HISNUL MUSLIM HAUSA

GARKUWAR MUSULMI TA ADDU’O’I DAGA ALKUR’ANI DA SUNNAH (Hisnul Muslim)
Rubutu Na Farko 0001
TA’ALIFIN
Shaikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Alkandahi
FASSARAR
Dr. Bashir Aliyu Umar Hafizahullah
RUBUTAWA
Abubakar Nuhu Koso
<>
GABATARWAR MAWALLAFI.
Dukkan yabo da godiya ta tabbata ga Allah muna godiya gareShi, mana neman taimakonsa, kuma muna neman gafararsa, kuma muna neman tsarinsa daga sharrance-sharrencen rayukanmu da miyagun aiyukanmu. Wanda Allah Ya shiryeshi babu mai batar dashi, wanda kuma Ya batar babu mai shiryar dashi. Ina mai shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, babu abokin tarayya gare Shi, kuma ina shaidawa cewa Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne, Allah Yayi tsira a gare Shi da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyakkyawan kwaikwayi har zuwa ranar kiyama kuma ya yi musu aminci, aminci mai yawa.
Bayan haka wannan littafi takaitaccen bayani ne daga littafina mai suna <> na takaita akan bangaren da ya shafi zikiri (watau ambaton Allah) don a samu saukin daukansa a halin tafiya.
Na takaita ambaton lafazin zikirin da kuma sunan daya ko biyu daga cikin litatattafan da aka rawaito zikirin a cikinsu wadanda na kawosu acikin littafina na asalin. Wanda yake son sanin sahabin da ya rawaito hadisin , ko karin bayanin litattafan da aka rawaito hadisin a cikinsu, to sai ya koma asalin littafin nawa. Ina rokon Allah, Mabuwayi mai daukaka, saboda albarkar sunayensa kyawawa da kuma siffofinsa masu daukaka, ya sanya shi domin fuskarSa mai daraja, kuma Ya amfane ni da shi a cikin rayuwata da kuma bayan mutuwata, Ya kuma amfani wanda ya karanta shi, ko ya buga, ko ya zama sababi wajen yada shi. Hakika Allah mai tsarki majibinci wannan ne kuma mai iko ne a kansa. Allah ya yi tsira da aminci ga Annabinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyakkyawan kwaikwayo har zuwa ranar hisabi. Ameen
Mawallafi.
an rubuta a watan safar 1409 hijira.
Ranar da na fara rubutawa.
08/01/1438
09/10/2016

Advertisements
%d bloggers like this: