MUHADARORI/WA’AZI DARI (100) NA SHEIKH KABIR GOMBE

MUHADARORI/WA’AZI DARI (100) NA SHEIKH KABIR GOMBE

Wadannan Kadan Ne Daga Cikin Wa’azuzzuka Da Babban Sakataren ‘Kungiyar Jama’atu-Izalatil-Bid’ah- Wa-Ikamatis-Sunnah Na Kasa Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe Hafizahullah Ya Gabatar, Wadanda Cibiyar Yada Sunnah Ta DARULFIKR Ta Dora, Kuma Admins Na Dandalin Masoya Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe Hafizahullah #ISupportSheikKabirGombe Suka Tattara Domin Ku Sami Saukin Saukewa.

000 Yi Like Din Shafin Mu A Facebook
http://facebook.com/ISupportSheikKabirGombe
001 Kula Da Sallah
http://darulfikr.com/s/21704
002 Kyautatawa a Musulunci
http://darulfikr.com/s/22411
003 Matasa Mu Tashi Mu Nema Ilimi
http://darulfikr.com/s/22414
004 Matan Aljannah A Duniya
http://darulfikr.com/s/22415
005 Tausayin Yara Mata akan Iyayensu
http://darulfikr.com/s/22523
006 Ta’aziyan Alhaji Ahmadu Chanchangi
http://darulfikr.com/s/22522
007 Kabari Aya ne A Garemu
http://darulfikr.com/s/22520
008 BANBAMCI TSAKANIN GWAURO DA MAI AURE
http://darulfikr.com/s/7431
009 Duniya Budurwar Wawa
http://darulfikr.com/s/10159
010 MATASA KASHIN BAYAN RAYA SUNNAH
http://darulfikr.com/s/21151
011 Muhimmancin Gudunmawa a Musulunci
http://darulfikr.com/s/10285
012 Rashin godiyar Allan mu game da BUHARIYYAH
http://darulfikr.com/s/8869
013 Saki kowa ka kama Allah
http://darulfikr.com/s/20022
014 Son Zuciya ubangiji ne da wasu ke bautawa
http://darulfikr.com/s/10113
015 Sunnah in Bakayi Bani Guri
http://darulfikr.com/s/9209
016 Waye Masoyin Annabi
http://darulfikr.com/s/10392
017 Ayatullahi Buratai
http://darulfikr.com/s/4106
018 Garin Neman Gira An Rasa Ido
http://darulfikr.com/s/2912
018 Rayuwa Adam Acikin Duniya
http://darulfikr.com/s/5093
019 Wasika Zuwaga Mawadata
http://darulfikr.com/s/3027
020 Ladubban Tarewa A Sabon Gida
http://darulfikr.com/s/3016
021 Tonon Silili Da Tufin Allah Tsine
http://darulfikr.com/s/4144
022 Anyi walkiya mun gansu
http://darulfikr.com/s/1309
023 DAN KASA NAGARI
http://darulfikr.com/s/18314
024 IKLar Shaye-Shaye
http://darulfikr.com/s/927
025 Riba da illolinta
http://darulfikr.com/s/929
026 Gyara kayan ba zai zamo sauke mu raba ba
027 http://darulfikr.com/s/3586
028 Ihidinas Siradal Musataeem
http://darulfikr.com/s/5413
029 BIDI’AR MAULIDI
030 http://darulfikr.com/s/935
031 Kowanne tsintsu kukan gidan su yake
http://darulfikr.com/s/5252
032 Majlisin Malamai
http://darulfikr.com/s/4401
033 Makircin Shi’a
http://darulfikr.com/s/2432
034 Nigeria ta fara hayaki
http://darulfikr.com/s/942
035
Ribar kafa
http://darulfikr.com/s/9092
036 ILLAR ZINA
http://darulfikr.com/s/939
037 Shirin Fatawa na Kada Fm
http://darulfikr.com/s/6854
038 ILLOLIN JAHILCI
http://darulfikr.com/s/944
039 SADA ZUMINCI
http://darulfikr.com/s/946
040 MADINAR GAUSI
http://darulfikr.com/s/949
041 MALAMN BIDIA DILALA SHARI
http://darulfikr.com/s/945
042 MATAN ANNABI SAW
http://darulfikr.com/s/947
043 MATAN ANNABI SAW 2
044 http://darulfikr.com/s/948
045 MUMMUNAR CIKAWA
http://darulfikr.com/s/950
046 SUNNA SAK BIDI’A SAM
http://darulfikr.com/s/952
047
HUKUNCHIN KALLO
http://darulfikr.com/s/951
048 KO KINKI KO KINSO
http://darulfikr.com/s/953
049 WEYE MAI SALLAH
http://darulfikr.com/s/955
050 YAN SHI’A
http://darulfikr.com/s/956
051 WA’AZIN KANGIWA
http://darulfikr.com/s/18197
052 WA’AZIN GARIN LARABAR ABASAWA
http://darulfikr.com/s/17975
053 WA’AZIN MATA NA DORAYI
http://darulfikr.com/s/17976
054 Wa’azin Mata Sumaila
http://darulfikr.com/s/17972
055 Wa’azin Lagos 01
http://darulfikr.com/s/9112
056 Wa’azin Lagos
http://darulfikr.com/s/7434
Waazin zamfarah
ttp://darulfikr.com/s/8764
057 Wa’azin Miya
http://darulfikr.com/s/5519
058 Wa’azin Owode Ogun
http://darulfikr.com/s/19055
059 Wa’azin sokoto 1
http://darulfikr.com/s/930
060 Wa’zin Sokoto 2
http://darulfikr.com/s/931
061 Wa’zin Sokoto 3
http://darulfikr.com/s/933
062 Wa’azin Mata Zamfarah
ttp://darulfikr.com/s/932
063 Wa’azin Suleja
http://darulfikr.com/s/934
064 Wa’azin Kankiya
http://darulfikr.com/s/3393
065 Wa’azin Yantumaki
http://darulfikr.com/s/937
066 Wa’azin Billiri
http://darulfikr.com/s/5258
067 Wa’azin Bolari
http://darulfikr.com/s/5252
068 Wa’azin Yola
http://darulfikr.com/s/957
069 Wa’azin Jalingo
http://darulfikr.com/s/20862
070 Wa’azin,Accra Ghana
http://darulfikr.com/s/9092
071 Wa’azin Niger
http://darulfikr.com/s/940
072 Wa’azin Illela
http://darulfikr.com/s/943
073 Wa’azin Pandogari 1
http://darulfikr.com/s/954
074 Wa’azin Pandogari 2
http://darulfikr.com/s/936
075 Wa’azin Sumaila Kano
http://darulfikr.com/s/17973
076 Wa’azin Agege Lagos
http://darulfikr.com/s/18503
077 Wa’azin Jahar Kano
http://darulfikr.com/s/13102
078 Wa’azin Bauchi
http://darulfikr.com/s/4203
079 Wa’azin Jihar Kano 5
http://darulfikr.com/s/1369
080 Wa’azin Liman Katagun Bauchi
http://darulfikr.com/s/4204
081 Waazin Mata Taraba
http://darulfikr.com/s/19931
082 Wa’azin Maza Ogere
http://darulfikr.com/s/19059
083 Wa’azin Mata Owode Ogun
http://darulfikr.com/s/19058
084 Wa’azin Maza Owode Ogun
http://darulfikr.com/s/19057
085 Wa’azin Mata Ogere
http://darulfikr.com/s/19074
086 Wa’azin Shagamu Ogun
http://darulfikr.com/s/19060
087 Alaba Rago Lagos
http://darulfikr.com/s/19075
088 Wa’azin Zaria
https://kiwi6.com/file/494p6nu72v
089 Wa’azin Yola 2
https://kiwi6.com/file/mritel0tu0
090 Wa’azin Kumo
https://kiwi6.com/file/xwu3stijrf
091 Wa’azin Lagos 2014
https://kiwi6.com/file/zo52lzbay2
092 Wa’azi Funtua
https://kiwi6.com/file/fh6j8e6e0v
092 Wa’azin Gamahttps://kiwi6.com/file/0ptyt0vi2m
093 Wa’azin Suleja 2
https://kiwi6.com/file/st2bmi55wv
094 Wa’azin Tsafe
https://kiwi6.com/file/1ygupz01fh
095 Wa’azin Dan Sadau
https://kiwi6.com/file/kfnr1bkenv
096 Wa’azin Ikara
https://kiwi6.com/file/71ngomy2zu
097 Wa’azin Madobi
https://kiwi6.com/file/56555ivywk
098 Wa’azin Rano
https://kiwi6.com/file/kmyjhjzx15
099 Wa’azin Jos
https://kiwi6.com/file/r8ghnl8jvu
100 Wa’azin Kaduna City
https://kiwi6.com/file/lhejc4i4nq
Kuci Gaba Da Kasancewa Damu Domin Samun Links Da Zaku Sauke Karatukan Malam Da Sauran Malaman Sunnah.
dannan Link Din Dake Kasa Kayi Like Na Shafin Mu.
http://www.facebook.com/ISupportSheikKabirGombe

Advertisements

Sunayen Ahalus Sunna A Wajen ‘Yan Shi’a – Matsayin Musulmi a wajen ‘Yan Shi’a Dr. Umar Labdo

Babi Na daya
Ma’anar Ahalus Sunna A
Wajen Rafilawa
Mai karatun littafan Shi’a
zai lura da wasu sunaye,
ko kuma laqabai, da suke
kiran Ahalus Sunna da su.
Wadannan lakabai suna
cikin littafan malamansu
na farko da malamansu na
zamani. Ba safai sukan kira
su da sunan Ahalus Sunna
ba sai nadiran. Sunayen
dukkaninsu suna nuna
kazafi da vatanci da
wulakanci. Zai yi kyau mu
fara bayani da wadannan
sunaye kafin mu shiga
magana a kan ma’anar
Ahalus Sunna a wajen
Rafilawa.
Sunayen Ahalus Sunna A
Wajen ‘Yan Shi’a
Akwai sunaye guda uku da
Rafilawa suke amfani da
su don ambaton Ahalus
Sunna a cikin littafansu da
maganganunsu wadanda
suka hada da
hudubobinsu da laccocinsu
da wa’azozinsu.
Wadannan su ne:
1. Nasibawa. Asalin sunan
da Larabci nasib, jam’insa
nawasib, watau mai kulla
gaba, ko wanda ya kafa
kiyayya. Abinda suke nufi
gaba da kiyayya ga Ahalul
Baiti, musamman Ali binu
Abi Dalib da Fadima, Allah
ya kara musu yarda, da
kuma imamai goma sha
biyu daga zuri’arsu.
Wannan suna shi ne mafi
muni kuma mafi yaduwa a
tsakaninsu wanda suke
ambaton Ahalus Sunna da
shi.
Malaminsu mai suna
Hussain Aali Usfur
Addarazi Albahrani, yana
cewa, “Al’ada ta gudana,
kai har ma da hadisan
imamai, a kan cewa nasibi
shi ne wanda a wajensu
suke kira Sunni.”[1]
A wajensu, yana nufin a
wajen Ahalus Sunna.
Amma su a nasu wajen
nasibawa suke ce da su.
Dubi yadda ya yi nuni ga
Ahalus Sunna da lamirin
“su” domin ya bambance
su da “mu” wanda a
zancensa yake nufin ‘yan
Shi’a. Wannan kawai ya isa
ya nunawa mai karatu
yadda dan Shi’a yake
daukar kansa da Ahalus
Sunna; watau abin mu ne
da su.
Malamin Shi’a na wannan
zamani wanda ya shahara
da tsaurin kai, Muhammad
Tijjani Samawi, yana cewa,
“Abu ne da ba ya bukatar
a fadi cewa mazhabin
nasibawa shi ne mazhabin
Ahalus Sunna wal
Jama’a.”[2] Haka yake
kamar yadda malamin ya
fadi. Wannan abu ba ya
bukatar a fadi saboda ya
shahara a tsakanin
Rafilawa kuma a cikinsu
babu mai ja a kai.
2. Amawa. Wannan shi ne
suna na biyu da Rafilawa
ke kiran Ahalus Sunna da
shi. Asalinsa da Larabci
aami, jam’insa awaam,
watau gama-gari, ko
tarkacen mutane. Kuma
sunan kishiyar lafazin
khaas ne (jam’insa
khawaas), wanda yake
nufin na musamman, ko
na-gari. Watau ‘yan Shi’a
su ne na musamman,
masu nagarta, Ahalus
Sunna kuwa tarkace,
gama-gari. Daga cikin
malaman Shi’a da suka yi
amfani da wannan suna
akwai Alhurrul Amili
wanda ya rubuta wani
babi mai taken “Babin
Hani Ga Barin Riko Da
Abinda Ya Dace Da
Amawa” a cikin littafinsa
mai suna Alfusulul
Muhimma. A qarqashin
wannan babin, ya ruwaito
imaminsu na shida, Ja’afar
Sadik, yana cewa idan aka
samu hadisai guda biyu
masu karo da juna, to a
dauki wanda ya saba wa
ra’ayin Amawa, a kyale
wanda ya dace da su.[3]
3. Suna na uku shi ne
Jumhur. Wannan suna
haka yake ko a Larabci,
kuma ba shi da tilo sai
jam’i kawai. Ma’anarsa ta
yi kama da gama-gari
koda yake a wani yayi
yana nufin agalabiya,
watau mafiya yawa, masu
rinjaye, ko kuma majorati,
kamar yadda ake fadi da
kalmar Turanci ta aro.[4]
Wadannan sunaye su ne
‘yan Shi’a suke amfani da
su wajen ambaton Ahalus
Sunna a cikin littafansu,
maganganunsu, laccocinsu
da hudubobinsu. Kuma
ma’anarsu a fili take; suna
nuna yadda ‘yan Shi’a suka
dauki masu bin tafarkin
Sunna a matsayin abokan
gaba masu kiyayya ga
imamai, bare waxanda ba
na gida ba, kuma koma-
baya wadanda suke
gama-gari ne su, tarkace.
Banda wadannan sunaye,
akwai wasu lafuza da
malaman Shi’a ke amfani
da su domin nuni ga duk
wani Musulmi wanda ba
ya bin tafarkinsu, wanda
yana iya hadawa da
Ahalus Sunna da wasunsu.
Waxannan sun haxa da
almukhalif, watau mai
saba mana, da gairuna,
watau waninmu, da
munafiq, watau munafiki,
da sauransu.
Ma’anar Ahalus Sunna A
Wajen ‘Yan Shi’a
Amma idan muka koma
ga haqiqanin ma’anar
Ahalus Sunna a wajen ‘yan
Shi’a, to sai mu ga cewa
sun gina ta a kan
abubuwa uku.
1. Abu na farko: Fifita
wanin Ali binu Abi Dalib
(RA) a kansa. Dangane da
wannan ma’ana ne
malaminsu dan hayaki,
Ni’imatullahi Aljaza’iri,
yake fadin wai, “An
ruwaito daga Annabi(SAW)
cewa alamar nasibawa ita
ce gabatar da wanin Ali a
kansa.”[5] Watau wanda
ya ce wani Sahabi ya fi Ali,
ko yana gaba da shi a
wajen daraja da falala, ko
shi ne Khalifa na farko ba
Ali ba, to wannan ya zama
nasibi. Babu shakka Ahalus
Sunna suna ganin cewa
Abubakar da Umar da
Usman suna gaba da Ali a
wajen falala da fifiko da
kuma jerin khalifanci.[6]
Kai a cikin kungiyoyin
Musulunci ma kaf, ba mai
fifita Ali a kan Abubakar da
Umar sai ‘yan Shi’a (koda
yake an samu wasu
wadanda suka fifita shi a
kan Usman). Saboda haka
a kan wannan, duk wanda
ba dan Shi’a ba nasibi ne
ke nan.
2. Abu na biyu: Yarda da
amincewa da khalifancin
Abubakar da Umar, Allah
ya kara musu yarda.[7]
Watau ko da mutum bai
fifita su ba, idan dai ya
yarda da cewa su khalifofi
ne, to ya zama nasibi.
3. Abu na uku: Jibintar
Jibtu da Dagutu, kamar
yadda suke fadi.[8] Abinda
suke nufi da Jibtu da
Dagutu su ne Abubakar da
Umar, Allah ya kara musu
yarda. Watau ba fifita su
ba, ba yarda da
khalifancinsu ba, ko
jibintar su ma kawai,
watau son su da daukar su
a matsayin ‘yan uwa
Musulmi, yana mai da
mutum nasibi.
Yana daga cikin akidun
Rafilawa sanannu cewa
mutum ba ya zama
Musulmi sai ya barranta
daga Abubakar da Umar
da manyan Sahabbai tare
da su, kuma ya barranta
daga duk mai son su, ko
jibintar su. Babban
malaminsu, Muhammad
Bakir Almajalisi, ya
tabbatar da wannan aqida
tasu inda yake cewa,
“Akidarmu ta barranta ita
ce cewa mu muna
barranta daga gumaka
hubu: Abubakar da Umar
da Usmanu da Mu’awiya;
da mataye hudu: A’isha da
Hafsa da Hindu da Ummul
Hakam; kuma muna
barranta daga dukkan
mabiyansu da magoya
bayansu; kuma muna
kudure cewa su ne mafiya
sharrin halittar Allah a
bayan qasa; kuma cewa
imani da Allah da
Manzonsa da imamai ba
ya inganta sai an barranta
daga makiyansu.”[9]
Daga wadannan bayanai
da suka gabata zai
bayyana a fili cewa a
ganin ‘yan Shi’a duk
wanda bai kudure
aqidarsu ba ta cewa Ali
binu Abi Dalib shi da
‘ya’yansa su kadai su ne
khalifofi, ko imamai, kuma
cewa Abubakar da Umar
da Usmanu ba wai kawai
su ba khalifofi ba ne a’a su
kafirai ne gumaka, wanda
duk bai kudure wannan
akida ba to shi ne nasibi
kuma imaninsa da Allah
da Manzo bai inganta ba.
Wannan yana nufi, a
takaice, duk wanda ba dan
Shi’a ba kafiri ne, tun daga
kan Abubakar(RA) har ya
zuwa ga kai mai karatun
wannan littafin, in kai ba
dan Shi’a ba ne.
To jama’a, ina karyar
hadin kai? Ina karyar
takrib da ta’aruf da “Islam
One”? Ina da’awar cewa
Musulmi duka daya ne?
Yaya masu barranta daga
Abubakar da Umar da
Usmanu da A’isha da Hafsa
da mabiyansu da magoya
bayansu za su hada kai da
wani? Shin ana hada kai
da kafiri wanda yake
goyon bayan mafiya
sharrin halittar Allah a
bayan qasa?
Amma ba a nan batun ya
kare ba. Saurari hukuncin
nasibawa waxanda suka
yarda da khalifancin
Abubakar da Umar, suka
fifita su a kan Ali.

Gabatarwa – Matsayin Musulmi a wajen ‘Yan Shi’a Dr. Umar Labdo

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
Gabatarwa
Lallai godiya ta tabbata ga
Allah, muna gode masa,
muna neman taimakonsa,
muna neman gafara tasa.
Muna neman tsari da Allah
daga sharrin kawunanmu
da miyagun ayyukanmu.
Wanda Allah ya shirye shi,
babu mai batar da shi
kuma wanda ya batar
babu mai shiriya tasa. Ina
shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai
Allah, shi kadai, ba shi da
abokin tarayya. Kuma ina
shaidawa cewa
Muhammad bawansa ne,
kuma Ma’aikinsa ne. Tsira
da aminci su tabbata a
gare shi, da Alayensa, da
Sahabbansa, da waxanda
suka bi Sunnarsa har zuwa
ranar sakamako.
Bayan haka, ‘yan Shi’a
suna yawan yin magana
dangane da hadin kan
Musulmi. Ba sa barin wata
munasaba ta wuce ba tare
da sun maimaita kira
izuwa hadin kai ba, da
sukan rarraba da
karkasuwa zuwa
kungiyoyi da mazhabobi.
Sau da yawa sukan yi kira
da hadin kai tsakaninsu da
Ahalus Sunna, suna masu
karfafa cewa bai kamata a
samu sabani ba domin
hakan yana raunana
Musulmi a gaban abokan
gabansu. A wasu lokuta
sukan nuna cewa
abubuwan da suka raba su
da Ahalus Sunna ba wasu
muhimmai ba ne, kuma su
da Ahalus Sunna duka abu
guda ne tunda Shi’a ita ma
mazhaba ce kamar sauran
mazhabobi.
A wasu kasashe, ‘yan Shi’a
suna kira da abinda suke
wa laqabi da Attakrib
bainal Mazahib, ko kuma
Atta’aruf, watau kusantar
da mazhabobi ga junansu
ko kuma fahimtar juna,
suna nufin kusanci da
fahimtar juna tsakanin
tafarkin Shi’a da na Sunna.
A nan Nijeriya kuwa, mun
san su da kirarin Islam
One, wanda suke bin gine-
ginen hukuma kamar
makarantu da ofisoshi
suna rubutawa, wai suna
nufin Musulunci daya ne,
babu bambanci tsakanin
wani tafarki da wani, ko
kuma wata mazhaba da
wata.
Amma mene ne hakikanin
abinda ‘yan Shi’a suka
dauki mai bin tafarkin da
ba nasu ba, musamman
Ahalus Sunna? Shin
gaskiya ne suna daukar
dukkan Musulmi daya ne,
ko kuwa kawai yaudara ce
suke yi don su samu
karbuwa a wajen mutane?
Mene ne abinda manyan
malaman Shi’a suke fadi
dangane da Ahalus Sunna,
da sauran Musulmi duka, a
da da kuma yanzu? Shin
sun yarda su Musulmi ne
kamar yadda su ma suke
da’awar Musulunci, ko
kuwa suna daukar su
dabam? Ya suka dauki
imaninsu da sallarsu da
azuminsu da hajjinsu da
yankansu da auratayyarsu
da sauran ma’amalolinsu
da ayyukansu na addini?
Wannan dan karamin
littafi zai yi kokarin amsa
wadannan tambayoyi, da
ma wasunsu, in Allah ya
yarda, kuma amsoshin
duka za su fito kai tsaye
daga bakin manyan
malaman ‘yan Shi’a, ta
hanyar littafansu waxanda
suka yarda da su. A qarshe
mai karatu zai fita da
sahihiyar fahimta ta
matsayin Ahalus Sunna, da
sauran Musulmi, a wajen
‘yan Shi’a ta yadda zai yi
hukunci da kansa a kan
wannan da’awa ta
Rafilawa ta kira zuwa ga
hadin kai da kusanto da
mazhabobi da fahimtar
juna idan gaskiya ce ko
kuwa qarya ce da yaudara.
Manufarmu a nan, in Allah
ya yarda, ita ce bayanin
gaskiya da sauke nauyin
da yake kanmu na
al’ummarmu, don wanda
ya halaka ya halaka a bisa
sani kuma wanda ya
shiriya ya shiriya a bisa
sani. Kuma gamon
katarinmu bai zamo ba sai
ga Allah, a gare shi muke
dogara, kuma gare shi
muke komawa.
Kano
U. M. Labdo
Oktoba, 2012