INGANTACCIYAR AKIDA DA KISHIYARTA 001

INGANTACCIYAR AKIDA DA KISHIYARTA
Rubutu Na Farko
.
WALLAFAR
Sheik Abdul’aziz Ibn Abdullah Ibn Bazz Rahimahullah
.
TARJAMAR
Sheik Shu’aib Abubakar Umar
.
MAI RUBUTAWA
Abubakar Nuhu Yahya

.
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Godiya ta Tabbata ga Allah Shi kadai, kuma Tsira da amincin Allah su tabbata ga wanda babu wani annabi bayansa, tare da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka, Yayin da ingantacciyar akida ta kasance itace asalin addinin Musulunci, ta kuma zama itace jigon addini, sai naga cewa abinda yafi, in zabi yin zance a kanta a wannan lakca.
Kuma abune sananne daga dalilan Alkur’ani da Sunnah, cewa duk wasu ayyuka ko zantuka suna ingantuwa ne, kuma su karbu idan sun samo asali daga akida wacce take ingantacciya, idan kuwa akida bata ingantu ba, to duk wasu ayyuka ko zantuka da za’ayi batattune kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce;
[Ma’ida aya ta 5]
Kuma Yace;
[Zumar, aya ta 65]
Ayoyi da suka zo da irin wannan ma’anar sunan da yawa.
Hakika littafin Allah mai bayyanawa da kuma sunnar Manzon Allah Amintacce Tsira da amincin Ubangijinsa su tabbata a gare Shi, sun nuna cewa ita akida ingantacciya ta tattara ne, cikin Imani da Allah, da Mala’ikunsa, da Litattafansa, da ManzanninSa, da ranar lahira, da kuma omani da kaddara Alherinta da sharrinta, Wadannan abubuwa guda shida sune asalin akida ingantacciya, kuma wacce da itace littafin Allah mai girma ya sauka, kuma da itace Allah Ya aiko ManzonSa Muhammad Tsira da amincin Allah Su tabbata a gare shi.
Duk wani abu daya wajaba ayi imani dashi, na al’amuran gaibu, dama duk abubuwan da Allah da Manzonsa Tsira da amincin Allah Su tabbata a gare shi, Suka bada labarinsa, sun samo asaline daga wadannan abubuwa guda shida da aka ambata.

Dalilai da suka zo akan
wadannan ginshikai guda
shida a cikin alkur’an da
sunnah suna da yawa
kwarai da gaske daga
cikin su akwai fadin Allah
tsarkakakke;
ﻟَّﻴْﺲَ ﺍﻟْﺒِﺮَّ ﺃَﻥ ﺗُﻮَﻟُّﻮﺍ ﻭُﺟُﻮﻫَﻜُﻢْ
ﻗِﺒَﻞَ ﺍﻟْﻤَﺸْﺮِﻕِ ﻭَﺍﻟْﻤَﻐْﺮِﺏِ ﻭَﻟَٰﻜِﻦَّ
ﺍﻟْﺒِﺮَّ ﻣَﻦْ ﺁﻣَﻦَ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻟْﺂﺧِﺮِ
ﻭَﺍﻟْﻤَﻠَﺎﺋِﻜَﺔِ ﻭَﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏِ ﻭَﺍﻟﻨَّﺒِﻴِّﻴﻦَ.

[Bakara, aya ta 177]
Da kuma fadinSa Tsarki Ya
Tabbata Gare Shi;
ﺁﻣَﻦَ ﺍﻟﺮَّﺳُﻮﻝُ ﺑِﻤَﺎ ﺃُﻧﺰِﻝَ ﺇِﻟَﻴْﻪِ ﻣِﻦ
ﺭَّﺑِّﻪِ ﻭَﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَ ۚ ﻛُﻞٌّ ﺁﻣَﻦَ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ
ﻭَﻣَﻠَﺎﺋِﻜَﺘِﻪِ ﻭَﻛُﺘُﺒِﻪِ ﻭَﺭُﺳُﻠِﻪِ ﻟَﺎ ﻧُﻔَﺮِّﻕُ
ﺑَﻴْﻦَ ﺃَﺣَﺪٍ ﻣِّﻦ ﺭُّﺳُﻠِﻪِ.
[Bakara,
Aya ta 285]
Da kuma fadinSa Tsarki Ya
Tabbata Gare Shi;
ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺁﻣِﻨُﻮﺍ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ
ﻭَﺭَﺳُﻮﻟِﻪِ ﻭَﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏِ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻧَﺰَّﻝَ ﻋَﻠَﻰٰ
ﺭَﺳُﻮﻟِﻪِ ﻭَﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏِ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺃَﻧﺰَﻝَ ﻣِﻦ
ﻗَﺒْﻞُ ۚ ﻭَﻣَﻦ ﻳَﻜْﻔُﺮْ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻣَﻠَﺎﺋِﻜَﺘِﻪِ
ﻭَﻛُﺘُﺒِﻪِ ﻭَﺭُﺳُﻠِﻪِ ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻟْﺂﺧِﺮِ ﻓَﻘَﺪْ
ﺿَﻞَّ ﺿَﻠَﺎﻟًﺎ ﺑَﻌِﻴﺪًﺍ
[An-Nisa’i,
aya ta 136]
Da kuma fadinSa Tsarki Ya
Tabbata Gare Shi;
ﺃَﻟَﻢْ ﺗَﻌْﻠَﻢْ ﺃَﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻳَﻌْﻠَﻢُ ﻣَﺎ ﻓِﻲ
ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ۗ ﺇِﻥَّ ﺫَٰﻟِﻚَ ﻓِﻲ
ﻛِﺘَﺎﺏٍ ۚ ﺇِﻥَّ ﺫَٰﻟِﻚَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻳَﺴِﻴﺮ
[Al-
Hajj, Aya ta 70]
Dalilai kuma da suka zo a cikin sunnah kan karfafa wadannan ginshikai shida na imani suna da yawa kwarai da gaske, A cikinsu Akwai ingantaccen hadisin nan, kuma mashahuri wanda muslim ya rawaito a cikin sahihinsa, daga hadisin sarkin muminai Umar ibn Khaddab, Allah Ya yarda dashi cewa Jibril, Amincin Allah Ya tabbata a gare Shi, yayi wa Manzon Allah Amincin Allah Ya tabbata a gare Shi Tambaya akan imani sai ya ce;
ﺍﻟْﺈِﻳﻤَﺎﻥِ ﺃَﻥْ ﺗُﺆْﻣِﻦَ ﺑِﺎَﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻣَﻠَﺎﺋِﻜَﺘِﻪِ ﻭَﻛُﺘُﺒِﻪِ ﻭَﺭُﺳُﻠِﻪِ ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻟْﺂﺧِﺮِ، ﻭَﺗُﺆْﻣِﻦَ ﺑِﺎﻟْﻘَﺪَﺭِ ﺧَﻴْﺮِﻩِ ﻭَﺷَﺮِّﻩِ

Wadannan ginshi kai guda Shida daga gare su ne duk wani abu daya zama wajibi musulmi yayi imani da shi ya fito, na gane da hakkin Allah Tsarkakakke, da kuma lamarin da ya shafi lahira da sauran al’amura na gaibi.
*Mu hadu a rubutu na gaba, zamu ji inda malam yayi bayani akan IMANI DA ALLAH TSARKAKAKKE*
.
Abubakar Nuhu Yahya
Tweet@#IbnNuhAssunnee
10-06-1438
09-03-2017

