MUHADARORI/WA’AZI DARI (100) NA SHEIKH KABIR GOMBE

MUHADARORI/WA’AZI DARI (100) NA SHEIKH KABIR GOMBE

Wadannan Kadan Ne Daga Cikin Wa’azuzzuka Da Babban Sakataren ‘Kungiyar Jama’atu-Izalatil-Bid’ah- Wa-Ikamatis-Sunnah Na Kasa Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe Hafizahullah Ya Gabatar, Wadanda Cibiyar Yada Sunnah Ta DARULFIKR Ta Dora, Kuma Admins Na Dandalin Masoya Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe Hafizahullah #ISupportSheikKabirGombe Suka Tattara Domin Ku Sami Saukin Saukewa.

000 Yi Like Din Shafin Mu A Facebook
http://facebook.com/ISupportSheikKabirGombe
001 Kula Da Sallah
http://darulfikr.com/s/21704
002 Kyautatawa a Musulunci
http://darulfikr.com/s/22411
003 Matasa Mu Tashi Mu Nema Ilimi
http://darulfikr.com/s/22414
004 Matan Aljannah A Duniya
http://darulfikr.com/s/22415
005 Tausayin Yara Mata akan Iyayensu
http://darulfikr.com/s/22523
006 Ta’aziyan Alhaji Ahmadu Chanchangi
http://darulfikr.com/s/22522
007 Kabari Aya ne A Garemu
http://darulfikr.com/s/22520
008 BANBAMCI TSAKANIN GWAURO DA MAI AURE
http://darulfikr.com/s/7431
009 Duniya Budurwar Wawa
http://darulfikr.com/s/10159
010 MATASA KASHIN BAYAN RAYA SUNNAH
http://darulfikr.com/s/21151
011 Muhimmancin Gudunmawa a Musulunci
http://darulfikr.com/s/10285
012 Rashin godiyar Allan mu game da BUHARIYYAH
http://darulfikr.com/s/8869
013 Saki kowa ka kama Allah
http://darulfikr.com/s/20022
014 Son Zuciya ubangiji ne da wasu ke bautawa
http://darulfikr.com/s/10113
015 Sunnah in Bakayi Bani Guri
http://darulfikr.com/s/9209
016 Waye Masoyin Annabi
http://darulfikr.com/s/10392
017 Ayatullahi Buratai
http://darulfikr.com/s/4106
018 Garin Neman Gira An Rasa Ido
http://darulfikr.com/s/2912
018 Rayuwa Adam Acikin Duniya
http://darulfikr.com/s/5093
019 Wasika Zuwaga Mawadata
http://darulfikr.com/s/3027
020 Ladubban Tarewa A Sabon Gida
http://darulfikr.com/s/3016
021 Tonon Silili Da Tufin Allah Tsine
http://darulfikr.com/s/4144
022 Anyi walkiya mun gansu
http://darulfikr.com/s/1309
023 DAN KASA NAGARI
http://darulfikr.com/s/18314
024 IKLar Shaye-Shaye
http://darulfikr.com/s/927
025 Riba da illolinta
http://darulfikr.com/s/929
026 Gyara kayan ba zai zamo sauke mu raba ba
027 http://darulfikr.com/s/3586
028 Ihidinas Siradal Musataeem
http://darulfikr.com/s/5413
029 BIDI’AR MAULIDI
030 http://darulfikr.com/s/935
031 Kowanne tsintsu kukan gidan su yake
http://darulfikr.com/s/5252
032 Majlisin Malamai
http://darulfikr.com/s/4401
033 Makircin Shi’a
http://darulfikr.com/s/2432
034 Nigeria ta fara hayaki
http://darulfikr.com/s/942
035
Ribar kafa
http://darulfikr.com/s/9092
036 ILLAR ZINA
http://darulfikr.com/s/939
037 Shirin Fatawa na Kada Fm
http://darulfikr.com/s/6854
038 ILLOLIN JAHILCI
http://darulfikr.com/s/944
039 SADA ZUMINCI
http://darulfikr.com/s/946
040 MADINAR GAUSI
http://darulfikr.com/s/949
041 MALAMN BIDIA DILALA SHARI
http://darulfikr.com/s/945
042 MATAN ANNABI SAW
http://darulfikr.com/s/947
043 MATAN ANNABI SAW 2
044 http://darulfikr.com/s/948
045 MUMMUNAR CIKAWA
http://darulfikr.com/s/950
046 SUNNA SAK BIDI’A SAM
http://darulfikr.com/s/952
047
HUKUNCHIN KALLO
http://darulfikr.com/s/951
048 KO KINKI KO KINSO
http://darulfikr.com/s/953
049 WEYE MAI SALLAH
http://darulfikr.com/s/955
050 YAN SHI’A
http://darulfikr.com/s/956
051 WA’AZIN KANGIWA
http://darulfikr.com/s/18197
052 WA’AZIN GARIN LARABAR ABASAWA
http://darulfikr.com/s/17975
053 WA’AZIN MATA NA DORAYI
http://darulfikr.com/s/17976
054 Wa’azin Mata Sumaila
http://darulfikr.com/s/17972
055 Wa’azin Lagos 01
http://darulfikr.com/s/9112
056 Wa’azin Lagos
http://darulfikr.com/s/7434
Waazin zamfarah
ttp://darulfikr.com/s/8764
057 Wa’azin Miya
http://darulfikr.com/s/5519
058 Wa’azin Owode Ogun
http://darulfikr.com/s/19055
059 Wa’azin sokoto 1
http://darulfikr.com/s/930
060 Wa’zin Sokoto 2
http://darulfikr.com/s/931
061 Wa’zin Sokoto 3
http://darulfikr.com/s/933
062 Wa’azin Mata Zamfarah
ttp://darulfikr.com/s/932
063 Wa’azin Suleja
http://darulfikr.com/s/934
064 Wa’azin Kankiya
http://darulfikr.com/s/3393
065 Wa’azin Yantumaki
http://darulfikr.com/s/937
066 Wa’azin Billiri
http://darulfikr.com/s/5258
067 Wa’azin Bolari
http://darulfikr.com/s/5252
068 Wa’azin Yola
http://darulfikr.com/s/957
069 Wa’azin Jalingo
http://darulfikr.com/s/20862
070 Wa’azin,Accra Ghana
http://darulfikr.com/s/9092
071 Wa’azin Niger
http://darulfikr.com/s/940
072 Wa’azin Illela
http://darulfikr.com/s/943
073 Wa’azin Pandogari 1
http://darulfikr.com/s/954
074 Wa’azin Pandogari 2
http://darulfikr.com/s/936
075 Wa’azin Sumaila Kano
http://darulfikr.com/s/17973
076 Wa’azin Agege Lagos
http://darulfikr.com/s/18503
077 Wa’azin Jahar Kano
http://darulfikr.com/s/13102
078 Wa’azin Bauchi
http://darulfikr.com/s/4203
079 Wa’azin Jihar Kano 5
http://darulfikr.com/s/1369
080 Wa’azin Liman Katagun Bauchi
http://darulfikr.com/s/4204
081 Waazin Mata Taraba
http://darulfikr.com/s/19931
082 Wa’azin Maza Ogere
http://darulfikr.com/s/19059
083 Wa’azin Mata Owode Ogun
http://darulfikr.com/s/19058
084 Wa’azin Maza Owode Ogun
http://darulfikr.com/s/19057
085 Wa’azin Mata Ogere
http://darulfikr.com/s/19074
086 Wa’azin Shagamu Ogun
http://darulfikr.com/s/19060
087 Alaba Rago Lagos
http://darulfikr.com/s/19075
088 Wa’azin Zaria
https://kiwi6.com/file/494p6nu72v
089 Wa’azin Yola 2
https://kiwi6.com/file/mritel0tu0
090 Wa’azin Kumo
https://kiwi6.com/file/xwu3stijrf
091 Wa’azin Lagos 2014
https://kiwi6.com/file/zo52lzbay2
092 Wa’azi Funtua
https://kiwi6.com/file/fh6j8e6e0v
092 Wa’azin Gamahttps://kiwi6.com/file/0ptyt0vi2m
093 Wa’azin Suleja 2
https://kiwi6.com/file/st2bmi55wv
094 Wa’azin Tsafe
https://kiwi6.com/file/1ygupz01fh
095 Wa’azin Dan Sadau
https://kiwi6.com/file/kfnr1bkenv
096 Wa’azin Ikara
https://kiwi6.com/file/71ngomy2zu
097 Wa’azin Madobi
https://kiwi6.com/file/56555ivywk
098 Wa’azin Rano
https://kiwi6.com/file/kmyjhjzx15
099 Wa’azin Jos
https://kiwi6.com/file/r8ghnl8jvu
100 Wa’azin Kaduna City
https://kiwi6.com/file/lhejc4i4nq
Kuci Gaba Da Kasancewa Damu Domin Samun Links Da Zaku Sauke Karatukan Malam Da Sauran Malaman Sunnah.
dannan Link Din Dake Kasa Kayi Like Na Shafin Mu.
http://www.facebook.com/ISupportSheikKabirGombe

Advertisements

KEBANTACCIYAR SALLAH A DAREN NISFU SHA’ABAAN. (Dr. Mansur Sokoto)

Dr. Mansur Sokoto
KEBANTACCIYAR
SALLAH A DAREN NISFU
SHA'ABAAN.
Malaman hadisi sun ce:
Babu wani hadisin da ya
tabbata daga Manzon
Allah (saw) game da
wannan sallar da ake
kira Salatul Alfiyya. Sai
hadisai qagaggu da
raunana. Kadan daga
cikin irin wadannan
hadisai akwai hadisin da
aka jinginawa
Sayyadina Aliyyu wai ya
ce: Manzon Allah (saw)
ya ce;
ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﻨﺼﻒ ﻣﻦ
ﺷﻌﺒﺎﻥ ، ﻓﻘﻮﻣﻮﺍ ﻟﻴﻠﻬﺎ
ﻭﺻﻮﻣﻮﺍ ﻧﻬﺎﺭﻫﺎ ، ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻠﻪ
ﻳﻨﺰﻝ ﻓﻴﻬﺎ ﻟﻐﺮﻭﺏ ﺍﻟﺸﻤﺲ
ﺇﻟﻰ ﺳﻤﺎﺀ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ، ﻓﻴﻘﻮﻝ
ﺃﻻ ﻣﺴﺘﻐﻔﺮ ﻓﺄﻏﻔﺮ ﻟﻪ ، ﺃﻻ
ﻣﺴﺘﺮﺯﻕ ﻓﺄﺭﺯﻗﻪ ، ﺃﻻ
ﻣﺒﺘﻠﻰ ﻓﺄﻋﺎﻓﻴﻪ ، ﺃﻻ ﺳﺎﺋﻞ
ﻓﺄﻋﻄﻴﻪ ، ﺃﻻ ﻛﺬﺍ ﺃﻻ ﻛﺬﺍ
ﺣﺘﻰ ﻳﻄﻠﻊ ﺍﻟﻔﺠﺮ
Ma'ana:
“Idan daren Nisfu
Sha'aban ya zo ku raya
darensa da Qiyamullaili,
kuma ku azumci
yininsa, domin Allah
Madaukakin Sarki yana
saukowa zuwa saman
duniya daga zarar rana
ta fadi, yana cewa: shin
akwai mai neman
gafara ana gafarta
masa, ina mai neman
arziki na arzuta shi, ina
wanda Allah ya jarrabe
shi na yaye masa, ina
mai kaza da kaza har
zuwa ketaowar alfijir."
Amma sallar da ake kira
Salatul Alfiyya, salla ce
da ba ta da asali a cikin
addinin musulunci, kuma
an rawaito hadisai
masu yawa game da
bayanin siffarta da
falalarta, sai dai
dukkaninsu babu wanda
ya tabbata daga
Manzon Allah (saw).
Daga cikin wadannan
hadisan akwai hadisin
da aka jinginawa
Sayyadina Aliyyuyu Ibn
Abi Dalib wai ya ce:
Manzon Allah (saw) ya
ce:
ﻳﺎ ﻋﻠﻲ ﻣﻦ ﺻﻠﻰ ﻣﺎﺋﺔ ﺭﻛﻌﺔ
ﻓﻲ ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﻨﺼﻒ ﻣﻦ ﺷﻌﺒﺎﻥ
ﻳﻘﺮﺃ ﻓﻲ ﻛﻞ ﺭﻛﻌﺔ ﺑﻔﺎﺗﺤﺔ
ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭ )ﻗﻞ ﻫﻮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺣﺪ (
ﻋﺸﺮ ﻣﺮﺍﺕ ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻳﺎ
ﻋﻠﻲ ﻣﺎ ﻣﻦ ﻋﺒﺪ ﻳﺼﻠﻲ ﻫﺬﻩ
ﺍﻟﺼﻠﻮﺍﺕ ﺇﻻ ﻗﻀﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ
ﻭﺟﻞ ﻟﻪ ﻛﻞ ﺣﺎﺟﺔ ﻃﻠﺒﻬﺎ
ﺗﻠﻚ ﺍﻟﻠﻴﻠﺔ ﻗﻴﻞ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ
ﻛﺘﺒﻪ ﺷﻘﻴﺎ ﺃﻳﺠﻌﻠﻪ ﺳﻌﻴﺪﺍ
ﻗﺎﻝ ﻭﺍﻟﺬﻱ ﺑﻌﺜﻨﻲ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻳﺎ
ﻋﻠﻲ ﺇﻧﻪ ﻣﻜﺘﻮﺏ ﻓﻲ ﺍﻟﻠﻮﺡ
ﺇﻥ ﻓﻼﻥ ﺑﻦ ﻓﻼﻥ ﺧﻠﻖ ﺷﻘﻴﺎ
ﻳﻤﺤﻮﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻳﺠﻌﻠﻪ ﺳﻌﻴﺪﺍ …
Ma'ana:
“Ya Aliyyu! Duk wanda
ya yi salla raka'a dari a
daren Nisfu Sha'aban,
ya karanta Fatiha da
Qulhuw Allahu goma. Sai
Annabi ya ce: ya Aliyyu!
Babu wani bawa da zai
yi wannan sallar, face
Allah mai girma da
buwaya ya biya masa
buqatunsa da zai nema
a wannan daren. Sai aka
ce; ya Manzon Allah ko
da Allah ya rubuta shi a
cikin marasa rabo zai
mai da shi mai rabo? Sai
Manzon Allah (saw) ya
ce: na rantse da wanda
ya aiko ni da gaskiya,
haqiqa an rubuta a jikin
Lauhul Hamfuz cewa:
wane dan wane dan
wane an halicce shi
shaqiyyi, amma sai
Allah ya shafe shi ya
mai da shi marabauci…"
Haka kuma an sami
wani hadisi daga Amr
Ibn Miqdam daga Ja'afar
Ibn Muhammad daga
babansa ya ce:
ﻣﻦ ﻗﺮﺍ ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﻨﺼﻒ ﻣﻦ
ﺷﻌﺒﺎﻥ ﻗﻞ ﻫﻮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺣﺪ ﺃﻟﻒ
ﻣﺮﺓ ﻓﻲ ﻣﺎﺋﺔ ﺭﻛﻌﺔ ﻟﻢ ﻳﻤﺖ
ﺣﺘﻰ ﻳﺒﻌﺚ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻟﻴﻪ ﻣﺎﺋﺔ
ﻣﻠﻚ ﺛﻼﺛﻮﻥ ﻳﺒﺸﺮﻭﻧﻪ
ﺑﺎﻟﺠﻨﺔ ﻭﺛﻼﺛﻮﻥ ﻳﺆﻣﻨﻮﻧﻪ
ﻣﻦ ﺍﻟﻌﺬﺍﺏ ﻭﺛﻼﺛﻮﻥ
ﻳﻘﻮﻣﻮﻧﻪ ﺃﻥ ﻳﺨﻄﺊ
ﻭﻋﺸﺮﺓ ﺃﻣﻼﻙ ﻳﻜﺘﺒﻮﻥ
ﺃﻋﺪﺍﺀﻩ
Ma'ana:
“Wanda ya karanta
Qulhuw Allahu Ahad
qafa dubu a raka'a
goma, ba zai mutu ba
har sai Allah ya aiko
masa da mala'iku guda
dari, guda talatin daga
cikinsu za su yi masa
albishir da aljanna, guda
talatin za su amintar da
shi daga azaba, guda
talatin za su daidaita
shi kada ya yi kuskure a
rayuwarsa, guda goma
kuma za su rubuta
maqiyansa."
– Sheikh Abdulwahhab
Abdullah (Imamu
Ahlissunnati Wa
Jama'ah Kano).

