INGANTACCIYAR AKIDA DA KISHIYARTA 001

INGANTACCIYAR AKIDA DA KISHIYARTA
Rubutu Na Farko
.
WALLAFAR
Sheik Abdul’aziz Ibn Abdullah Ibn Bazz Rahimahullah
.
TARJAMAR
Sheik Shu’aib Abubakar Umar
.
MAI RUBUTAWA
Abubakar Nuhu Yahya

.
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Godiya ta Tabbata ga Allah Shi kadai, kuma Tsira da amincin Allah su tabbata ga wanda babu wani annabi bayansa, tare da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka, Yayin da ingantacciyar akida ta kasance itace asalin addinin Musulunci, ta kuma zama itace jigon addini, sai naga cewa abinda yafi, in zabi yin zance a kanta a wannan lakca.
Kuma abune sananne daga dalilan Alkur’ani da Sunnah, cewa duk wasu ayyuka ko zantuka suna ingantuwa ne, kuma su karbu idan sun samo asali daga akida wacce take ingantacciya, idan kuwa akida bata ingantu ba, to duk wasu ayyuka ko zantuka da za’ayi batattune kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce;
[Ma’ida aya ta 5]
Kuma Yace;
[Zumar, aya ta 65]
Ayoyi da suka zo da irin wannan ma’anar sunan da yawa.
Hakika littafin Allah mai bayyanawa da kuma sunnar Manzon Allah Amintacce Tsira da amincin Ubangijinsa su tabbata a gare Shi, sun nuna cewa ita akida ingantacciya ta tattara ne, cikin Imani da Allah, da Mala’ikunsa, da Litattafansa, da ManzanninSa, da ranar lahira, da kuma omani da kaddara Alherinta da sharrinta, Wadannan abubuwa guda shida sune asalin akida ingantacciya, kuma wacce da itace littafin Allah mai girma ya sauka, kuma da itace Allah Ya aiko ManzonSa Muhammad Tsira da amincin Allah Su tabbata a gare shi.
Duk wani abu daya wajaba ayi imani dashi, na al’amuran gaibu, dama duk abubuwan da Allah da Manzonsa Tsira da amincin Allah Su tabbata a gare shi, Suka bada labarinsa, sun samo asaline daga wadannan abubuwa guda shida da aka ambata.

Dalilai da suka zo akan
wadannan ginshikai guda
shida a cikin alkur’an da
sunnah suna da yawa
kwarai da gaske daga
cikin su akwai fadin Allah
tsarkakakke;
ﻟَّﻴْﺲَ ﺍﻟْﺒِﺮَّ ﺃَﻥ ﺗُﻮَﻟُّﻮﺍ ﻭُﺟُﻮﻫَﻜُﻢْ
ﻗِﺒَﻞَ ﺍﻟْﻤَﺸْﺮِﻕِ ﻭَﺍﻟْﻤَﻐْﺮِﺏِ ﻭَﻟَٰﻜِﻦَّ
ﺍﻟْﺒِﺮَّ ﻣَﻦْ ﺁﻣَﻦَ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻟْﺂﺧِﺮِ
ﻭَﺍﻟْﻤَﻠَﺎﺋِﻜَﺔِ ﻭَﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏِ ﻭَﺍﻟﻨَّﺒِﻴِّﻴﻦَ.

[Bakara, aya ta 177]
Da kuma fadinSa Tsarki Ya
Tabbata Gare Shi;
ﺁﻣَﻦَ ﺍﻟﺮَّﺳُﻮﻝُ ﺑِﻤَﺎ ﺃُﻧﺰِﻝَ ﺇِﻟَﻴْﻪِ ﻣِﻦ
ﺭَّﺑِّﻪِ ﻭَﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَ ۚ ﻛُﻞٌّ ﺁﻣَﻦَ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ
ﻭَﻣَﻠَﺎﺋِﻜَﺘِﻪِ ﻭَﻛُﺘُﺒِﻪِ ﻭَﺭُﺳُﻠِﻪِ ﻟَﺎ ﻧُﻔَﺮِّﻕُ
ﺑَﻴْﻦَ ﺃَﺣَﺪٍ ﻣِّﻦ ﺭُّﺳُﻠِﻪِ.
[Bakara,
Aya ta 285]
Da kuma fadinSa Tsarki Ya
Tabbata Gare Shi;
ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺁﻣِﻨُﻮﺍ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ
ﻭَﺭَﺳُﻮﻟِﻪِ ﻭَﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏِ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻧَﺰَّﻝَ ﻋَﻠَﻰٰ
ﺭَﺳُﻮﻟِﻪِ ﻭَﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏِ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺃَﻧﺰَﻝَ ﻣِﻦ
ﻗَﺒْﻞُ ۚ ﻭَﻣَﻦ ﻳَﻜْﻔُﺮْ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻣَﻠَﺎﺋِﻜَﺘِﻪِ
ﻭَﻛُﺘُﺒِﻪِ ﻭَﺭُﺳُﻠِﻪِ ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻟْﺂﺧِﺮِ ﻓَﻘَﺪْ
ﺿَﻞَّ ﺿَﻠَﺎﻟًﺎ ﺑَﻌِﻴﺪًﺍ
[An-Nisa’i,
aya ta 136]
Da kuma fadinSa Tsarki Ya
Tabbata Gare Shi;
ﺃَﻟَﻢْ ﺗَﻌْﻠَﻢْ ﺃَﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻳَﻌْﻠَﻢُ ﻣَﺎ ﻓِﻲ
ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ۗ ﺇِﻥَّ ﺫَٰﻟِﻚَ ﻓِﻲ
ﻛِﺘَﺎﺏٍ ۚ ﺇِﻥَّ ﺫَٰﻟِﻚَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻳَﺴِﻴﺮ
[Al-
Hajj, Aya ta 70]
Dalilai kuma da suka zo a cikin sunnah kan karfafa wadannan ginshikai shida na imani suna da yawa kwarai da gaske, A cikinsu Akwai ingantaccen hadisin nan, kuma mashahuri wanda muslim ya rawaito a cikin sahihinsa, daga hadisin sarkin muminai Umar ibn Khaddab, Allah Ya yarda dashi cewa Jibril, Amincin Allah Ya tabbata a gare Shi, yayi wa Manzon Allah Amincin Allah Ya tabbata a gare Shi Tambaya akan imani sai ya ce;
ﺍﻟْﺈِﻳﻤَﺎﻥِ ﺃَﻥْ ﺗُﺆْﻣِﻦَ ﺑِﺎَﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻣَﻠَﺎﺋِﻜَﺘِﻪِ ﻭَﻛُﺘُﺒِﻪِ ﻭَﺭُﺳُﻠِﻪِ ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻟْﺂﺧِﺮِ، ﻭَﺗُﺆْﻣِﻦَ ﺑِﺎﻟْﻘَﺪَﺭِ ﺧَﻴْﺮِﻩِ ﻭَﺷَﺮِّﻩِ

Wadannan ginshi kai guda Shida daga gare su ne duk wani abu daya zama wajibi musulmi yayi imani da shi ya fito, na gane da hakkin Allah Tsarkakakke, da kuma lamarin da ya shafi lahira da sauran al’amura na gaibi.
*Mu hadu a rubutu na gaba, zamu ji inda malam yayi bayani akan IMANI DA ALLAH TSARKAKAKKE*
.
Abubakar Nuhu Yahya
Tweet@#IbnNuhAssunnee
10-06-1438
09-03-2017

Advertisements