Advertisements

SHAWARA GA YAN BIDI’AH AKAN ABUBUWAN DAKE FARUWA A YAU

SHAWARA GA YAN BIDI’AH AKAN ABUBUWAN DAKE FARUWA A YAU
«»«»«»«»«»«»«»«»«»
«»«»«»«»«»«»«»«»«»
IDAN MALAMANKU SUN KASA FADA MUKU GASKIYA SABODA KARE ZAKIN MIYARSU, KU DAURE KU TAMBAYI DATTAWAN CIKINKU CEWA, DON ALLAH SHEKARU TALATIN 30 DA SUKA WUCE
—«» ANA TARA MUTANE A ZAGAYE GARI DA SUNAN ADDINI?«»
—«» ANA HADUWA AYI RAWA ANA DUKAN KIRJI DA SUNAN ZIKIRI?
—«» ANA HADA YAN MATA DA SAMARI DA SUNAN MAULIDI?
—«» SHIN WAI ANSAN KALMAR SHOKI BALLE RAWAR SHOKI?
—«» ANA RATAYA HOTUNAN WANI SHEHI DA SUNAN KARAMA?
—«» ANA AMMATO SHEHU DA SUNAN YA TSARE MUTUM DAGA FITINA?
—«» WAI A WANCAN LOKACIN AN SAMU A YIWA WANI MALAMI SUJJADA?
——————————————————
DON ALLAH DATTAWA KU FADA MANA GASKIYA SHEKARA TALATIN DA SUKA WUCE
—«» AN TABA DAGA SPEAKER AKA CE AKAN INYASS ZA’A TAKA ANNABI SALLALLAHU ALAYHI WASALLAM?
—«» AN TABA YIN WAKAR BARHAMA YAFI ALLAH SUBHANAHU WA TA’ALA
—«» DON ALLAH KUNJI WAKAR DA AKACE WANI BAI HAIFA BA KUMA BA’A HAIFESHI BA?
—«» SHIN WAI A WACCAN LOKACIN KUNA ZUWA KAULAHA DON TABARRAKI?
••••••••••••••••••••••••••••••••••
IDAN HAR YA TABBATA SHEKARU TALATI DA SUKA WUCE IYAYENMU BASUYI WADANNAN ABUBAUWAN BA
—«» ME YASA ZA’AKE ZARGIN WANDA BAYAYI?
—«» ME YASA ZA’A CEMA WANDA YACE AJI TSORON ALLAH YADAI NA KAFIRTA MUSULMI?
—«» SHIN WAI WANDA YACE BARHAMA YAFI ALLAH SHINE MUSULMI?
—«» KO WANDA YACE AKAN INYASS ZAI TAKA ANNABI SHINE MUSULMI?
—«» KO KUWA WANDA YACE BARHAMA BAI HAIFA BA, BA’A HAIFE SHIBA SHINE MUSULMI?
—«» ME YASA MALAMANKU BASA YAKAR WADANNAN MUNANAN AYYUKAN?
—«» ME YASA SU WADANNAN MALAMAN SUKA MAI DA HANKALI WAJEN AIBATA MALAMAN SUNNAH?
—«» ANYA BA SUNA NUFIN KARE WADANCAN MUSHIRIKAN DA SUKA FAKE A CIKINKU BANE?
«»«»«»«»«»«»«»«»«»«»«»«»«»«»«»«»«»«»
DAGA KARSHE YA KAMATA KUJI TSORON ALLAH DOMIN KUWA WALLAHI BA MANUFAR MALAMANKU BANE KARE MARTABAN MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAYHI WASALLAM, DOMIN KUWA DA ITACE MANUFARSU DA BASU BARI ANA YADA BARNA ANA SHIRKA ANA CIN MUTUNCIN MANZON ALLAH A CIKIN DALIBANSU, YA KAMATA KUYI NAZARI SOSAI A WATAN RABI’UL AUWAL DAYA GABATA ANYI DUK ABINDA AKA GA DAMA DA SUNAN ADDINI AMMA KODA A JIHA DAYA BA’AYI MAULIDIN JIHABA, AMMAFA A HAKA KWANANNAN NIGERIA HARMA DA KASASHE SABODA MAULIDI INYASS, IN HAR ANNABI AKE NUFI ME YASA BA’A HADA TORON DA AKE CE MUTANE MILIYAN UKU SUKA ZOBA, SABODA HAKA WALLAHI KUJI TSORON ALLAH KU TUBA DAGA WADANNNAN MIYAGUN AIYUKAN.
—————————
—————————
ALLAH YA KARE MU DAGA DUKKAN AYYUKAN DA ZASU KAIMU ZUWA GA BATA.

