DAGA BAKIN FARIN JAKADA [151-170]

DAGA BAKIN FARIN JAKADA
[151-170]
________________________________
______________
.
✺✺✺✺ GARE KU MATA !!!
✺✺✺✺
.
[151] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
Ita mace bata kasancewa
mafi kusanci ga
mahaliccinta (a wani wuri)
fiye da cikin gidanta.”
.
[Silsilatus-sahiha 2688]
.
[152] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
Duk macen da ta shafa
turare, sai ta wuce wasu
mutane don suji qamshin
(jikinta) to ita mazinaciya
ce.”
.
[Sahihu sunanin Nasa’i
5141]
.
[153] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
Duk macen da tasa turare
ta fita zuwa Masallaci,
baza’a amsa mata Sallar
taba har sai tayi wanka.”
.
[Silsilatus sahiha 1031]
.
[154] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
Duk wanda ALLAH ya
azurta shi da mace
tagari,hakika ALLAH ya
taimake sa da rabin
addini, sai ya kiyaye
dokokin ALLAH wajan
samun sauran rabin
addininsa.”
.
[Sahihut Targheeb-1916]
.
[155] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
Duk matar da ta tambayi
mijinta saki ba tare da
wani laifi ba, to haramun
ne ta ji qamshin aljanna.”
.
[Tirmizy 1199, Abu Dawud
2209]
.
[156] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
kada wata mata ta bayar
da izinin (shiga) gidan
mijinta, alhali yana nan,
sai da yardarsa .”
.
[Muslim 1026]
.
[157] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
Mutane biyu sallar su bata
wuce kawunan su:
.
1→ Bawan da ya gujewa
mai gidansa har sai ya
dawo.
.
2→Matar da take sa6awa
mijinta har sai ta dena.”
.
[Sahihut targib 1948]
.
[158] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
Mace baza ta taba sauke
Haqqin ALLAH ba har sai ta
sauqe haqqin mijinta
gabaki daya.”
.
[Sahihut targib 1943]
.
[159] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
Da ace zan umurci wani
yayi ma wani sujada, toh
da na Umurci mace tayi
wa mijinta sujjada.”
.
[Sahihut targib]
.
[160] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
ALLAH baya kallon matar
da bata godewa mijinta,
kuma bata wadatuwa da
shi.”
.
[Sahihut targib 289]
.
[161] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
Ku saurara, Ashe bana
baku labarin matan ku ba
a cikin aljannah ??? (sai
yace): “Itace mai soyayya
kuma mai haihuwa. Idan
tayi fishi ko aka saba
mata, ko kuma mijinta
yayi Fishi sai tace masa:
wannan shine hannu na a
kan hanunka, bazan Qifta
ido ba har sai ka yarda.”
.
[Sahihut targib 1941]
.
[162] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
Matar da take kwaikoyon
maza ALLAH Ya La’ance
ta.”
.
[Ahmad 2/325, Abu dawud
4098-4099]
.
[163] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace:
“Akwai wasu mutane
guda 2 jinsin su na ‘Yan
wuta ne sai dai bai ta6a
ganin su ba ……… Da kuma
mata ga sutura ajikin su
amma dasu da tsiraici
d’aya suke, karkatattu
masu karkatarwa,
kawunan su kamar tozon
raqumi, bazasu shiga
aljannah ba ko qamshin
aljannar bazasu ji ba,
kuma qamshin Aljannah
ana samunta daga wuri
kaza zuwa wuri kaza.”
.
[Muslim 2128]
.
[164] Annabi (Sallallahu
Alaihi wasallam) Yace: ”
Duk matar da ta cire
suturar ta agidan da ba
gidan mijinta ba, ta qeta
hijabin da ke tsakaninta
da ALLAH mabuwayi mai
d’aukaka.”
.
[Imam Ahmad 6/199, 267,
Hakeem cikin Mustadaraka
4/288]
.
[165] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
Kuji tsoron duniya sannan
kuji tsoron mata, domin
farkon fitinar bani isra’ila
ta kasance daga mata ne.”
.
[Muslim 2742]
.
[166] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
Ana auren Mata da
abubuwa guda 4: Don
dukiyarta, don kyawunta,
don nasabarta, don
addininta, na hore Ku da
Ku auri ma’abociya addini
saboda zaku ribantu da
ita.”
.
[Muttafaqun Alaihi]
.
[167] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace:
“Mafi alkhayrin jindad’in
duniya, shine ka samu
Mace Saliha.”
.
[Muslim]
.
[168] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace:
“Idan mace ta sallaci lokaci
biyar, tayi azumin watan
Ramadan, kuma ta kiyaye
farjinta kuma tayi biyayya
ga mijinta, ta shiga
Aljannah.”
.
[Rawahul Bazzar]
.
[169] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace:
“Mace Saliha idan kayi
duba gareta sai ta d’ebe
maka kewa idan ka 6uya
gareta sai ta kiyaye
kanta.”
.
[Alhadith]
.
[170] Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yace: ”
Ya taron Mata Ku yawaita
sadaqa kuma Ku yawaita
neman gafara, domin lallai
naga kunfi yawa acikin
Wuta” sai wata mace daga
cikin su tace: Me muka
aikata Ya Manzon ALLAH
muka zama mafi
yawanmu ma’abota
wuta ? Sai Manzon ALLAH
(Sallallahu Alaihi
Wasallam) Yace: ” kuna
zagi sannan kuma kuna
kafurcewa (butulcewa)
Mazajen Ku.”
.
[Bukhari]
.
RUBUTAWA:
Faridah Bintu Salis
(Bintus~sunnah)
.
Daga: BENEFICIAL FORUM II

Advertisements