HUKUNCIN HADA SITTU SHAWWAL DA RAMUWAR RAMADAN


HUKUNCIN HADA SITTU SHAWWAL DA RAMUWAR RAMADAN
Tambaya 
Assalamu alaikum Malam  idan ana binka ramuwar azimi za ka iya niyya biyu : wato  da nufin sittu shawwal da ramuwar Ramadhana a guda daya ?  don Allah mlm taimaka min da bayani.
Amsa 
 Wa alaikum assalamu To ‘yar’uwa kowanne daban ake yinsa, saboda manufarsu ta banbanta, don haka ba za’a hada su da niyya daya ba, kamar yadda ake yi a wankan janaba da wankan juma’a, za mu fahimci haka, a cikin fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : “Duk wanda ya azumci Ramadhana sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal, Allah zai ba shi ladan wanda ya yi azumin shekara” Muslim ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 1164, kin ga wannan yana nuna Ramadan daban, sittu-shawwal daban.
Fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : ” Sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal”  ya sa wasu malaman sun tafi akan cewa : bai halatta ayi sittu-shawwal ba, sai bayan an kammala ramuwar Ramadan. Kamar yadda ya zo a : sharhurmumti’i    6\443
Allah ne ma fi sani.
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
18/7/2014

One response to “HUKUNCIN HADA SITTU SHAWWAL DA RAMUWAR RAMADAN”

  1. Badamasi Rabe Avatar
    Badamasi Rabe

    Allah yasaka muku da Alkhairi

    abuu Muhammad

    On Thu, 28 May 2020 19:23 ABBAKARKOSO ISLAMIC SITE, wrote:

    > Abubakar Nuhu Yahya Koso posted: “HUKUNCIN HADA SITTU SHAWWAL DA RAMUWAR > RAMADANTambaya Assalamu alaikum Malam idan ana binka ramuwar azimi za ka > iya niyya biyu : wato da nufin sittu shawwal da ramuwar Ramadhana a guda > daya ? don Allah mlm taimaka min da bayani.Amsa” >

    Like

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Hey!

I’m Bedrock. Discover the ultimate Minetest resource – your go-to guide for expert tutorials, stunning mods, and exclusive stories. Elevate your game with insider knowledge and tips from seasoned Minetest enthusiasts.

Join the club

Stay updated with our latest tips and other news by joining our newsletter.