*Muhadarori Guda 30 Da Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah (Hafizahullah) Ya Gabatar*

*Muhadarori Guda 30 Da Sheikh Musa Yusuf
Asadussunnah (Hafizahullah) Ya Gabatar*
1. *Abubuwanda suke sawa mutum ya karkace
ma tafarkin Allah*
http://darulfikr.com/s/12420
2. *Alakar Shia da Qur-ani*
http://darulfikr.com/s/9197
3. *Anyi Walkiya Koya Yaga Kowa 1*
http://darulfikr.com/s/8963
4. *Anyi Walkiya Kowa Yaga Kowa 2*
http://darulfikr.com/s/9009
5. *Hakkin Shugabanni Akan Alumma*
http://darulfikr.com/s/8634
6. *Muhimmancin Hadin Kai ga Musulmai*
http://darulfikr.com/s/8655
7. *Nasiha ga Manoman Nigeria*
http://darulfikr.com/s/8568
8. *Sabubban Da kesa Kyakyawan Cikawa*
http://darulfikr.com/s/11140
9. *Sada Zumunci da Hadarin yanke shi 1*
http://darulfikr.com/s/8131
10. *Sada Zumunci da Hadarin yanke shi 2*
http://darulfikr.com/s/8121
11. *Wacece Nana Aisha 1*
http://darulfikr.com/s/5271
12. *Wacece Nana Aisha 2*
http://darulfikr.com/s/5270
13. *Matsalolin aure 1*
http://darulfikr.com/s/3020
14. *Matsalolin aure 2*
http://darulfikr.com/s/3019
15. *Matsalolin aure 3*
http://darulfikr.com/s/3017
16. *Matsalolin aure 4*
http://darulfikr.com/s/3018
17. *Illar shaye-shaye ga matasa da kuma hanyar
magance su 1*
http://darulfikr.com/s/7225
18. *Illar shaye-shaye ga matasa da kuma hanyar
magance su 2*
http://darulfikr.com/s/7226
19. *Me Ya Faru a Karbala*
http://darulfikr.com/s/2976
20. *Dokar Addini*
http://darulfikr.com/s/5229
21. *Akidun shi’a 1*
http://darulfikr.com/s/4194
22. *Akidun shi’a 2*
http://darulfikr.com/s/4193
22. *Allah ne ya Halicce ka da rauni*
http://darulfikr.com/s/1836
23. *Girma Ya Fadi Rakumi YA Shanye Ruwan
Yan Tsaki 1*
http://darulfikr.com/s/5012.
24. *Girma Ya Fadi Rakumi YA Shanye Ruwan
Yan Tsaki 2*
http://darulfikr.com/s/5014
25. *Menene Salafiyya 1*
http://darulfikr.com/s/7066
26. *Menene Salafiyya 2*
http://darulfikr.com/s/7067
27. *Muhimmancin Hijabi 1*
http://darulfikr.com/s/5009
28. *Muhimmancin Hijabi 2*
http://darulfikr.com/s/5010
29. *Tambayoyi biyar*
http://darulfikr.com/s/1834
30. *Kare Martabar Sahabbai*
http://darulfikr.com/s/3416
Ayi sauraro Lafiya
Kasance da darulfikr.com dan samun karatun
malaman sunnah a saukake.
Darulfikr taku ce domin yada sunnah
© Copyright:-
*Nura Ibrahim Maigoro*
20/02/2017.

WA’AZIN KASA A GARIN KANGIWA NA JIHAR KEBBI

Shugaban kungiyar Izala Ash-Sheikh Abdullahi Bala Lau
Shugaban Majalisar Malamai Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo
Daraktan agaji Injiniya Mustapha Imam Sitti
A madadin kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunna ta tarayyar Najeriya, suna farin cikin gayyatar ‘yan uwa musulmi zuwa wajen wa’azin kasa da zata gabatar a garin kangiwa dake jihar Kebbi a Naijeriya A Ranakun Asabar 25 da Lahadi 26 ga wannan wata na februru a shekata ta 2017 in Allah ya yarda.
-Babban Bako na Musamman : Mai girma gwamnan jihar kebbi, Sanata, Atiku Bagudu Abubakar
-Manyan Baki sun hada da:
– Mataimakin Gwamnan jihar kebbi,
Alhaji kanal, Sama’ila Yombe Dabai (mai ritaya)
-Sanata mai wakiltar kebbi ta tsakiya,
Alhaji Muhammadu Adamu Aliero.
-Sanata mai wakiltar Kebbi ta Arewa, Dr. Yahaya Abdullahi Argungu
-Dan Majalisar tarayya mai wakiltar, Arewa Dandi
Alhaji Dakta Hussaini Sulaiman Kangiwa
-Dan Majalisar tarayya mai wakiltar Suru da Bagudo Abdullahi Hassan Suru.
-Dan Majalisar tarayya mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza Engr. Abdullahi Umar Muslim
-Uban taro: Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Isma’ila Muhammadu Mera .(CON)
Masu masaukin Baki:
Alhaji Yusuf Sulaiman (Mai arewan Kangiwa)
-Hon. Muhammad Hamid
Kantoman karamar hukumar Mulki ta kangiwa
-shugaban Izalar jihar kebbi, Ustaz Aliyu Abubakar Dan’agaji jega.
Malamai masu wa’azi:
-Sheikh Dr. Alhassan Sa’id Adam Jos
-Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina
-Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe
Sheikh Abbas Muhammad Jega
-Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe
-Sheikh Habibu Yahaya Kaura
-Sheikh Abubakar Giro Argungu
-Sheikh Dr. Abdullahi Saleh Pakistan
-Sheikh Barr. Ibrahim Sabi’u Jibia
-Sheikh Sheikh Khalid Usman Khalid
-Sheikh Abdulbasir Isah Unguwar mai kawo
-Sheikh Umar Jega
-Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi rijiyar lemo
-Alaramma Abubakar Adam Katsina
-Alaramma Ahmad Suleiman Kano
-Alaramma Nasiru Salihu Gwandu
-Alaramma Usman Birnin Kebbi
-Alaramma Bashir Gombe
-Alaramma Yusuf Suru
Da sauran malamai da alarammomi na kungiyar
Allah ya bada ikon halarta Amin.
Sanarwa daga Babban Sakataren kungiyar, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe
JIBWIS NIGERIA

AUDIO NA WA’AZIN WALIMA DA AKA GABATAR RANAR LITININ A GARIN KOSO

AUDIO NA WA’AZIN WALIMA DA AKA GABATAR RANAR LITININ A GARIN KOSO
Danna links din dake kasa damin sauraro ka sauke wa’azin da Kungiyar SHABABUS-SUNNAH DOGUWA suka gabatar a garin koso bisa Shiryawar ‘yan uwa Ahlussunnah Na garin koso ranar litinin 08/05/1438 – 06/02/2017; Sannan muna kara godiya ga dukkan ‘yan da suka halarci wa’azin dafatan Allah Ya kara hada kanmu A sunnar Annabi Muhammad Sallallahu Alayhi Wasallam.
.
001 MALAM ABDUSSALAM DOGUWA
http://kiwi6.com/file/1js8e4ij0x
002 MALAM ABBA ADO DOGUWA
http://abbakarkoso.wapka.mobi/music/view/53276688
003 MALAM SURAJO DOGUWA
http://kiwi6.com/folders/m7t5u1oq3v
004 SHEIKH MUHAMMAD AUWAL IBRAHIM DOGUWA
http://kiwi6.com/file/1lf23orgya
005 JAWABIN GODIYA – MALAM MUKHTAR GARBA KOSO
http://kiwi6.com/file/jjuv6n8lzf
.
Ayi sauraro lafiya
Abubakar Nuhu Koso
#IbnNuhAssunnee
13/05/1438
11/02/2017.

***KYAKKYAWAN ZANCE 004***

***KYAKKYAWAN ZANCE 004***
.
Shirka ta kasance mafi girman laifi kuma mai aikatata Aljannah Ta Haramta A gareshi saboda haka yan uwa mu nesanceta, Allah Subhanahu Wata’ala Yace: Lalle wanda ya hada
Allah da wani, hakika
Allah ya haramta
aljannah a gare shi kuma
makomarsa wutane, bai
kasance ga azzalumaiba
mai taimako.
[suratul ma’ida]
ALLAH YA TSARE MU DAGA AIKATA SHIRKA
.
Abubakar Nuhu Yahya
#IbnNuhAssunnee
03/05/1438
31/01/2017

***KYAKKYAWAN ZANCE 003***

***KYAKKYAWAN ZANCE 003***
.
A Koda Yaushe Zuciyar
Dan Adam tana riya
masa wasu abubuwa
na furuci ko aiki harma
yayi yunkurin Aikata
wasu, Saidai ba ko
Yaushe ne Take Hasaso
Alkairiba, Saboda Haka
Dan Uwa Kayi nazari
Sanna Ka auna Koma
me zakayi da Alkur’ani
da Sunnah, kafin ka
Aikata ko furta Abinda
zuciyarka ta bijiro
maka Dashi.
.
Abubakar Nuhu Yahya
#ibnNuhAssunnee
03/05/1438
31/01/2017

***KYAKKYAWAN ZANCE 002***

***KYAKKYAWAN ZANCE 002***
.
Dan uwa ni da kai
duka muji Tsoron Allah
(SWA) a cikin dukkan
al’amuran rayuwa kada
son jin dadin duniya ya
mantar damu
wadannan manyan
kalubalen dake
gabanmu.
*Mutuwa.
*Tambayoyin Kabari,
*kwanciya da azabar
kabari.
*Tashin Alkiyama.
*Tsayuwa a filin
alkiyama
*Tambayoyin ranar
karshe.
*Ketara siradi.
*Amsar takardu a
filn alkiyama.
*Hisabin ayyukan da
mukayi
Aljanna zani ko
wuta. (ALLAH YA
KAREMU).
.
Abubakar Nuhu Yahya
#ibnNuhAssunnee
03/05/1438
31/01/2017

***KYAKKYAWAN ZANCE 001***

***KYAKKYAWAN ZANCE 001***
:
Annabi
Muhammad
Sallallahu Alayhi Wasallam
Yace:
Lallai Gaskiya Tana
shiryarwa Zuwa ga Da’a,
Shi kuma Da’a yana
Shiryarwa Zuwa ga
Aljannah, lallai mutum
baita yin Gaskiya Ba Face
An rubuta shi A wurin
Allah Subhanahu Wa
Ta’ala shi Mai Gaskiyane
”SIDDIQINE” .
Lallai Karya Tana
shiryarwa Zuwa ga Fajirci,
Shi kuma Fajirci yana
Shiryarwa Zuwa ga Wuta,
lallai mutum baita yin
Karya Ba Face An rubuta
shi A wurin Allah
Subhanahu Wa Ta’ala shi
Makaryacine.
{BUKHARI DA MUSLIM}
.
Abubakar Nuhu Yahya
# ibnNuhAssunnee
03/05/1438
31/01/2017

***KYAKKYAWAN ZANCE 001***
:
Annabi
Muhammad
Sallallahu Alayhi Wasallam
Yace:
Lallai Gaskiya Tana
shiryarwa Zuwa ga Da’a,
Shi kuma Da’a yana
Shiryarwa Zuwa ga
Aljannah, lallai mutum
baita yin Gaskiya Ba Face
An rubuta shi A wurin
Allah Subhanahu Wa
Ta’ala shi Mai Gaskiyane
”SIDDIQINE” .
Lallai Karya Tana
shiryarwa Zuwa ga Fajirci,
Shi kuma Fajirci yana
Shiryarwa Zuwa ga Wuta,
lallai mutum baita yin
Karya Ba Face An rubuta
shi A wurin Allah
Subhanahu Wa Ta’ala shi
Makaryacine.
{BUKHARI DA MUSLIM}
.
Abubakar Nuhu Yahya
# ibnNuhAssunnee
03/05/1438
31/01/2017

%d bloggers like this: