPOSE: Peace. MY LORD: ALLAH. MY ROLE MODEL: Rasulullah. MY GUIDE : Al-Qur'an. MY LIGHT: Hadith. REAL SUBJECT: Tauheed. MY PRACTICE: Sunnah. MY AIM: Jannatul Firdaus. MY MISSION: Da'awatu ilallah MY WEAPON: Du'a. MY LAW: Shari'ah. TOWN & VILLAGE: Koso, Kaduna, Nigeria. NATIONALITY: Nigeria. CONTACT ADRESS: Koso, Kaduna, Nigeria. CONTACT NUMBER: 08025298937, 08023140157. EMAIL ADDRESS: Abbakarnuhks@gmail.com, Ibnnuhks@yahoo.com NICKNAME: IbnNuhAssunnee. ALKUNYA: Abu Abdullah. AQEEDAH: Alkitab was sunnah, Ahlus-sunnah wal jama'ah min Fahmi salafus salih. MY RELIGION ORGANISATIONS: Jama'atu-Izalatil-Bid'ah Wa-Ikamatis-Sunnah MY HOBBIES: Reading & Writing MY FAVOURITE SCHOLARS: 01, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe Hafizahullah 02, Shiekh Imam Abdullahi Bala Lau Hafizahullah 03, Sheikh Dr.Isah Aliyu Ibrahim Pantami Hafizahullah.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: