MUHADARORI/WA’AZI DARI (100) NA SHEIKH KABIR GOMBE

MUHADARORI/WA’AZI DARI (100) NA SHEIKH KABIR GOMBE

Wadannan Kadan Ne Daga Cikin Wa’azuzzuka Da Babban Sakataren ‘Kungiyar Jama’atu-Izalatil-Bid’ah- Wa-Ikamatis-Sunnah Na Kasa Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe Hafizahullah Ya Gabatar, Wadanda Cibiyar Yada Sunnah Ta DARULFIKR Ta Dora, Kuma Admins Na Dandalin Masoya Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe Hafizahullah #ISupportSheikKabirGombe Suka Tattara Domin Ku Sami Saukin Saukewa.

000 Yi Like Din Shafin Mu A Facebook
http://facebook.com/ISupportSheikKabirGombe
001 Kula Da Sallah
http://darulfikr.com/s/21704
002 Kyautatawa a Musulunci
http://darulfikr.com/s/22411
003 Matasa Mu Tashi Mu Nema Ilimi
http://darulfikr.com/s/22414
004 Matan Aljannah A Duniya
http://darulfikr.com/s/22415
005 Tausayin Yara Mata akan Iyayensu
http://darulfikr.com/s/22523
006 Ta’aziyan Alhaji Ahmadu Chanchangi
http://darulfikr.com/s/22522
007 Kabari Aya ne A Garemu
http://darulfikr.com/s/22520
008 BANBAMCI TSAKANIN GWAURO DA MAI AURE
http://darulfikr.com/s/7431
009 Duniya Budurwar Wawa
http://darulfikr.com/s/10159
010 MATASA KASHIN BAYAN RAYA SUNNAH
http://darulfikr.com/s/21151
011 Muhimmancin Gudunmawa a Musulunci
http://darulfikr.com/s/10285
012 Rashin godiyar Allan mu game da BUHARIYYAH
http://darulfikr.com/s/8869
013 Saki kowa ka kama Allah
http://darulfikr.com/s/20022
014 Son Zuciya ubangiji ne da wasu ke bautawa
http://darulfikr.com/s/10113
015 Sunnah in Bakayi Bani Guri
http://darulfikr.com/s/9209
016 Waye Masoyin Annabi
http://darulfikr.com/s/10392
017 Ayatullahi Buratai
http://darulfikr.com/s/4106
018 Garin Neman Gira An Rasa Ido
http://darulfikr.com/s/2912
018 Rayuwa Adam Acikin Duniya
http://darulfikr.com/s/5093
019 Wasika Zuwaga Mawadata
http://darulfikr.com/s/3027
020 Ladubban Tarewa A Sabon Gida
http://darulfikr.com/s/3016
021 Tonon Silili Da Tufin Allah Tsine
http://darulfikr.com/s/4144
022 Anyi walkiya mun gansu
http://darulfikr.com/s/1309
023 DAN KASA NAGARI
http://darulfikr.com/s/18314
024 IKLar Shaye-Shaye
http://darulfikr.com/s/927
025 Riba da illolinta
http://darulfikr.com/s/929
026 Gyara kayan ba zai zamo sauke mu raba ba
027 http://darulfikr.com/s/3586
028 Ihidinas Siradal Musataeem
http://darulfikr.com/s/5413
029 BIDI’AR MAULIDI
030 http://darulfikr.com/s/935
031 Kowanne tsintsu kukan gidan su yake
http://darulfikr.com/s/5252
032 Majlisin Malamai
http://darulfikr.com/s/4401
033 Makircin Shi’a
http://darulfikr.com/s/2432
034 Nigeria ta fara hayaki
http://darulfikr.com/s/942
035
Ribar kafa
http://darulfikr.com/s/9092
036 ILLAR ZINA
http://darulfikr.com/s/939
037 Shirin Fatawa na Kada Fm
http://darulfikr.com/s/6854
038 ILLOLIN JAHILCI
http://darulfikr.com/s/944
039 SADA ZUMINCI
http://darulfikr.com/s/946
040 MADINAR GAUSI
http://darulfikr.com/s/949
041 MALAMN BIDIA DILALA SHARI
http://darulfikr.com/s/945
042 MATAN ANNABI SAW
http://darulfikr.com/s/947
043 MATAN ANNABI SAW 2
044 http://darulfikr.com/s/948
045 MUMMUNAR CIKAWA
http://darulfikr.com/s/950
046 SUNNA SAK BIDI’A SAM
http://darulfikr.com/s/952
047
HUKUNCHIN KALLO
http://darulfikr.com/s/951
048 KO KINKI KO KINSO
http://darulfikr.com/s/953
049 WEYE MAI SALLAH
http://darulfikr.com/s/955
050 YAN SHI’A
http://darulfikr.com/s/956
051 WA’AZIN KANGIWA
http://darulfikr.com/s/18197
052 WA’AZIN GARIN LARABAR ABASAWA
http://darulfikr.com/s/17975
053 WA’AZIN MATA NA DORAYI
http://darulfikr.com/s/17976
054 Wa’azin Mata Sumaila
http://darulfikr.com/s/17972
055 Wa’azin Lagos 01
http://darulfikr.com/s/9112
056 Wa’azin Lagos
http://darulfikr.com/s/7434
Waazin zamfarah
ttp://darulfikr.com/s/8764
057 Wa’azin Miya
http://darulfikr.com/s/5519
058 Wa’azin Owode Ogun
http://darulfikr.com/s/19055
059 Wa’azin sokoto 1
http://darulfikr.com/s/930
060 Wa’zin Sokoto 2
http://darulfikr.com/s/931
061 Wa’zin Sokoto 3
http://darulfikr.com/s/933
062 Wa’azin Mata Zamfarah
ttp://darulfikr.com/s/932
063 Wa’azin Suleja
http://darulfikr.com/s/934
064 Wa’azin Kankiya
http://darulfikr.com/s/3393
065 Wa’azin Yantumaki
http://darulfikr.com/s/937
066 Wa’azin Billiri
http://darulfikr.com/s/5258
067 Wa’azin Bolari
http://darulfikr.com/s/5252
068 Wa’azin Yola
http://darulfikr.com/s/957
069 Wa’azin Jalingo
http://darulfikr.com/s/20862
070 Wa’azin,Accra Ghana
http://darulfikr.com/s/9092
071 Wa’azin Niger
http://darulfikr.com/s/940
072 Wa’azin Illela
http://darulfikr.com/s/943
073 Wa’azin Pandogari 1
http://darulfikr.com/s/954
074 Wa’azin Pandogari 2
http://darulfikr.com/s/936
075 Wa’azin Sumaila Kano
http://darulfikr.com/s/17973
076 Wa’azin Agege Lagos
http://darulfikr.com/s/18503
077 Wa’azin Jahar Kano
http://darulfikr.com/s/13102
078 Wa’azin Bauchi
http://darulfikr.com/s/4203
079 Wa’azin Jihar Kano 5
http://darulfikr.com/s/1369
080 Wa’azin Liman Katagun Bauchi
http://darulfikr.com/s/4204
081 Waazin Mata Taraba
http://darulfikr.com/s/19931
082 Wa’azin Maza Ogere
http://darulfikr.com/s/19059
083 Wa’azin Mata Owode Ogun
http://darulfikr.com/s/19058
084 Wa’azin Maza Owode Ogun
http://darulfikr.com/s/19057
085 Wa’azin Mata Ogere
http://darulfikr.com/s/19074
086 Wa’azin Shagamu Ogun
http://darulfikr.com/s/19060
087 Alaba Rago Lagos
http://darulfikr.com/s/19075
088 Wa’azin Zaria
https://kiwi6.com/file/494p6nu72v
089 Wa’azin Yola 2
https://kiwi6.com/file/mritel0tu0
090 Wa’azin Kumo
https://kiwi6.com/file/xwu3stijrf
091 Wa’azin Lagos 2014
https://kiwi6.com/file/zo52lzbay2
092 Wa’azi Funtua
https://kiwi6.com/file/fh6j8e6e0v
092 Wa’azin Gamahttps://kiwi6.com/file/0ptyt0vi2m
093 Wa’azin Suleja 2
https://kiwi6.com/file/st2bmi55wv
094 Wa’azin Tsafe
https://kiwi6.com/file/1ygupz01fh
095 Wa’azin Dan Sadau
https://kiwi6.com/file/kfnr1bkenv
096 Wa’azin Ikara
https://kiwi6.com/file/71ngomy2zu
097 Wa’azin Madobi
https://kiwi6.com/file/56555ivywk
098 Wa’azin Rano
https://kiwi6.com/file/kmyjhjzx15
099 Wa’azin Jos
https://kiwi6.com/file/r8ghnl8jvu
100 Wa’azin Kaduna City
https://kiwi6.com/file/lhejc4i4nq
Kuci Gaba Da Kasancewa Damu Domin Samun Links Da Zaku Sauke Karatukan Malam Da Sauran Malaman Sunnah.
dannan Link Din Dake Kasa Kayi Like Na Shafin Mu.
http://www.facebook.com/ISupportSheikKabirGombe

Advertisements

MANYAN SAHABBAI GOMA YAN ALJANNAH!

Dr Isa Ali Pantami at ﺍﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﺍﻟﻤﻨﻮﺭﺓ. ﻣﺴﺠﺪ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ. .

HAUSA & ENGLISH
MANYAN SAHABBAI GOMA YAN ALJANNAH!
Annabi (SAW) yana cewa: abubakar yana
Aljannah; 'Umar yana Aljannah; 'Uthman
yana Aljannah; 'Ali yana Aljannah; Talhah
yana Aljannah; al-Zubair yana Aljannah;
'AburRahman Bn 'Awf yana Aljannah; Sa'd
yana Aljannah; Sa'eed yana Aljannah; sannan
Abu 'Ubaidah ibn Jarrah yana
Aljannah." (Abu Dawood, 4649; al-Tirmidhi,
3747; Shaykh Albaaniy ya inganta shi).
Wajibi ka san su, da ayyukansu don kayi koyi
da su, kuma ka kare martabansu. Yaa Allah
ka bamu ikon koyi da wadannan Sahabai
(RA) da sauran Sahabbai. Yaa Allah ka sa mu
makwabce su a Aljannah,…
TEN COMPANIONS WITH GLAD TIDINGS OF
PARADISE!
The Prophet (SAW) says: “Abubakar in
Paradise; ‘Umar in Paradise; ‘Uthmaan in
Paradise; ‘Ali in Paradise; Talhah in Paradise;
al-Zubayr in Paradise; ‘Abd al-Rahmaan ibn
‘Awf in Paradise; Sa’d in Paradise; Sa’eed in
Paradise; and Abu ‘Ubaydah ibn al-Jarraah in
Paradise.”
(Narrated by Abu Dawood, 4649; al-Tirmidhi,
3747; classed as saheeh by Shaykh Albaaniy)
You must study their biography, emulate
their actions and defend their personality.
May Allah give us the ability the emulate the
Companions (RH) and make us their
Neighbors in Paradise,…

SAKON KHUDUBAR JUMU’AH DAGA MASALLACIN MANZON ALLAH (SAW) DA YAKE MADINAH DAGA BAKIN DR SALAH BN MUHAMMAD AL-BUDAIR (HZ) TA YAU JUMU’AH 26/04/1437AH (05/02/2016CE).

SAKON KHUDUBAR JUMU’AH DAGA
MASALLACIN MANZON ALLAH (SAW) DA YAKE
MADINAH DAGA BAKIN DR SALAH BN
MUHAMMAD AL-BUDAIR (HZ) TA YAU JUMU’AH
26/04/1437AH (05/02/2016CE).
FASSARAWAR DAN’UWANKU ISA ALI PANTAMI
Wannan Matashin limamin mai shekaru 46
yayi khudubar Jumuah bayan sama da wata
uku da yayi yana fama da jinya ta rashin
lafiya. Yayi khudubar kan “FITINTINUN
MATASA DA WAJIBCIN HADUWAR AL’UMMAH
DA BIYAYYA GA SHUGABANNIN MUSULMAI.”
Ga sakon a takaice:
1) Limamin yayi Muqaddimah da fara godiya
ga Allah (SWT) akan Ni’imominsa wadanda
suke da yawa, sannan yayi salati da yabo ga
AnnabinSa (SAW) da addu’ar alheri ga
Sahabbansa (RA).
2) Ya tunatar da masallata Musulmai akan
ILMI, da TAQWAH da FAHIMTAR ADDINI na
hakika sune hanyar tsira daga dukkan
fitintinu. Wato dole muyi riko da su don mu
tsira.
3) Sannan yayi bayani kan yarda wannan
kasa mai Albarka “Mamlakah” take dore
akan addini da shari’ar Musulunci.
4) Ya bayyana cewa lalle haduwar al’ummah
(akan gaskiya) RAHAMA CE. Sannan
rarrabuwa sharri ne.
5) Duk da wannan kokari na “MAMLAKAH”
an samu jama’ar da suka yi tawaye suka fice
daga karkashin shugabanci, sun kashe
Musulmai da wandanda ba musulmai ba.
6) Masu wannan fahimtar duk wanda yayi
magana da (sunan addini) suna bin sa
kawai (ba tare da cikakken ilmi ba).
7) Duk wanda ya taimakawa masu irin
wannan aqidah ta tawaye da barna, tabbas
ya taimaki ‘barna.
8) Sannan masu irin wannan fahimta ta
‘barna galibinsu masu karancin shekaru ne.
9) Limamin ya karanta hadisai na Manzon
Allah(SAW). Daga cikin su, ya karantar cewa
Annabi (SAW) yana cewa: Wanda ya fita
daga Jama’ah, ya raba Jama’ah in ya mutu
yayi mutuwar Jahiliyyah (Muslim ne ya
ruwaito).
10) Masu wannan fahimtar, Jama’ah ne
batattu kamar yadda Sunnah ta bayyana.
11) Limamin yayi bayani akan hatsarin da
iyaye ke abkawa na barin ‘ya’yansu suna
afkawa cikin wadandan fitintinu, da bin
kowa, yara suna kwana a waje, ba tare da
iyayensu sun sani ba, kuma iyayen ba sa
bincike. Duk uban da ya bar ‘ya’yansa haka
lalle yana cutar al’ummah.
12) Akwai hatsari sosai cikin masu zagi da
yawan aibata daular musulunci ta Saudi
Arabia.
13) KHAAWAARIJ (wadanda suke fita daga
yiwa jagororin addinin musulunci biyayya su
dauki makami) batattun mutane ne.
14) KHAAWARIJ (masu tawaye) kala biyu ne.
1) Akwai wadanda suke zaune, 2) akwai na
tsaye, wadanda suke fita da makamai.
15) Wadanda ke zaune suna karantar da
matasa kashe kawunansu a kasuwanni da
masallatai da sauran wurare.
16) Sannan wadandan matasa masu
karancin shekaru suna aikata irin wadandan
munanan ayyuka.
17) Limamin yayi kira ga masu raba Jama’ah
(da kawo irin wadannn fitintinu) da cewa
cin amanar addini ne.
18) Limamin ya tunatar da cewa “Idan mun
yi TAQAWAH (kyakykyawar biyayya ga Allah)
za’a karemu a tunkude mana fitina daga
garemu.
19) Yaku Musulmi ku bi littafin Allah da ya
saukar muku.
20) Sannan yayi tsokaci kan abunda ke
faruwa a Syria da sauran kasashe yadda ake
kashe musulmai, yara da manya da mata.
21) A Syria yau ana koran mutane daga
gidajen su suna gudu zuwa jeji. Ana koran
tsofi, kuma ana kashe su.
22) Wajibi ne kokari wajen kawo karshen
wadannan fitintinu.
23) Limamin ya yiwa Annabi (SAW) Salati.
24) Yayi adduar Allah ya hadamu a Aljannah
gaba daya.
25) Limamin yayi addu’ar Allah ya taimaki
Musulunci da Musulmai.
26) Yayi addu’ar Allah ya rusa makiya addini
da sauran Daqutai.
27) Limamin yayi addua wa al-Ummar Syria
da Palestine.
28) Yayi adduar Allah ya datar da Imam
kuma Shugabanmu “Khaadimul Haramayn”
da mataimakansa biyu zuwa ga abunda
Allah yake so ya yarda da shi.
29) Yayi adduar Allah ya taimaki sojojin
Musulmai dake filin daga.
30) Yayi adduar Allah ya samu cikin masu
Taqawah.
31) Daga karshe yayi adduar cewa “Yaa
Allah ka amsa mana addu’o’inmu,…
Daga karshe muna addu’ar Allah ya amsa
mana wadannan addu’o’inmu sannan ya
bamu ikon aiki da khudubar,…
(You may wish to share it to get reward. May
Allah reward you immensely for sharing).