SALLAH MAFIFICIYAR IBADAH !!! . _________FITOWA TA 8__________

SALLAH MAFIFICIYAR IBADAH !!!
.
_______FITOWA TA 8__________
.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
.
CIGABA GAME DA WASA DA SALLAH !!!
.
Kamar yadda muka fara haqalto abunda ya
tabbata daga Qur'ani da hadisi da
maganganun magabata dan gane da wasa
da sallah, haqiqa addinin musulunci yayi
bayani sosai ga matsayin sallah da hukuncin
wasa da shi.
.
•Imam Ahmad Ya ruwaito cikin "isnadi"
daga hadithin Abdullahi dan Amr (ALLAH Ya
qara masa yarda) daga Annabi (sallallahu
alaihi wasallam) Yace: "Wanda baya kiyaye
sallah, bayi da wani haske bayi da hujja bayi
da ku6uta, kuma zai kasance a ranar
alqiyama tare da Qaruna da Fir'auna da
Hamaana da ubayyu bin khalaf"
.
"Sahih ne Ahmad ya fitar dashi 6576 da
Daarimy 2/301-302]
.
•KISSAR ANNABI MUSA (ALAIHISSALAM) DA
WATA MATA DAGA BANI ISRA'ILA:
.
An ruwaito cewa wata mata daga cikin Bani
isra'ela taje zuwa ga Annabi Musa (Amincin
ALLAH su tabbata agare shi) tace: Ya Manzon
ALLAH, Ni na aikata zunubi, zunubi mai
girma, kuma haqiqa na tuba zuwa ga ALLAH
(SWT) ka qirayi ALLAH Ya gafarta min.
.
Sai Annabi Musa (Alaihissalam) yace da ita:
menene zunubinki? Sai tace: Ya Annabin
ALLAH, Ni na aikata zina kuma na haifi yaro
kuma na kashe yaron !!!
.
Sai Annabi Musa (Alaihissalam) Yace: tashi ki
fita Ya fajira kada a sauqar da wuta daga
sama ya qona mu saboda shu'umcin ki, sai
ta fita tana mai karaya a zuciyarta.
.
Sai Mala'ika Jibrilu (Alaihissalam) ya sauqa
yace: Ya Musa, Ubangijinka madaukaki Yace
a fada maka, Me yasa ka kori wacce take
neman tuba Ya Musa, shin baka san akwai
abunda yafi wannan sharri ba ???
.
Sai Annabi Musa (Alaihissalam) Yace:
menene abunda yafi wannan sharri? Sai
Jibrilu (Alaihissalam) Yace: "BARIN SALLAH DA
GANGANCI".
.
•MU HANKALTA: wannan kissar tana mana
hannunka mai sanda wajen nuna mana
cewa Barin sallah da ganganci zunubinsa
yafi muni sama da wanda ya aikata zina
wa'iyazubillahi.
.
Ya ALLAH Ka gafarta mana zunubanmu kuma
ka kar6i kyawawan ayyukanmu kuma ka
sanya mu masu tsaida sallah tare da bayinka
salihai (Ameen)
.
Mu hadu a Fitowa ta 9 inshaa ALLAH.
.
YAR'UWARKU:
Faridah Bintu Salis
(Bintus~sunnah)

SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!! . __________FITOWA TA 7__________

SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!!
.
________FITOWA TA 7__________
.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
.
CIGABA GAME DA WASA DA SALLAH !!!
.
Har yanzu muna cigaba ne cikin bayanin me
wasa da sallah kamar yadda muka ce zamu
kawo bayanan da suka zo daga ayoyin
ALLAH da Hadisai da kuma maganganun
magabata.
.
Ibn Hazam Yace: babu wani zunubi mafi
girma bayan shirka irin mutum yayi wasa da
sallah har lokacinta ya fita, ko kuma kashe
mumini ba tare da haqqi ba.
.
Hammam Ya ruwaito cewa Qatada daya ne
daga cikin tabi'ai, daga Hasanul basari daga
haraithu dan qabisatu Yace: Abi-hurayrah ya
bamu labari daga Manzon ALLAH (sallallahu
alaihi wasallam) Yace: "Farkon abunda za'a
fara yiwa bawa hisabi da shi na ayyukansa
ranar alqiyama ita ce Sallah, idan aka samu
sallar tayi kyau, to haqiqa ya rabauta kuma
ya tsira, idan kuma ta 6aci to haqiqa ya ta6e
kuma yayi hasara"
.
[Ingantacce ne Nasa'I ya fitar dashi 1/232
da Tirmizi 413, daga hadisin Huraithu dan
Qabisatu, rufaffe ne shi]
.
Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam)
Yace: "An umurce ni na yaqi mutane har sai
sun shaida cewa: Babu abun bautawa da
gaskia sai ALLAH kuma lallai muhammadu
Manzon ALLAH ne, kuma su tsaida Sallah
kuma su bada zakkah, idan suka aikata haka
juninsu da dukiyarsu ya ku6uta daga gare
ni, sai dai idan da wani haqqi na musulunci,
to wannan kuma hisabinsu naga ALLAH"
.
[Andaidaita akansa]
.
Daga Abi-sa'eed (ALLAH Ya qara masa Yarda)
Yace: "Lallai wani mutum Yace: Ya Manzon
ALLAH, Kaji tsoron ALLAH, Sai Manzon ALLAH
(Sallahu alaihi wasallam) Yace: "ka ta6e, a
doron qasa akwai wanda yafi cancanta yaji
tsoron ALLAH bayan ni !!?" Sai Khalid Bin
Waleed (ALLAH Ya qara masa Yarda) Yace: Ya
Manzon ALLAH ba zaka bari na fille masa kayi
ba, sai Manzon ALLAH (sallallahu alaihi
wasallam) Yace: "A'A wataqila ya kasance
yana yin sallah"
.
[Andaidaita akansa]
.
ALLAHU AKBAR, Yan'uwana ku duba saboda
falalar sallah ne Manzon ALLAH (Sallallahu
alaihi wasallam) Ya hana sahabin nan
khaleed bin waleed sare kan wannan
mutumin.
.
Kuma hadisin ba falalar SALLAH kadai take
tabbatarwa ba hada falalar HAQURI, duba da
irin girma da daraja ta Annabin ALLAH amma
yayi haquri da abunda mutumin nan ya fada
masa ya kuma hana a sare shi.
.
Amma mutanen wannan zamanin wanda
idan da za a haqalto da ayyukanmu ko
farcen qafa na ayyukan wani sahabi bai kai
ba. Amma da wani zai ce wane kaji tsoron
ALLAH shike nan sai ka tada jijiyoyin wuya
kana huci wai kai a dole an rena maka wayo
saboda ance kaji tsoron ALLAH.
.
Ya ALLAH Ka shiryar damu bisa hanya
madaidaiciya, ka sanya mu cikin bayinka
salihai masu tsayar da sallah (Ameen)
.
Mu hadu a Fitowa ta 8 inshaa ALLAH.
.
YAR'UWARKU:
Faridah Bintu Salis
(Bintus~sunnah)

SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!! . __________FITOWA TA 6__________

SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!!
.
________FITOWA TA 6__________
.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
.
CIGABA GAME DA WASA DA SALLAH !!!
.
A rubutun da ya gabata mun fara bayani
game da mai wasa da sallah kamar yadda
yazo daga ayoyin ALLAH da Hadisai da kuma
maganganun magabata.
.
Manzon ALLAH (sallahu alaihi wasallam)
Yace: "Alqawarin da ke tsakanin mu da
sauran bayin ALLAH sallah ne, wanda ya
barta yaqi yi gaba daya ya zama kafiri"
.
[Ingantacce ne Ahmad ya fitar dashi 5/346
da Tirmizi (2621) da Nasa'I (464)]
.
Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam)
Yace: "Duk wanda ya bari sallar la'asar ta
kubce masa (da ganganci) to ayyukansa sun
lalace"
.
[Ingantacce ne Bukhari fitar dashi (553) da
Nasa'I (1/236]
.
Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam)
Yace: "Abunda ke tsakanin bawa da shirka
ita ce sallah"
.
[Ingantacce ne, Muslim ya fitar dashi
(82/134) da Tirmizi (2619)
.
Manzon ALLAH (sallallahu Alaihi wasallam)
Yace: "Duk wanda yabar sallah da gaganci,
haqiqa alqawarin da ALLAH ya dauka na
taimako akan shi ya warware"
.
[Ingantacce ne Bukhari ya fitar dashi cikin
Adabul Mufrad (18) da Ibn Majah (4034)]
.
Umar dan Khattab (ALLAH Ya qara masa
Yarda) Yace: "Yadda al'amari yake dukkan
wanda ya tozarta sallah to bayi da kaso
acikin musulunci"
.
[Ingantacce ne Muhammad dan Nasr ya fitar
dashi acikin Ta'azimu Qadarus swalat (925)]
.
Ibrahimun Nakha'iy (Almajiri ne daga
Almajiran Abdullahi dan Abbas ALLAH Ya
qara masa Yarda) Yace: wanda ya bar sallah
da ganganci ya kafirta"
.
Ayuba Assakhityani shima abunda ya fada
misalin hakan ne.
.
[Ingantacce ne Dan Nasr ya fitar dashi acikin
Ta'azimu Qadarus swalaat (978) da sanadi
ingantacce]
.
Jareer Ya ruwaito daga Abdullahi dan
shaqeeq, daga Abu-hurayrah (ALLAH Ya qara
musu Yarda) Yace: "Sahabban Manzon ALLAH
(Sallallahu alaihi wasallam) sun kasance basa
ganin wani aiki wanda barinsa yake mai da
mutum kafiri idan ba sallah ba"
.
[Ingantacce ne Hakeem ya fitar dashi (1/8)
da sanadi mai rauni, sai yace: Tirmizi ya fitar
dashi (2622) da sanadi ingantacce wa lahu
shaahid]
.
Ya ALLAH Ka sanya mu cikin bayinka salihai
masu tsayar da sallah (Ameen)
.
Mu hadu a Fitowa ta 7 inshaa ALLAH.
.
YAR'UWARKU:
Faridah Bintu Salis
(Bintus~sunnah)

SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!! . __________FITOWA TA 5__________

SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!!
.
________FITOWA TA 5__________
.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
.
WASA DA SALLAH !!!
.
A rubutun da ya gabata munyi bayanin
matsayin sallah da falalarsa da irin darajar
da mai kiyayeta zai samu daga sakayyar
UbangijinSa. Yanzu kuma zamu daura akan
bayani game da WASA DA SALLAH da irin
sakamakon da mai yinsa zai samu kamar
yadda yazo cikin alqur'ani da sunnah da
fahimtar magabata.
.
Babban Malamin nan Dr. Mustapha Miraad ya
haqalto acikin littafinsa mai suna "Nisa'u
Ahlun naar" inda yake cewa: daga manyan
zunubai a wajen ALLAH masanin gaibu
bayan shirka da kafurci sai wasa da sallah,
ALLAH (Subhanahu wa Ta'ala) Yana cewa:
.
۞ ﻣَﺎ ﺳَﻠَﻜَﻜُﻢْ ﻓِﻴﺴَﻘَﺮ۞ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﻟَﻢْ ﻧَﻚُ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻤُﺼَﻠِّﻴﻦ۞ﻭَﻟَﻢْ
ﻧَﻚُ ﻧُﻄْﻌِﻢ ﺍﻟْﻤِﺴْﻜِﻴﻦ۞ﻭَﻙﺎَّﻧُ ﻧَﺨُﻮﺽُ ﻣَﻊَ ﺍﻟْﺨَﺎﺋِﻀِﻴﻦ۞ﻭَ
ﻛُﻨَّﺎ ﻧُﻜَﺬِّﺏُ ﺑِﻴَﻮْﻡِ ﺍﻟﺪﻳﻦ۞ﺣَﺘَّﻰٰ ﺃَﺗَﺎﻧَﺎ ﺍﻟْﻴَﻘِﻴﻦُ ۞
.
FASSARA: "suce musu me ya shigar daku a
cikin saqar * suka ce bamu kasance masu
yin sallah ba* kuma bamu kasance masu
ciyar da miskinai ba* kuma mun kasance
masu kutsawa da masu kutsawa* mun
kasance muna qaryata ranar sakamako* Har
gaskia (wato mutuwa) tazo mana."
.
[Suratul Mudaththir aya ta 42 zuwa 47]
.
Hakanan yana cewa:
.
۞ َﻓَﺨَﻠَﻒَ ﻣِﻦ ﺑَﻌْﺪِﻫِﻢْ ﺧَﻠْﻒٌ ﺃَﺿَﺎﻋُﻮﺍ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﻭَﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﺍ
ﺍﻟﺸَّﻬَﻮَﺍﺕِ ﻓَﺴَﻮْﻑَ ﻳَﻠْﻘَﻮْﻥَ ﻏﻴﺎ۞
.
FASSARA: "sai wadansu 'yan baya suka maye
a bayansu, suka tozarta sallah, kuma suka bi
sha'awowin su, to da sannu zasu hadu da
wani sharri"
.
[Suratul Maryam aya ta 59]
.
Kuma Yake cewa:
.
۞ ﻓَﻮَﻳْﻞٌ ﻟِّﻠْﻤُﺼَﻠِّﻴﻦَ۞ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻫُﻢْ ﻋَﻦ ﺻَﻠَﺎﺗِﻬِﻢْ ﺳَﺎﻫُﻮﻥَ ۞
.
FASSARA: "Bone ya tabbata ga masallata *
wadanda suke masu shagala daga sallar su"
.
[Suratul Ma'uun aya ta 4 zuwa 5]
.
Idan wannan ya kasance sakamakon mai
jinqirin sallah har lokacinta ya wuce, ko
kuma zai yita akan lokaci amma baya bayar
da rukunnanta, ko kuma baya yin khuhu'i
acikinta, to yaya kuma matsayin wanda baya
yinta gaba daya ???
.
Ya ALLAH Ka sanya mu cikin bayinka salihai
masu tsayar da sallah (Ameen)
.
Mu hadu a Fitowa ta 6 inshaa ALLAH.
.
YAR'UWARKU:
Faridah Bintu Salis
(Bintus~sunnah)َ

SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!! . __________FITOWA TA 4_________

SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!!
.
________FITOWA TA 4_________
.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
.
Kamar yadda muka yi bayanin falalar sallah
da irin rabautar da bawa zai samu idan ya
kasance ma'abocin kulawa da ita.
.
Kamar yadda muka yi bayani lallai ita sallah
tana da salloli na kwadaitarwa musamman
kasancewa ALLAH Ta'ala yana son bawa mai
yawan sujjada.
.
Sujjada yana daya daga cikin abubuwanda
ALLAH Ta'ala yake so, saboda girman sallah
da darajarta sai sujjada ya kasance wani
6angare ne daga cikin sallah, saboda kuma
girman sujjada har ta zamanto hanyar shiga
aljannah ga mai yawan yinta.
.
Sai dai kash !!! Mafi yawan bil'adama a
wannan zamanin ba kowa bane yake
jajircewa wajen aikata salloli na
kwadaitarwa wanda zai bashi damar
yawaita yin sujjadar.
.
Yan'uwa dole ne sai mun jajirce mun kori
shaidan kafin mu samu mu cimma burinmu
na son kasancewa cikin ni'imar ALLAH
Ta'ala.
.
Haqiqa masoyinmu fiyayyen halitta Annabi
Muhammad (sallallahu alaihi wasallam) Ya
kwadaitar damu yawan sujjada ya kuma
sanar damu girman falalarta da soyuwarta
ga ALLAH Ta'ala.
.
Kamar yadda hadithai suka zo daban daban
zamu kawo wasu daga ciki kamar haka:
.
• Daga Abu Firas Rabi'ata bn ka'abu
al'aslamy (Radiyallahu anhu) Hadimin
Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam
kuma daya daga Ahlussufah yace: Na
kasance ina kwana tare da Manzon ALLAH
(Sallallahu alaihi wasallam) sai na kawo masa
ruwan alwalarsa da abun buqatarsa, sai
Yace dani: "tambayi abunda kake buqata"
sai nace ina roqon kasancewa tare da kai a
Aljannah, sai yace: "kodai wani abun ba
wannan ba" sai nace: Ni dai wannan nake
roqo, sai yace to ka taimaka min da yawan
sujjada"
.
[Muslim ya ruwaito]
.
• Daga Abi-Abdillah, Thauban (Radiyallahu
anhu) 'Yantaccen Manzon ALLAH (Sallallahu
alaihi wasallam) yace naji Manzon ALLAH
(Sallallahu alaihi wasallam) yana cewa: "ka
kula da yawan sujjada, domin duk lokacin
da kayi Sujjada daya saboda ALLAH, Sai
ALLAH Ya daukaka darajarka kuma ya shafe
maka zunubi daya saboda ita"
.
[Muslim ne ya ruwaito shi]
.
• Daga Jabir (Radiyallahu anhu) yace: Naji
Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam)
yana cewa: "lallai acikin dare akwai wani
lokaci, wanda matuqar musulmi ya dace
yana roqon ALLAH wani abu na alkhayri
acikinsa, wanda ya shafi lamarin duniya
dana lahira, tabbas ALLAH zai bashi, wannan
kuwa yana kasancewa ne cikin ko wani
dare"
.
[Muslim ne ya ruwaito shi]
.
• Daga Mughira dan shu'abah (Radiyallahu
anhu) yace : Annabi (Sallallahu alaihi
wasallam) yayi qiyamullaili har sai da
qafafuwansa suka kumbura, da akace dashi
ai ALLAH Ya gafarta maka abunda ya gabata
da wanda ya jinqirta daga zunubinka sai
Yace: "Ashe bazan kasance bawa mai godia
ba?"
.
[Bukhari da Muslim da Nasa'e ne suka
ruwaito shi]
.
• Hadith yazo daga dan Abbas (Radiyallahu
anhu) yace Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi
wasallam) ya umurce mu da yin salkah cikin
dare, ya kwadaitar game da haka, har ta kai
yana cewa: "ku kula yin sallah cikin dare
koda kuwa raka'a daya ne tak zaku sallata"
.
[Dabarani Ya ruwaito]
.
• Dabarani ya ruwaito acikin Alkabir, daga
Abu-malik al'ash'ari (Radiyallahu anhu) yace:
Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam)
yace: duk mutumin da ya farka cikin dare, ya
tashi matarsa, idan kuma bacci ya rinjayeta
ya yayyafa mata ruwa a fuska, suka ambaci
ALLAH mai girma da buwaya, tsawon wani
lokaci acikin dare to tabbas za'ayi musu
gafara"
.
Dan'uwa mai iyali sai ka tambayi kanka sau
nawa ka tashi cikin dare har ka tashi
iyalinka domin qiyamullaili ???
.
Mu ma masu karatu sai mu tambayi kanmu
shin sau nawa muka aikata hakan???
.
Lallai sai mun jajirce dai mun fafari shaidan
kafin mu samu damar aikata ayyukan ibada.
.
Muna roqon ALLAH Ya bamu iko Ya gafarta
mana Ya sanya mu cikin bayinsa masu
tsaida sallah dayin sallolin kwadaitarwa.
(Ameen)
.
Mu hadu Fitowa ta 5 Inshaa ALLAH.
.
Daga Yar'uwarku:
Faridah Bintu Salis
(Bintus~sunnah)