Kungiyar Izala reshen Jahar Kaduna ta bada umarnin sake zaben Mallam Nasir Ahmad El-rufai a matsayin gwamna karo na 2. Daga Ibrahim Shehu Giwa A babban taronta daya gudana a wannan Lahadin, kungiyar Jibwis reshen jahar Kaduna ta bada umarni ga mabiyanta da su sake zaben mal Nasir Ahmed El-Rufai a zaben dake tafe ranar Asabar me zuwa. Da take bayani, shugaban kungiyar na jihar Kaduna Sheikh Alh Tukur Isah, ya baiyana cewa wajibi ne alumma su sanya maslahan addini dana alumma sama da maslahar kawunansu. Shima da take jawabi a wajen taron , babban sakataren kungiyar na qasa Sheikh Muhammad Kabiru Gombe ya ce wajibi ne a tashi da fadakarwa a dukkan masallatan salloli 5 ba wai na jumaa ba kawai muhimmancin fitowa a zabe Elrufain, ya qara da cewa a zaben shugaban qasa da aka gudanar mafi yawancin alumma basu fito kada kuria ba daga bangaren da musulmi keda yawa, a don haka wannan zaben yafi na shugaban qasa muhimmanci kuma yakamata kowa yafito musamman mata, inda ya shawarce su da su dinga bi gida gida don wayar da kan mata yan uwansu muhimmancin zaben. A qarshe shugaban mata na qungiyar wato Amira ta Nisa’ussunnah tayi kira ga mata da su dena amsan na goro suna zaben abinda ba shine ba, kuma an jinjina ma jajircewan da sukai wajen zaben da ya gabata na shugaban qasa. Taron dai yasama halartan shugabannin kungiyar na dukkan qananan hukumomin 23 ne da shugbannin yan Agaji da kuma mata reshen nisaussunnah na dukkan qananan hukumomin jahar.