“Kungiyar IZALA bata da alaka ko wace iri da wata kungiyar asiri, darika ko kuma kungiyar #Siyasa.”

Tunatarwa!
“Kungiyar IZALA bata da alaka ko wace iri
da wata kungiyar asiri, darika ko kuma
kungiyar #Siyasa.” “Kungiyar tana kan tafarkin musulunci ne
wanda ta dogara ga Qur’ani da hadisan
Annabi Muhammad (SAW) Bisa fassarar
Magabata.” Mun tsakuro wannan babin
ne daga kundin tsari na kungiya wanda
Shugabanni da Malaman Kungiyar a farkon tafiya suka hadu suka rubuta shi.
Dan Haka Malamai a guji Siyasa da
ambatan ‘yan siyasa akan mumbarin
Izala, Hakan sauka ne daga Manufar
kafa kungiyar kuma zunzurutun cin
amanar kungiyar ce. …..In kunne yaji, jiki ya tsira.

Advertisements

*ZAN IYA FASA ABIN DA NA YI NIYYA A ZUCIYATA ?*

*ZAN IYA FASA ABIN DA NA YI NIYYA A
ZUCIYATA ?*
*Tambya Assalamu alaikum Malam, barka da
kokari tare da fatan Allah Ya saka da
alheri. Mutum ne abokin shi ya tambaye
sa bashi, shi kuma sai ya bashi amma a
zuciyar shi sai ya raya kyauta ya bashi.
bayan abokin ya samu sai ya dawo mashi da kudin shi kuma kawai sai ya karba
kayan shi. Malam Ya matsayin kudin a
wurin sa ?
*Amsa:*
Wa alaikum assalamTo dan’uwa tun da
riyawa ka yi a zuciya, ba ka furta ba, to hukuncin bai hau ba, kuma ba ka da laifi
in ka fasa, Annabi S.a.w. yana cewa :
“Allah ya daukewa Al’umata abin da suka
riya a zuciyar şu, mutukar ba su furta ba”
Bukhari hadisi mai lamba ta: 4869.
Saidai yana da kyau ka Sani cewa : duk lokaçın da za ka yi kyauta to Sheidan zai
dinga nuno maka talauci, duk wanda ya
bayar da wani abu saboda Allah, tabbas
Ubangiji zai mayar masa da ninkin-ba-
ninki, kamar yadda hakan ya tabbata a
ayoyi da yawa a cikin alqu’ani mai girma. Allah ne mafi sani.
*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
8/1/2016.
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

*SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN ALBASHI ?*

*SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN
ALBASHI ?*
*Tambaya*
Assalamu alaikum
Malam yaya zakkar ma’aikaci ya kamata
ta zamo? Domin wasu ma’aikatu sukan bada alawus a dunkule wanda ya isa
zakkah to amma wasu sukanyi gini ko
sayen filaye ko gonaki da kudin kafin
shekara ta zagayo sun kare
*Amsa*
Waalaikumussalam To dan’uwa, hukuncin wannan albashi
zai fara ne daga lokacin da ya shiga
mulkinsa, don haka mutukar ba su
shekara ba, to babu zakka a ciki, domin
ba kawai samun nisabI ne ya ke wajabta
zakka ba, dole sai an samu zagayowar shekara daga lokacin da kudin su ka
shiga mulkinsa, don haka duk albashin
da ya kai nisabin zakka, kuma aka ajjiye
shi ya shekara to ya wajaba a fitar masa
da zakka, amma mutukar shekara ba ta
zagayo masa ba, to zakka ba ta wajaba ba akan wanda ya mallake shi.
saidai yana daga cikin dabarun da sharia
ta haramta, mutum ya yi abin da zai
sarayar masa da wajibi da gangan, don
haka mutukar ya sayi filayan ne da nufin
kaucewa fitar da zakka, to tabbas ya sabawa Allah.
Allah ne ma fi sani
*Dr. Jameel Zarewa*
13/3/2014

Riba Goma sha Biyu (12) ga Auren Mace ‘Yar Izala!!!

Riba Goma sha Biyu (12) ga Auren Mace
‘Yar
Izala!!!
(1) In kana son zaman lafiya a gidan ka!
Auro ‘Yar Izala.
(2)Ilimi a gidanka! Auro ‘Yar Izala. (3)Tsoron Allah a gidan ka! Auro ‘Yar
Izala.
(4)Babu bin Malamai da Bokaye a gidan
ka!
Auro ‘Yar Izala.
(5)Ba Guru ba Laya a cikin Kitso! Auro ‘Yar
Izala.
(6)Kamala babu fidda tsiraici! Auro ‘Yar
Izala.
(7)Tarbiyan Yara! Auro ‘Yar Izala.
(8)Tsabta a gidanka! Auro ‘Yar Izala. (9)Wallahi sanin Darajar Iyayen ka! Auro
‘Yar
Izala.
(10)Jin Tausayin ka! Auro ‘Yar Izala.
(11)Tawakkali akwai da babu! Auro ‘Yar
Izala. (12)Amanar Aure! Auro ‘Yar Izala.
Kai abin yaimin dadi ya Allah ka Qara
Daukaka Sunnah da Jama,ar da suke
cikinta
da magoya bayanta a duk inda suke

NISABIN ZAKKAR KUDI DR. JAMILU YUSUF ZAREW

NISABIN ZAKKAR KUDI !
Tambaya : Malam donAllah
nawa ne nisabin zakka a
yanzu ?, saboda ina da wasu ‘yan kudade ne na
ke so na sani, ko akwai hakkin Allah a cikin su,
Allah ya kara maka albarka a rayuwarka.
Amsa : To dan’uwa amsa wannan tambayar yana da
mutukar wahala, saboda ya dogara ne da
sanin kudin gram din gwal a kasuwa, ko
kuma na azurfa, domin yana daga cikin kuskure
rubuta nisabi daya tal ga zakka, har zuwa
tsawon shekara guda, kamar yadda wasu suke
yi a calendar, saboda gwal yana tashi a
kasuwa yana kuma sauka . Wannan ya sa na yi
tattaki zuwa kasuwar masu saida gwal a
Madina ranar talata : 2/12/2014 , in da na samu
cewa har zuwa ranar ana saida kowanne gram
daya na gwal din da ba’a sana’anta shi ba akan
kwatankwacin naira : 5969, kamar yadda muka
sani gram 85, shi ne nisabin zakka, don haka,
in muka buga wancan adadin sau 85 , zai ba
mu : dubu dari biyar da bakwai da dari uku da
sittin da biyar (507365). Wannan shi ne nisabin
zakka, har zuwa tarihin da na rubuta a
sama, idan har kudinka sun kai wannan adadi,
kuma shekara guda ta zagayo musu, to zakka
ta wajaba a cikinsu, za ka raba gida arba’in
ka bayar da kashi daya . Allah ne mafi sani

TSOTSON FARJIN MACE YAYIN SADUWA ! ! DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

TSOTSON FARJIN MACE
YAYIN SADUWA ! !Tambaya :
Assalamu alaikum, M. Na
kasance ina tsotsan azzakarin mijina, shi
kuma yana wasa da gabana da harshensa
kafin mu sadu, ina matsayin haka a addinin
musulunci. Amsa : To ‘yar’uwa hakan ya halatta, ba
matsala a sharian ce, saidai ya wajaba a
tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin
mata, saboda a bude yake, sannan kuma wuri
ne da ake yin haila, ake kuma zuba maniyyi,
ga shi kuma yana kusa da wajan yin bahaya, wasu
masana likitanci suna bada shawarar
cewa : a dinga wanke wurin da gishiri kafin a
tsotsa, saboda neman kariya Allah madaukakin
sarki a cikin suratul Bakara aya ta : 223, ya
kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan sai
ya nuna dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji
dadi da su, in ban da cikin dubura wacce nassi
ya togace. Duba : Mawahibul-jalil 3\406
Allah ne mafi sani.

YADDA AKE WARWARE SIHIRI

YADDA AKE WARWARE
SIHIRI Tambaya :Assalamu
alaikum Dan Allah malam a fitar
dani cikin duhu game da abin da yake
damuna Mahaifiya ta ce ta je gurin
malami ai mata naganin ciwon mara dz yake
damunta, tace tana da ciki yakai shekara, amma
likitoci sun yi scanning sunce ba komai to sai
malamin ya ce mata asiri aka yi mata, kuma zai
yi mata magani nan take ta haife abinda yake
cikinta amma za ta kawo tunkiya da dubu bakwai,
sai take min magana in kawo kudi a sayi
tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya
malam zuciyata ba ta aminta da malaman ba ne
shi yasa ! Na keso ka bani fatawa shin irin
wannan hanyar ta magani ta halatta a addini? Idan
bata halatta ba wacce hanya zan bi wajen qin
biyan kudin da kuma sanar da ita, saboda ina
da matsala , ta bangaren aqeeda mun
banbanta? Wassalam na gode malam Allah ya qara
basira. Amsa : To ‘yar’uwa tabbas ba a warware
sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware
sihiri ta hanyar ayoyin Alqur’ani, wasu malaman
sun yi bayani cewa : ana iya warware sihiri ta
hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da
Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta : 117 zuwa
ta 122, na suratul A’araf, sai kuma aya ta :
79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da
aya ta : 65-70 a suratu Dhaha, za’a karanta su,
sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya
guda bakwai, sannan ayi wanka da shi .
Amma bai halatta ki taimaka mata ba, wajan bada
wadannan kayan da boka ya nema, saboda ba’a
yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah. Ya
wajaba ki yi mata nasiha cikin hikima, ki
sanar da ita cewa : Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi yana cewa :” “Duk wanda ya
je wajan boka, ya tambaye shi wani abu, Allah
ba zai amshi sallarsa ba, ta kawana arba’in”
kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi mai
lamba ta : 2230. Kin ga in mutum ya mutu a
wadannan kwanaki akwai matsala, musamman ma
tun da akwai hanyar da shari’a ta yarda da ita,
a wani hadisin kuma yana cewa : “Duk wanda
ya je wajan boka ya gaskata abin da ya fada, to
tabbas ya kafurce da abin da annabi Muhammad ya
zo da shi” kamar yadda ya zo a Sunanu-
abi-dawud hadisi mai lamba ta : 3904, kuma Albani
ya inganta shi . INA GANIN DA IRIN
WADANNAN HADISAN ZA KI IYA GANAR DA ITA, TA DAWO
KAN HANYA. Allah ne mafi sani . DR. JAMILU YUSUF ZAREWA