SAKON KHUDUBAR JUMU’AH DAGA MASALLACIN MANZON ALLAH (SAW) DAKE MADINAH DAGA BAKIN SHEIKH ABDULMUHSIN BN MUHAMMAD AL-QASIM (HZ) A YAU RANAR 19/04/1437AH (29/01/2016CE).

SAKON KHUDUBAR JUMU'AH DAGA MASALLACIN MANZON
ALLAH (SAW) DAKE MADINAH DAGA BAKIN SHEIKH
ABDULMUHSIN BN MUHAMMAD AL-QASIM (HZ) A YAU RANAR
19/04/1437AH (29/01/2016CE). FASSARAWAR DAN'UWANKU: ISA
ALI IBRAHIM PANTAMI.
Limamin a ranar wannan Jumu'ah yayi Khudubar ne akan "ILMI,
DARAJARSA DA MATSAYIN MA'ABOTANSA."
Ga sakon kamar haka
1) Babban limamin ya fara da al-Khudubatul-Hajah, wacce itace
khudubar da Annabi (SAW) yake fara wa'azi ko huduba da ita.
Tana karantar da kadaita Allah, da nuna shiriya ta Allah ne, kuma
ribar rayuwa na cikin Taqwa.
2) Sannan Limamin yayi umurni da "Taqwa" wato cikakkiyar
biyayya ga Allah (SWT). Domin Taqwa itace hasken da ake gani da
shi, kuma Taqwa ke rayar da zuciya. Allah yana cewa: "Lalle
wanda yafi daraja gun Allah shine wanda yafi Taqwa."
3) ILMI DA TAQWA ke shiryar da bawa zuwa ga MahaliccinSa.
Domin da ilmi da Taqwa ake banbancewa tsakanin HALAL da
HARAM.
4) Ma'abota Ilmi da su ake samun shiriya. Imam Ahmad Bn
Hambal (RH) yana cewa: "Mutane suna da bukatar Ilmi fiye da
abinci. Domin abinci akan bukace shi ne sau 2 ko sau 3 a wuni,
amma ILMI ana bukatarsa a kowane lokaci a kowace rana."
5) Allah ya siffata kan Sa da ilmi. Allah yana cewa: "(Allah) ya
ilmantar da mutum abun da bai sani ba."
6) ILMI HIKIMA CE, da Allah ke baiwa bayinSa. Allah yana cewa:
"Yana bada hikima ga wanda ya so, duk wanda aka ba shi hikima,
hakika an ba shi alheri mai yawa."
7) Allah ya fifita dan Adam da ilmi akan Malaa'ika. "Wa 'allama
Adamal Asma'a kullaha thumma arabhahum alal Malaa'ikati…."
8) Allah ya bawa Yusuf (AS) ilmi. Allah yace: "Lokacin da ya kai
karfinsa, mun ba shi hukunci da ilmi."
9) Allah ya daukaka darajar wasu Annabawa sosai kuma ya
bayyana cewa ya ba su ilmi. Daga cikinsu, akwai Musa, Is'haq,
Daud, Sulayman, da Isa (AS).
10) Duk da darajar Annabi Musa (AS) yaje wajen Khidr neman ILMI
kamar yadda Qur'ani ya bayyana cikin Suratul Kahf. (Wannan ke
bayyanawa cewa DARAJA ko daukaka ba sa hana neman ilmi).
11) Qissar Annabi Sulayman a Suratun-Naml ta karantar da mu
cewa, lalle mai Ilmi yafi mai karfi da bai da ilmi. (Kamar yadda
Qur'ani ya nuna mana cewa, Aljanin da ke da "Ilmun Minal Kitaabi"
yafi "Ifritu" da ke da karfi, samun nasara wajen ayyuka).
12) Allah ya karantar da mu cewa shi ya ILMANTAR da Annabinmu
(SAW). Allah SWT yana cewa: "Ya ilmantar da kai abun da ba ka
sani ba. Lalle falalar Allah akan ka mai girmace."
13) Annabi (SAW) bai nemi karin wata ni'imah ba a duniya sai ILMI.
Yana adduah da cewa: "Rabbi zid niy ILMA."
14) Annabi (SAW) yana cewa: "Malamai magada Annabawa ne.
Kuma Annabawa ba su gadar da zinare ko azurfa ba, sai dai sun
gadar da ILMI…"(Tirmizhiy ya ruwaito).
15) Allah ya nuna darajar shaidar masu ilmi. Allah yana cewa: Allah
yayi shaidar babu abun bautawa da gaskiya sai Shi, haka Malaa'iku
da ma'abota ilmi, cewa Allah yana tsaye da adalci."
16) Allah ya nuna mana cewa Malaman (gaskiya) sune masu
tsoron Allah.
17) Masu daraja idan sun nemi ilmi wannan na kara musu daraja.
Annabi (SAW) yana cewa: "Zababbunku a jahiliya su ne
zababbunku a musulunci idan sun fahimci addini."
18) Ba'a samun ingantacciyar Aqeedah da Ikhlasi dole sai da ilmi.
Allah yana cewa: "Ka sani babu abun bautawa da gaskiya sai
Allah."
19) Darajar mai ilmi bata zama daya da darajar jahili.
20) ILMI HASKE NE. Allah yace: "shi (ilmi) ayoyi ne bayyanan nu a
cikin zukatan wadanda aka bawa ilmi."
21) ILMI SHI YAKE DAIDAITA HANKALI. Allah yace: "Wadancan
misalai ne muke bugawa don mutane, amma babu masu hankalta
sai masu ilmi."
22) ilmi ya halatta ayi tsere-tsere cikin neman sa.
23) Hanyar ilmi, hanya ce ta Aljannah. Annabi (SAW) yana cewa:
"Duk wanda ya kama hanya don neman ilmi, Allah ya sauwake
masa hanyar zuwa Aljannah." (muslim ya ruwaito)
24) Imam Malik RH yana cew: "ilmi kariya ne daga FITINTINU."
25) Annabi (SAW) yana cewa: "Ku isar da ga gare ni, ko aya daya."
26) Allah ya umurce mu, mu rika tambayar masu ilmi kan kowace
matsala.
27) Annabi ya kan yi adduah ga duk wanda yake so, da Allah ya
kara masa ilmi. Kamar yadda yayi wa Abdullahi bn Abbas (RA)
adduar Allah ya kara ma sa fahimtar addini.
28) Allah yana daukaka masu ilmi da imani.
29) Annabi (SAW) yana cewa idan mutum ya mutu, duk
ayyukansa sun yanke amma ban da guda uku, daga cikinsu akwai
ilmi mai amfani.
30) Mafi girman Ilmi shi ne ilmin sanin Allah, da sunayenSa da
SiffofinSa, da kadaituwarSa.
31) Duk lokacin da ilmi ya karu, daraja tana karuwa.
32) Malamai sune kan gaba wajen sanin Allah (SWT).
33) Girmama Malamai (na kwarai) wani bangare ne na addini.
Saboda sune Waliyan Allah kamar yadda Imam Shaafiiy RH yake
fada.
34) Allah yayi umurni da yiwa AnnabinSa salaati. (Allahumma Salli
ala Muhammadin, wa ala..)
35) Ya Allah ka kara yarda da Abubakar, da Umar, da Uthman da
Aliyyu da sauran Sahabbai (Radhiyal Lahu Anhum ajma'in).
36) Allah ka taimaki Musulunci da Musulmai.
37) Allah ka albarkaci garuruwanmu kuma ka kara mana wadata.
38) Allah ka gyara kasashen dake cikin Fitintinu da damuwa.
39) Yaa Allah ka datar da Shugabanmu cikin yin dai dai, Yaa Allah
ka datar da shi cikin aiki da littafinKa da Sunnar AnnabinKa (SAW).
Yaa Allah ka taimaki sojojinmu kuma ka basu ikhlasi.
40) Yaa Allah ka shayar da mu ruwan sama.
41) Yaa Allah lalle mun zalunci kawunanmu, idan ba ka gafarta
mana ba, kuma baka mana rahama ba, zamu kasance cikin masu
asara,
Yaa Allah ka bamu ikon aiki da khudubar, Yaa Allah ka amsa mana
addu'o'inmu,…
Fassarawar Isa Ali Pantami
(Please share it through facebook, WhatsApp, email etc…) — at

KHUDUBAR MU TA JUMU’AH A MASJID QUR’AN!, May 10, 2013

Sheikh Isa Ali
Pantami
KHUDUBAR MU TA
JUMU'AH A MASJID
QUR'AN!
A Yau khudubarmu a
MAJID QURAN' tayi
magana Akan BABBAR
WASIYYAR MANZON
ALLAH (SAW) ga
musulmai. In da Abu
Zarriy (RA) ya shiga gun
Annabi (SAW) yace Yaa
Manzon Allah kamin
wasiyya. Sai Annabi
(SAW) yace: Ina maka
wasiyya da TAQWA
domin shine adon
al'amuranku gaba daya.
Sai Abu Zarriy yace Yaa
Manzon Allah ka k'ara
min wata wasiyyar.
Sai Annabi (SAW) yace:
Ina umurtanka da
karatun Al-Qur'an da
Ambaton Allah domin
shine Ambatonka a
SAMA kuma HASKENKA
a bayan KASA.
Sai yace Yaa Manzon
Allah ka k'ara min wata
wasiyyar.
Sai Annabi (SAW) yace:
Ina hana ka yawan
DARIYA domin yana
kashe ZUCIYA kuma
yana lalata HASKEN
FUSKA.
Sai Abu Zarriy yace Yaa
Manzon Allah ka k'ara
min wata wasiyyar.
Sai Annabi (SAW) yace:
ka fad'i GASKIYA komai
dacinta.
Sai Abu Zarriy yace Yaa
Manzon Allah ka k'ara
min wata wasiyyar.
Sai Annabi (SAW) yace:
Yace kada kaji TSORON
ZARGIN KOWA a cikin
bin Umurnin Allah.
(Ahmad, Dabaraniy, Ibn
Majah da Hakim sun
ruwaito
May 10, 2013 at 1:58pm ·

Gaishe da mara lafiya – sheikh isa ali pantami

Sheikh Isa Ali
Pantami
ZUWA GAISUWAR
MARAR LAFIYA BABBAR
IBADA NE! Allah ya
mana karin LAFIYA da
IMANI,…
Imam Bukhari, Shaykhul
Islam da Ibn
Uthaymeen
(Rahimahumul Laah)
dukkansu sun tabbatar
da cewa zuwa gai da
majinyaci wajibi ne.
Amma Bn Uthaymeen
(RH) yana ganin cewa
yana halatta wani ya
wakilci wani a gaisuwa
ko kuma zuwan wasu
yasa wajibcin ya sauka
kan wasu "Fardhu
Kifaayah."
Annabi (SAW) yana
cewa: ku ciyar da Mai Jin
Yunwa, ku ziyarci
MARAR LAFIYA, sannan
ku yanta Fursunoninku
(Bukhari).
FALALAR ZUWA
GAISUWAN: Annabi
(SAW) yana cewa: Duk
wanda yaje gaisuwa ga
marar lafiya da SAFE,
Mala'iku dubu saba'in
zasu masa Addu'ah har
zuwa yamma. Idan yaje
da Yamma Mala'iku
dubu saba'in zasu masa
Addu'ah har gari ya
Waye. Kuma ana masa
TANADIN LAMBU a
ALJANNAH. (Tirmithiy,
Sahihun ne a cikin Sahih
Tirmithiy).
Annabi (SAW) ya kara
da cewa: Lalle Musulmi
Idan ya ziyarci Marar
Lafiya to yana tafiya ne
a cikin inuwar Aljannah
har sai ya dawo.
(Muslim).
Yaa Allah ka bamu ikon
zuwa gaisuwa ga
marassa lafiya,…
June 2, 2013 at 2:56pm ·

DUK WANDA YA SANYA TUFAFIN ALFAHARI DA BURGEWA A DUNIYA, ZA’A SANYA MASA KAYAN KASKACIN A LAHIRA!

HAUSA & ENGLISH:
DUK WANDA YA SANYA
TUFAFIN ALFAHARI DA
BURGEWA A DUNIYA,
ZA'A SANYA MASA
KAYAN KASKACIN A
LAHIRA! Allah ka kare
mu daga Tufafin
K'ASK'ACI a LAHIRA,…
Manzon Allah (SAW)
yana cewa: Duk wanda
ya sanya TUFAFIN
ALFAHARI a DUNIYA,
za'a sanya masa
TUFAFIN K'ASK'ASHIN a
RANAR LAHIRA (Ahmad
da Abu-Daud sun
riwaito, sannan Shaykh
Albani ya inganta shi a
Sahihul-Jamiy 6526).
Menene Tufafin
Alhafari da burgewa?
Shaykh Ibn Uthaymeen
(RH) yana cewa:
Tufafin Alfahari shine
kayan da aka sanya don
RIYA ko kuma don jan
hankalin mutane a duk
lokacin da Mutum ya
shiga cikin jama'ah.
TUNATARWA: Addinin
Musulunci ya karantar
da mu sanya kaya
masu "MUTUNCI"
amma ya hana mu
tufafin "Alfahari" da
sanya kaya kawai "Don
cinye taro".
Yaa Allah ka kare mu
daga kayan ALFAHARI
da "Kayan CINYE
TARO",…
ENGLISH:
The Prophet
Muhammad (SAW)
says: "He who wears
"libaas ul-shuhra" (i.e
the dress of high
repute,in order to
show-off or as a
status symbol) in this
world will be dressed in
humiliating clothes on
the day of
judgment." (narrated by
Ahmed & Abu Dawood,
confirmed as authentic
by Al Albani in Sahih Al-
Jami' 6526).
" What consists of
libaas ul-shurah?" What
is meant by this
expression is a anything
worn to show-off and
to attract the
attentions of others,
so as to look upwards
unto him/her once he/
she appears wearing it.
May Allah protect us
from the dress of
show-off or status
symbol,…
By
Isa Ali Ibrahim Pantami
June 4, 2013 at 3:39pm ·